NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 1) 17&18

       *_♦RAINA KAMA……!!♦_*
               _{Kaga gayya}_
         *_Bilyn Abdull ce????????_*
????????1⃣7⃣
     ………Cikeda girmamawa yace, “Ranka ya dad’e barka da dare?”.
        “barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k’asar kenan?”.

         Gabansa yad’an fad’i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k’asarba, dakiyar dole ya aro yace, “wlhy kuwa nashigo d’azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma”.
      “tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben”.
       d’an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, “ranka ya dad’e lafiya dai ko?”.
      “lafiya k’alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine”.
      “to shikenan, zanshigo insha ALLAH ”.
      “to madalla saina ganka”.
         Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d’aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak’uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak’a matane, yad’an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.
★★★★★
     Rashin reply d’in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.
      Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.
    Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d’aga bikinta again.
      “munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu’a yakamata muyima ‘Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu’ar dazamu mata itace tsantsar k’aunarta a garemu”.
          “shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad’ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da ‘Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam”.
       Murmushi innarmu tayi, tace, “addu’a”.
★★★★★
      Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket.
    Cikeda mamaki Harun yace, “yaushe kashigo k’asar Galadima?”.
     K’aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d’in hannun rigar milk d’in shaddarsa yake k’okarin sakawa, cikeda dakiya yace, “jiya nazo da daddare, kuma inagama yau zan koma”.
       “tofa, amma baka cikin masarauta?”.
      “no a hotel Na sauka”.
      “ok barato a nema ticket d’in, sai muzo mu d’aukeka”.
     “karka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad’u dakai kawai a airport ”.
        Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d’aya yakoma mak’aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k’arya) amma sai gashi shi yana zundumata, “Astagafurullh” yashiga maimaitawa a zuciyarsa.
        Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k’aunar milk) d’inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k’yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had’a a waje d’aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d’in.
        Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad’anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa.
    Muftahu yace, “zaka dawo ta nan kenan?”.. 
      Kai Galadima yad’aga alamar a’a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje.
      Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.
        Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima.
      Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai.
       Basu wani dad’e a airport d’inba jirgin su Galadima yatashi.
★★★★
    Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba’anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad’i, amma kunsan maza darashin d’aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba.
      Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k’arfi.
         Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti.
      Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa.
        Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k’arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita.
        Kusan yamma saigasu Safara’u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki.
      Har dare ba’abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai.
      Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d’iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.
★★★
        Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak’o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d’auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d’aya yabud’e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d’in suje.
          Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d’aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d’in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?.
       Driver yace, “oga ina muka nufa?”.
      Bai bud’e idonsaba kuma bai d’agoba, yace “gidan sarki”.
      Ta madubi driver n ya kallesa, “yalla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta?”.
       Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
       Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima.
         Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d’aga musu, fuskarsa ad’an sake take, bai d’aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye.
      Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.
       Cike fadar take da ‘yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.
    Hannu kawai ya d’aga musu ya rissina yana mik’a gaisuwa ga Sarki.
     Sarki da fuskarsa tacika da fara’ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.
    Nan dogarai suka d’au da fad’in “sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.
       Galadima Yakuma rissinawa ya mik’a gaisuwa ga ‘yan majissar sarki, suma cikeda fara’a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k’aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.
       Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.
      Haka kowa yatashi yana musu addu’ar kasancewa cikin aminci.
    Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik’e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.
      Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad’ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d’aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.
      Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.
        Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.
     Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa, “Muhammad Sameer! kana lafiya”.
      “Alhmdllh ranka ya dad’e”.
       “Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da ‘yan uwanka kuma su Haneefa?”.
       “Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka”.
      “to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima”.
       Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.
          Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k’arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k’oshi sukayi hamdala ga ALLAH.
     
     babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.
     tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace “ranka yadad’e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai”.
       Sarki yay murmushinsu Na manyan k’asaitattun masu ji da mulki, “basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d’iyar ‘Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko”.
       Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k’afarsa, cikeda girmamawa yace “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad’e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik’ewa”.
        Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik’o hannun Galadima, “Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji”.
       “amin ranka ya dad’e, ngd sosai ”.
     Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k’aunar juna, kowanne yanajin d’an uwansa sosaih  a ransa.
     Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak’ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.
      Tundaga k’ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k’imtsa da k’yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.
       Fuskarsa d’auke da k’ayataccen murmushi ya k’araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy”.
       Kunnensa tad’anja kad’an, cikeda tsokana tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martaba”.
     Yayi ‘Yar dariya yana fad’in “tuba nake ginbiyar papi”.
       “ja’irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da ‘yan uwanka?”.
      “kowa lafiya lau ranki ya dad’e”.
       “to Alhmdllhi ”.
  Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.
       Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba.
       Sarkin fada yace “yo kunacan kuna shashanci yaza’ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki ”.
      ‘yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.????
       Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k’annenta, dukda dai bako ina yashigaba.
        Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.
    
Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.
********
Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad’an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d’aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma.
      Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k’ok’arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta.
     Wannan furuci ya d’an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d’ore to kana cinna mata ‘yan canji ta k’ark’ashin k’asane????, amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba????. (Ho innaro mu ta mutunci????????‍♀, ina yinki over ginbiyar Malam faruku????????)
⛹????‍♀
       Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d’aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k’aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai.
      A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci.
       Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k’irji suka fara zama abokaina.
     Ranar data kama sati biyu cif saiga bak’i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak’in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud’in aurena yana son abama d’ansa.
     Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa ‘yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan.
     Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza’ayi su d’auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta.
    Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak’i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta.
     Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d’iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad’an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.
      Lamarifa yayi tsamari a d’an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda ‘yan gidanmu sukejin Dad’i kamar su had’a fati.
    Nikuwa uwar gayya ai ba’a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak’i shiga ko sau d’aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, ‘Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar.
      Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d’auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud’in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk’i auruwa tamkar ni.
     Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya.
      An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti…..
    
*********
     A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid’in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll).
     Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul’fatah idris) saikusha mamaki Ku d’auka ba itace mai ji da kanta d’innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo????).
          Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama’ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul’fatah yamusu dai-dai, koba komai an k’ask’antar da Galadima d’in,  Wanda yadace ace an sama masa d’iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak’inin shine yakama ta ya gada.
         Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k’yak’yk’yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d’iyar babban sarki, amma shi yanada yak’inin ko d’iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.
     Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak’inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta.
           A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k’anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k’annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa  jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya.
       Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak’inin sun fisu komai.
     Hakan ya burge sarki Absul’fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad’i. Sun bada kud’in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal.
     Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren ‘yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abba????????).
      Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul’fatah dad’i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad’e yana masa fata da addu’ar samu.
         Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu’a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi).
       Data sanarma Abie saiya fad’ad’a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.
         
    A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul’fatah yayta masa nasihar yawan hak’uri da kar6ar k’addara, ya nuna masa sunada yak’inin zaici ribar can.
      Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k’ara tasirantar da imani a zuciyarsa.
      Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d’ad’ashi da k’asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a.
     Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun.
      Cikin tsokana sauban dake d’ayan gefen Abie shima yace “yaa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad’i k’ofar gidan kowa”.
     Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad’ad’a afuskarsa………….✍????
Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.
Guys kuje zuwa kawai, k’ila zuwa dare kujini da bonus⛹????‍♀⛹????‍♀
   ALLAH yabama munaya lafiya.
Barka da juma’a.????✋????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????
[4/19, 9:44 PM] ‪+234 706 231 6249: *_Typing????_*
  *_HASKE WRITERS ASSO…????_*
       _(Home of expert and perfect writer’s)_
       *_♦RAINA KAMA……!!♦_*
               _{Kaga gayya}_
         *_Bilyn Abdull ce????????_*
????????1⃣8⃣
     ……….A Asibiti gado suka bani, sunata fad’an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi ‘yar k’aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
     Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
     Wannan karonma Mama Rabi’a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga ‘yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
     Duk suncika d’akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi’a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
     Doctor ne yashigo yace sud’an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi’a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
      Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara’u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d’aukar kai, saikace ba ‘yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak’uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba????.
      Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
        Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad’in maganinku ai, baku masu dangiba……….gabana yafad’i, saboda jin tamkar k’amshin turarensa. da sauri Na d’ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
        Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k’ananun kaya wad’anda suka fidda ainahin k’irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
     Mu 4 ne kawai a d’akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
     A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud’ani.
     Sauran ‘yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d’in.
      Annanma yayi kusan mintuna hud’u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k’arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad’a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa……. tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d’aya.
       Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
    Hannu kawai ya d’aga musu yamatso jikin gadon danake.
       Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad’anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara’u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za’a kwashe.
       Munubiya ce cikin k’arfin hali tace “Munaya ki tashi ana miki magana fa”. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
      Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad’o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba’a iya banbancesu.
        Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
    Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, “ya jiki?”. tamkar bayaso haka yayi maganar.
      Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud’e idona nace “Alhmdllh”.
     Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
      Na d’a6e baki sannan nace “masassara”.
      Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
      Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace “tana nufin fever”.
        Caraf fiddausi tace, “ranka yadad’e k’arya take hawan jinine”.
     Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad’anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, “Sister naga drugs d’innan?”. yafad’a kamar anmasa dole.
     Ko kad’an Munubiya bataji maiya fad’aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d’aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
      Nikaina saida Na bud’e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k’asa-k’asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud’e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
      Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik’ama Munubiya magungunan.
     Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad’in “ALLAH yak’ara lafiya”.
     Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had’a idanu.
        Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d’insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
    su Safara’u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
       Ko kallonsu baiyiba ya d’aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.
        Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?.
    Ta Sanar masa.
Addu’a yaymin sannan yabar wajen shima.
      Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan.
        Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k’ok’arin had’iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?….
    Batada mai bata amsa, su safara’u ma magana suketayi k’asa-k’asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo.
       Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?.
     “wlhy shine kuwa mama”. cewar Fiddausi.
      Haleematu ta kar6e da fad’in “mama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsu”.
       Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, “yo ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d’an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad’i gareshi ai dama, kum…….”
    Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d’aya, yace subarni Na huta.
     Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi.
       Daganan gida suka wuce suna ‘yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.
★★★★★
     Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce.
     Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan ‘yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta”. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku).
       Lips d’insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad’ai yasan burin daya d’auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin.
    Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.
★★★★
   Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.
     Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba.
     Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.
    Yanda ‘yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran ‘yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d’auka itama zata aurar da ‘ya’ya har biyu baneba.
      Mama Rabi’a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d’id’d’irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had’ad’d’en sabulun wanka da mai data had’a mana, ga wasu turare masu sirrin k’amshi, takuma gargad’emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik’af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya.
    Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa.
      Abbanmu yakira mama Rabi’a yabata wasu kud’i akan tak’ara amana siyayyar kayan kitchen da ‘yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata.
     Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad’i, harma tamasa godiya itama.
       Tafiya mama Rabi’a tayi da k’ud’in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k’yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k’arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.
*_kwanci tashi_*
       Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k’ok’ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana ‘yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara’u da Fiddausi.
     Suma dai kam saidai mak’iyi, amma jikin maman safara’u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba.
     Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi’a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na ‘Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad’i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k’ok’ari gaskiya.
      Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d’ai-d’ai.
       Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana????????.
      Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu.
     Nifa dariyama tabani wlhy.
      Ganin ni babu lefe yasaka su baba k’arami siyomin kaya masu k’yau na fitar biki har kala 10, aka d’inka min, sai takalma da bags da veils masu k’yau suma.
      Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam.
         A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k’awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k’awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba.
        Abin mamaki ranar kamu sai ganin k’awayenmu mukayi harna secondary.
        munji dad’in hakan sosai kuwa.
     A ranar kamun saiga wasu mata hud’u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi’a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund’e da gulma irinta ‘yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba’a lefene? dabasu kawoma jikartaba?.
       Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.
    Washe gari kuma akayi k’unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d’aya.
      A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba’asan ina za’aje ayiba.
      Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k’ok’arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta.
    Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik’inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk’in jama’a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.
       
   Tunda aunty Salamah tagama yimana k’unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida.
    Gashi Yau zamuyi sister’s and brother’s day, duk da dai saima da yamma.
★★★★★
       Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga ‘yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, “kunga zanma mantafa, my k’ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?”.
          Yatsine fusaka yad’anyi yana gyara zamansa, “nifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d’akkoba ai”.
         Wata uwar harara ta watsa masa tace, “lallai bakada kai yaro, bar ganin matarka za’a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi ehe”
        Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k’asaitarsa yace, “Samha! jeki bedroom d’ina ki duba, maybe suna can“.
      “bama kada tabbas kenan?” cewar mom.
    Bud’e idanunsa yayi yana murmushi, “no mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d’auko su Akash a airport ”.
      Ummu Hasheem tace “kaje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenan”.
       Mik’ewa yayi yana fad’in “thanks you Ummu, nabarku lafiya”.
    Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d’aya bane dabasu dinga wannan rawar k’afarba, sun wani zauna sun had’a uban kayan lefe, yad’an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.
     Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d’aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba).
         An tsara iya wad’anda zasu kai lefenne.
    Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k’yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar.
      Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad’an da zasu kai lefen.
     Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu ‘yan cikin gidansu Galadima ne su hud’u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma ‘yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud’u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam.
        Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi.
     Da kansa yabud’e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa.
        Cikeda d’oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba.
       Kansa yad’an dafe dan yakula Samha na neman k’uresa, shikuma yafad’a mata maganarne domin yanason agaban jama’a yadinga yana tsantsar k’aunar Munaya, a bad’ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud’in saba yabud’e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k’yau, gakuma kud’in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k’annen mahaifinsa.
     Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d’akkota ne zaiba khaleel d’azun yama manta, mik’ama Samha yayi yace “gashi kibata”.
        Da dariya samha ta kar6a tace “Uncle ta gode to”.
       Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen.
      motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.
     
 ★★★★
       Gidanmu ya cakud’e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d’aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.
     A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama’a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k’ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking.
     Babu Wanda yay mamaki a ‘yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad’e masarautar cewar Galadima’yar talakawa zai aura.
       Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud’e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama’ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota.
     Batare da neman isoba Kuyangin  suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu…………..✍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button