BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 1

Page -1⃣

Matashiyar yarinya ce yar shekara goma sha-bakwai dauke da farantin giɗa tana tsaye jikin window makaranta tana leken daliban da ake yi wa darasi.
Yadda ta maida hankali tana sauraren darasin da ake wa dabiban sai ka rantse da Allah har da ita a cikin daliban. Ilmin zamani na daya daga cikin abubuwan da suke matukar burge Aminatu kuma shi ne kadai abun da ta rasa a yanzu, wanda ta riga ta maye gurbinsa da talla a halin yanzu, a izuwa yanzu ta tabbatar bata da muhalli a ilmin zamani, sai dai shi ilmin yana da muhallin a zuciyarta.

“Ba ni gidar goma”

Wata dalibar ta fada da kamar rada gudun kar malamin da yake musu darasin ya ji ta, a munafunci ta jefowa Aminatu wata tsohuwar naira goma, sannan ta maida hankalinta gurin Malamin.
Aminatu ta duka kasa ta sauke farantin dake hannunta sannan ta dauki naira goma din ta daga hijabinta ta saka naira goma din cikin hular dake kanta ta gyara hijabinta sannan ta dauki giɗar ta mika mata, yarinyar ta karba da sauri ta boye.
A lokacin ne malamin ya hango Aminatu tana kallon allon da yake koya musu darasin, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake arba da yara na shigowa makarantar talla, wani lokacin har cikin ajijuwa suke zagayawa idan sun ga babu malamai a ciki.
Sai dai tsayawa a nasu ana daukar darasin karatu babu kamar Aminatu domin ko daliban makaranta basa nuna mata natsuwa da maida hankali sai dai su nuna mata iya rubutu da kuma fahimtar darasin yadda ya kamata domin su a kullum suna aji ne, ita kuma sai idan talla ta biyo da ita.

“Mtcheesss idan ba makarantun kauye ba ina ake wannan abun? Ace makaranta a bude har masu talla suna shigowa, ko wane aji babu ganbu (Kaure) balle har ma ace an zagaye mana makarantar”

Malamin ya fada cike da jin zafin yadda aka wofintar da abun da ya shafi ilmin boko a yanki.
Aminatu na jin haka sai ta duke kasa gabanta na faduwa, daman can yarinya ce mai gujewa fitina da tsoron bacin ran mutane. Dukuduku tai ta fice daga gurin cikin sanda ta koma can bakin kofar makarantar inda suke zama ita da sauran masu talla suna jiran a tashi yan makaranta fito siye siye.
Rayuwar Aminatu rayuwa ce da ta ginu da ilimin addinin da kuma talla, domin bayan noma da mahaifinta yake yi wanda shi ne mafi akasarin mutanen garin galadi suke yi, babu wani abu da aka doraga da shi a gidansu kamar tallar da take, da rana zata kai giɗa makarantar boko, dare kuma ayi mata tuwo, da safe kuma ta fita tallar koko, hakan yasa rabin rayuwarta ta kare a talla. Sai dai ko kadan bata da matsalar rayuwa ta ko’ina domin ita kadai ce mace da mahaifiyarta ta haifa bayan zaratan maza bakwai. Rayuwarta kusan haka rabin rayuwar yan matan garin take ba kowa ya ke damuwa da karatun boko kamar yadda suke damuwa da talla ba, domin talla tana ba su komai cikin har da kayan dakin da ake yi ma yan mata.
Garin Galadi wani yanki ne dake cikin karamar hukumar mulki ta shimkafi, gari ne mai cike da albarka manoma, kusan idan ka ambashi shimkafi kowa ya san gari ne na manoma garin mai cike da albarka da kuma mutanen kwarai. Karamar hukumar Shinkafi tana cikin jihar Zamfara, shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Hedikwatar karamar hukumar tana cikin garin Shinkafi kuma karamar hukumar na da iyaka da karamar hukumar Zurmi Maradun da wasu sassan jihar Sokoto da jamhuriyar Nijar.

Garuruwa da kauyukan da suka kunshi karamar hukumar Shinkafi sun hada da Miyasa, Shinkafi, Bwane, Tunga, Fidani, Tubali, da Faru. An kiyasta yawan al’ummar karamar hukumar Shinkafi ya kai 177,811 mazauna yankin da ‘yan kabilar Hausa da Fulani suka mamaye. Yaren Hausa dai ana magana ne da shi a karamar hukumar, addini Musulunci shi ne addininsu.
Karamar hukumar Shinkafi tana da fadin kasa kilomita murabba’i 674 kuma tana da matsakaicin zafin na digiri 34. Karamar hukumar tana da kogin Tafin Kaiwa da ke ratsa cikin yankinta yayin da matsakaicin saurin iska a yankin ya kai kilomita 11/h. Noma wani babban aiki ne na tattalin arziki da al’ummar karamar hukumar Shinkafi ke aiwatarwa.
Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da al’ummar karamar hukumar Shinkafi suka gudanar sun hada da farauta, kasuwanci, kiwon dabbobi, da ayyukan fata.

                  ***    ***    ***

Tana zaune a gurin har aka tashi yan makarantar masu siyen gid’ar suka siya, wanda tai saura sai ta dauki farantin ta dora akai ta nufi gida tare da kawar tafiyarta Rumaisa, suna tafe tana kirga kudin gidarta har suka kawo mararabar hanya (Hanyar da ta kasu hudu) a nan sukai sallama kowa ce ta nufi gidansu. Da sallama ta shiga gidan kamar yadda ta saba.

“Wa’alaikissalam yar Inna yar Albarka”

Inna ta fada tana juyowa ta kalleta fuskarta dauke da murmushi. Sanusi ya wara ido ya zubar da ruwan daya wanke tufafinsa.

“Mu da ba yan Inna ba a nuna mana bolar mu”

Aminatu ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba, tai saurin aje farantin dake kanta ta mikawa Inna kudin hannunta sannan ta karbi dawon (Fura) da Inna take da inna take kirbi (Daka) ta cigaba da yi tana fada mata ko nawa aka samu yau.

“Aminatu Auta, himma dai yar Audu”

Sanusi ya sake fada da fuskar zolaya, daman can indai yana gida ya fi kowa zolayarta kamar wata abokiyar wasarshi.

“Na ji dai ai ina aiki dai ni ba kamar sauran auta ba ne, kai da baka iya noma fa sai sana’ar tireda”

Ta masa gwalo. Sai Inna ta saka dariya.

“Fada masa dai yar auta gogar aiki, shi baya iya aikin karfi irin na maza sai sana’ar zama”

Aminatu ta wani yi warrr da ido tana jin kirarin da Inna tai mata har cikin ranta, ganin hakan yasa Sanusi sake tsokanarta.

“Eyee su igeee anji dadi, Igengen…”

Take ta turo baki gaba.

“Inna kin ga yana ce min Ige ko?”

“To maza nawa aka haifa kamin a haife ki? Kin zama Ige ai”

Aminatu ta kalli Inna da kwababbiyar fuskarta kamar zata fashe da kuka.

“Inna kina jinsa ko?”

“Dan Allah Sanusi ka gama ka fita ka bar mana gidanmu, ya zaka takurawa Auta”

Inna ta fada. Sai Aminatu ta gyada kai

“Atooo”

Dariya yai ya debi ruwa a babbar buta ya zagaya bandakin da ya kasance na kasa kuma iya tsawon habar mutum, (shoulder) domin idan ka mike tsaye gaba daya, za a iya hangoka.
Kamin ya gama wanka Aminatu ta gama kirba dawon har ta kwashe ta zuba wani, Auta ce amman ba kamar sauran ba, domin bata da ƙwiyar aiki, ita dai bar ta da shagwaba da yawan kuka idan an taba ba.

“Baka ma wanku ba tsami kake yi”

Ta fada tana yatsina fuska kamar gaske. Dariya yai ya shiga karamin dakin dake kusa da na Inna ya shirya cikin wata karamar shadda ta marasa karfi da ta gama shan jiki ya saka hullarsa taɓani ka ji Hadisi, sannan ya fito yana ta kwanbo da talkaminsa na roba.

“Wallahi ba kai kyau ba”

Cewar Aminatu tana dariya, sai Inna ta taya ta.

“Lallai kam kyau ai sai Auta hanci har baka (Baki) sai dai a gwada mata haske shi ma kadan”

“Inna Wallahi ki daina biyewa wannan yarinyar, idan ma ta samu miji irina ta more…”

Har Aminatu ta bude baki tai magana sai kuma tai shiru ta maida dubanta gurin yayanta Amadu, wanda take tsoro kamar mutuwarta domin idan yana a cikin gidan bata da sukuni ko wani motsin kirki bata yi. Na tsantsiyar yarinya ce, sai dai shigowar Amadu ya saka ta kara natsuwa ta yi tsit a gurin kamar babu ita. Amadu irin mazan nan ne da basa wasa da yara balle kuma ita da take kanwarsa ta biyar.
Wani tsohon babur dinsa Honda ya turo ya karaso inda suke, Inna na nashe dawon a tukunya, Aminatu kuma na zaune gaban turmin idonta kasa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button