YANCIN KI Page 21 to 30

Yana jinta sai dai yayi mata banza batare da ya ko kalli inda take ba har sanda ta maida idanunta akan machine din “uhmmmmm Allah sarki machine dinmu kenan “ko tun yaushe kake dawainiya damu? Kana
Ta matso kusa dashi har suna iya shakar numfashin junansu “kana ji ko fu’ad,Kafin yanzu yaci ace ka kalli duniyar wata ,duba yanayin morar machine dinka dakayi, tazarar dake tsakanin duniya da wata Mil dubu biyu ne da talatin da biyu da d’ari takwas da sha uku ,ta sake matso shi sosai tamkr zata shige jikinsa wanda hakan yahaddasawa zuciyarsa bugawa da karfi yaja baya kad’an “meye hk kike kuqarin yi ?
Sharesa tayi kmr bata manufarsa ba tace “bari na tmbyeka wani abu ra’ayinka ne hawa machin ko me ?
“kinsan acikin duniyar rayuwata ba son takura balle shishigi, Dan hk ki kama gabanki kawai ya wuce yasoma tafiya dan yasan machin dinsa ya rigada ya tashi daga aiki ,da sauri ta biyo bayansa “wai abun yayi maka rashin dadi ne ko me daka wuce kabarni tsaye?
Sake banza yayi daita yacigaba da d’aga kafafunsa batare daya kalli inda take ba “kana jina ko zan sai maka lafiyayyiyar mota kiran zamani saboda kafi karfin ka dinga hawar wannan kwarababben machen din , shi km wannan machine sai ka kyautar dashi amman kafin nan zan saka kanikawa suzo su d’auka domin gyara .
yayi saurin juyowa yana fuskantarta har hucin numfashinsa ya bugi hancinta ,tayi saurin lumshe idanunta kirjinta na mahaukacin bugawa kusan minti biyu suna tsaye suna kallon kwayar idanun juna sannan a kasalance muryarsa ta fito “anan garin aka haifeni na tashi na girma, nasan kowani lugu da sako dake nan unguwar, akwai makanikai idan ina bukata zan nemesu da kaina, “batu na mota km kibar abunki saboda fu’ad bai bukata komai daga gareki .
“no karkace hk mana bayan da dukkanin alamun rayuwarka na bukatar ha…..a matukar tsawace ya katseta ta hanyar cewa “Kimin shiru anan kafin na d’aukeki da maruka …
“Mari fa kace?”kina mamakin faruwan hknne ? Yayi mata tmbyr yana tsare gira ,” Tayi saurin girgiza kanta alamun a,a “ok na d’auka kina mamaki ne kiga aiki da cikawa wawiya kawai sannan ya juya yacigaba da tafiya tayi saurin shan gabansa tana sauke naunayen ajiyar zuciya tareda rike kugunta da duka hannuwanta “ok muje na saukeka a gida tunda baka bukatar taimakona “nagode kije abunki kawai….
“Haba fu’ad me yasa kake min hk, Allah fa shi yasan abinda yake nufi daya had’amu ,kayi hakuri kabari na saukeka..a fusace yace “banaso ko dole ne?
Ta. runtse idanunta ahankali tana jin d’aci da rad’ad’in ,wulakanshi gareta, kusan second biyu tana tsaye agurin tana experience din abinda rayuwa kan zowa mutun batare daya shirya ba ,ko a mafarki bata ta’ba expecting zata tsinci kanta cikin soyayya da irinsa ba ,ta d’an Jima tsaye domin ita kad’ai tasan halin tashin hankalin data tsinci kanta sannan tasoma kok’arin bud’e idanunta taga wayam babu shi babu alamunsa agurin ta kara gaba da sauri ta fito titi still bata ganshi ba ,sai ma cin karo datayi da wasu yara kusan su 6 tsaye abakin titi mutun uku makafai yayinda 3 suka kasance masu ido, da alamun titi suke son tsallakawa , tsawon minti uku tana tsaye tana dubansu yayinda mota ko d’aya batayi kok’arin tsayawa domin basu damar tsallakawa ,sbd idan ba lura kayi da kwayar idanunsu da sukayi sama ba, ba bazaka ta’ba cewa marasa idanu bane ,cike da matsanancin tashin hankali ta karasa zuwa inda suke tsaye tare da d’agawa mota ta karshe dake shirin kunno kai hannuta take motar ta tsaya cak, sannan tasoma tsallakar dasu d’aya byn d’aya, wanda hkn ya faru ne a idanun fu’ad ,ahankali shima ya fito daga inda yake zaune yana jiran ta wuce ya kama gabansa, yak’araso inda sauran yaran ke tsaye, sai waigawa tayi tagansa rungume da yaro daya, d’ayan km rike a hannunsa
bayan sun gama tsallakar da yaran, tasoma kok’arin iskeshi inda yaja ya tsaya rungume da hannunwasa duka a kirji yana kallonta tmkr ranar yasoma ganinta ,tana k’arasowa ta tsura masa idanunta tana kallonsa kmr yadda yake kallonta gabadaya kowanensu zuciyarsa cike take taf da shaukin juna “me yasa kake kallona hk ?
“Na canza maka ne ko kuwa har yanzu kana jin haushina aranka ?tayi masa tmbyr ajare tana sake kallon kwayar idanunsa da suka soma canza launi “a halin yanzu bana jin kiyayyarki cikin raina sakamakon kyawawan halaiyenki ki cigaba abu ne mai kyau taimako da kyatatawa kmr hk…..
yana gama fadar hk ya juya zai wuce tayi saurin riko lauluasar tafin hannunsa cikin nata tana murzawa,ahankali”ina zaka fu’ad kabarni ?
“Dan Allah kagaya min kana sona ko akasin hk saboda ina son na karshen komai a tsakaninmu takarasa mgnr tana cigaba da Murza laulausan tafin hannunsa .”a zahirin GSKY bazan sani ba, ko zuciyata na sonki ko akasin hk amman zaki iya tmbyr ita zuciyarta duk amsar databaki zaki iya d’aukarta amatsayin kaddararki.
Ta narke masa fuska tmkr zatayi kuka alamun shagwaba “ni dai kace kana sona plx tafiya zanyi gobe zuwa Abuja takarasa fad’ar hk tana kai hannuta daidai saitin zuciyarsa dake wani irin harbawa “plz now say something to me “kace kana sona Dan Allah.
“Baza’a ce ba , yasanya d’ayan hannunsa ya zare hannunsa dake rike cikin nata, yakara gaba ya barta tsaye agurin , ita km tsurawa bayansa idanunta tana kallonsa har sanda ta daina ganinsa sannan ta juya ahankali zuwa inda tayi parking din motarta.
tana isa tun daga nesa ta hango safwan zaune akan motarta yana dubanta tare da yi mata kallon kasa da sama sannan yace “sweetie daga ina kike haka? Tayi masa banza ta isa jikin kofar tana kok’arin bud’ewa ya duro daga saman motar tare da riko hannunta ,a matukar fusace ta d’ago kyawawan idanunta ta. Zuba masa tana yi masa kallon kaskanci “cool down sweetie abinda nake son sanar dake akwai kuskure acikin abinda kika aikata a mintunonin da suka gabata, barin mota a irin wuraren nan Sam bai kamata akwai hatsari aciki,gashi kin bar motar dake tattare da sirrikan rayuwarki abud’e “saurin me kikeyi da har kika bar kofar motarki a bude?
Tayi kokari fixge hannunta cikin nasa Amman ta kasa saboda irin rikon da yayi mata bazata iya kwatar hannunta ba ,”karki wahalar min da kanki dan bazaki iya ba ,shiga mota kawai muje gida akwai mahiman bayanan, ko nace magana ta karshe dazamuyi dake ..