HAUSA NOVEL

NARJEESAH

1&2

➿➿➿➿➿➿ Tsaye take a kaina sai masifa takeyi bama zata barni da abunda yake damuna ba.

Kawai matar taci gaba da fad’ar, “yo in banda kin rai nani kin mayar dani ba’a bakin komai ba, dan bani ce na haife kiba, aini matar uban ki ce, kuma dolene na saka ki aiki kiyi mani, ko dan kin ga uban naki baya a raye ne iye? “.

 

Masifar tace ta ishe ni nace, “dan Allah Mama kiyi hakuri ki dubi halin da nake ciki ki dubi yanda nayi kumburi bayana ciwo yake yi mani gashi daket nake zama daket nake tashi, kuma fa ɗazun inno ta sakani wankin yara da nata kayan wallahi da zaune na ƙarasa shi ma”.

Mamar tace, “chan gareki wankin ɗan wankin da kika yi masu wanda bai wuce abun a zo a gani ba? Ni ki tashi kiyi mani nawa aikin ki wanke mani zanen gado na guda biyu da labule na duk sunyi datti kuma idan kin ƙarasa ki ɗora mani girki, yau dambu ma zakiyi muna a gidan nan kafin su Halira su dawo makaranta suda suke da tarbiyya “yam mata ne su sai neman ilimi su basu biye wa kwaɗayi ma buɗin wahala ba, wanda ya biye wa kwaɗayi shike zaman gida baya fita dole ayi aikin gidan iyaye, waima mutum dan yasan ya kwaso mugun abu ai dole ne ya zauna gida yayi aiki ko zai samu zunubin sa ya ragu, amman ke kina wasa da ladar da zaki samu har laifin naki ya rage! “.

Cike da jin zafin maganar da take sakar mani mai mugun ƙona mani zuciya jin na keyi da sa’a tace ba matar ubana ba wallahi da duk irin yanda nake jin jiki na sai na mareta, kawai nace da ita, “Ai kuwa wallahi a yanda nake jin nan ba zan iya yi maki wani abun ba, da ƙasan ciki na ma ciwo yakeyi da baya na! “.

Hannu wa Mama ta fara tafawa tare da rafka uban salati ta ce, “ikon Allah wato yan zun dan kin ganki da wannan ƙaton cikin wanda ba’a san uban sa ba shine kike ganin kin girma baki da kunya har kike zagi na, to mutanen gidan nan kuna jin abunda wannan marar kunyar take faɗa mani magana har da zagi, Yaya! Yaya!! Kuzo ku gani kuma kuji da kunnen ku dan malam baya a raye shine zaki zage ni? dan kada ace nayi mata ƙazafi “.

 

Duk kan nin su matan gidan suka haɗu gurin ɗaya harda Umma na, tunda Umma na ta fahimci cewar dani ake wannan dramar sai ta koma gefe bata ce damu komai ba.

 

Mama tace, “wai har nice zan saka Narjeesah aiki taƙi aikatawa, wai bata iya wa? “.

Inno tace, “Narjeesah kwana kin nan na lura dake fitsara kike ji, ke ce zaki ɓata muna zaman lafiyar da Malam ya ɗauki shekaru yana ginawa, to a gaskiya ba zamu ɗauki wannan rashin mutum cin ba taya zaki zagi wadda take matsayin mahaifiyar ki? “.

 

Ni kuwa shiru nayi ina sauraren su, abun da nakeji a jikina shine kawai yafi damuwa ta.

Ki kayi kunnen uwar shegu damu, sai ka ce kin ga abokan wasan ki a gurin, “Mama ce ke wannan maganar cike da annuri a fuskar ta harda murmushi take zaki tunda ta samu magoya bayan ta”

 

Tashi tsaye nayi na raɓasu na wuce da ket na ke ɗaga ƙafata har na ƙarasa ƙofar ɗakin mu na shige nayi kwanciya ta, ina jin haushin kowa a duniyar nan.

 

Yaya ce ta ce, “Wai nikam Umman yara ba zaki riƙa yiwa Narjeesah magana ba akan abun da ta tsira na yiwa Larai rashin kunya? dan tana ɗauke da wannan cikin kuma ya tsufa ai ya kama ta tayi mata biyayya ko? Kuma ai tariƙa yawan motsa jikin ta ba wai ta riƙa biyewa jikin ta ba, saboda gurin haihuwa zata sha baƙar wahala ne”.

Inno ta ce, “haba ai dai kowa yasan halin Umman yara indai akan Narjeesah ne tofa baza kiji, bakin ta ba, saboda ita sam bata ɗaukar Narjeesah a matsayin “yarta ta cikin ta saboda kasan cewar ta ‘yar fari alkunya, ake yi mata inda dai su Mariya da Nusaiba ne tofa da kinji bakin ta har yafi na kowa, kuma amman banda Narjeesah shi yasa Malam ya cire Narjeesah daga cikin ɗakin ta, ya mai da ita cikin ɗakin na, amman kuma yan zun duk ta sauya idon ta ya buɗe dama idon ta a buɗe yake ga shegen rashin kunya da fitsara”.

 

Ita dai shiru Umma tayi tana sauraren su tace, “to ya zanyi da ita ni wallahi nayi tsammanin da wani kuke magana bada ita ba”.

Shiru sukayi kowa ya kama gaban sa, Umma ce ta sameni a cikin ɗakin ta ina kwance ina haki kamar wadda taci gudu, kallo ɗaya tayi mani ta ɗauke kan ta, taje bakin gadon ta, mai rumfa ta zauna tayi shiru zuwa can ta ce, “Ke ki riƙa daurewa kina motsa jikin ki, nifa bana son kina yawan saka ni magana kuma ba cewa zakiyi ba zaki iya aikata mata aikin taba, sai dai kawai kice, tayi maki haƙuri zuwa anjima ba rashin kunya zakiyi ba kwana kin nan ina lura da yan da kike yiwa Larai rashin kunya to bana so kuma kada na sake ji ko na gani”.

 

Sai da Umma tayi shiru zuwa can nace, “shike nan dan kawai ina cikin wani hali sai ace nice zan riƙa aikin komai a gidan nan ita ce fa ke zagi na amman kinji ta lauye abun, to ina su Anty Asma dasu Balkisu kawai sai ace nice zanyi komai, in kuma ance su manya na ne , su Fauziyya fa? “.

Shiru kawai Umma tayi bata sake magana ba, dama nasan ba zata ƙara maganar ba saboda bata magana fiye da biyu dani koda dagani sai ita ne uwa uba muna da yawa matsawar ana labari na saka baki na to ba zatayi magana ba har sai na tashi nabar gurin ko ita tabar gurin ina jin ciwon wannan abun fiye da zato, ace kai da mahaifiyar ka amman babu wata alamar shaƙuwa ko nuna soyayar ɗa da mahaifiyar sa.

Aikin da banyi ba ke nan aikuwa dambun ta dafa na tsakin masara, ta baiwa kowa banda ni, ni kuwa dama koda nake da ciki da jarabar masu ciki ban fiye son abin da zanci a koma gefe ayi mani habaici ba, dan Umma tasan halina kai kowa ma yasan hali na, bana cin duk abunda ya kasan ce na gori ne, Inno da kanta ta aiko kira na, da ket na tashi na fito a tsakiyar gidan suke zaune ta kalleni tace, “jeki ɗakina ki buɗe kular Yayan ku Deeni akwai alale na nan ki zuba wanda zakici, saura kuma ki ragawa Yayan naku saboda nasan yau sai dai ki zauna da yunwar ki, kije ki ɗora wa mutane aiki”.

 

Saboda nasan halin Inno kuma a ɗakin ta na tashi sam ita bata da rowa kuma koda bata shiri da kai sai ta taya maka ko miye a gaban ta, bata da muba, kuma babu ranar da zata goran ta maka, shi yasa na je na zubo alalen, a kusa da Inno na zauna na fara dubawa nayi shiru, Yaya ce ta kawo mani, yaji da mai na ansa na zuba na fara ci, Anty Basira ce ta ce, “A’a kaga su Hajiya Narjees yau fa kinyi mani ƙatuwa da yawa wallahi wai miye sirrin ne? .

 

Kallon ta kawai nayi, ban ce da ita komai ba, sai alokacin ne Yaya tace, “babu ko shakka Narjeesah haihuwa na kusa, kin kusa haihuwa dan wannan kum buri ya nuna cewar cikin yayi nauyin kuma sai ya zun ne na lura da cewar cikin yayi ƙasa sosai “.

 

Mama tace, “to yan zun idan Narjeesah ta haifu a gidan nan ya ya zamuyi da mutane, kuma taya kuke ganin Narjeesah da abunda zata haifa su zauna da kwanciyar hankali kai gaskiya babu su babu kwanciyar hankali a garin nan dan haka gara ma tun yan zun asan abunyi dan ni babu ɗan da ya isa ya jami zagi, abunda yara na basuyi ba ke nan inda gidan mijin ta take ai da munyi firin ciki amman yan zun sai baƙin ciki muke ciki nikam ba zan yarda ba ehe ! “.

 

Duka kallon Mama kowa keyi, wani kuka naji yana shirin zubo mani amman kuma sai na dake, naji ta bakin kowa.

Cikin mamaki Inno ta ce, “wannan wace irin magana ce kikeyi hakan Larai? Da kika cewa yaran ki basu jawo maki zagi ba, ai itama Narjeesah “yar kice Narjeesah indai da gaske ne Malam son gaskiya kike yi masa ai irin son da Malam yake yiwa Narjeesah kema kiso ta”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button