Labarai

Gurguwar budurwa mai shekaru 70 ta ce saurayi danye shakaf mai shekaru 21 take so ta aura

Wata budurwa yar shekara 70, mai suna Genevieve ta bayyana muradin ta na auren saurayi mai shekaru 21Matar, wacce bata taba barin gidan ta ba, ta bayyana yadda bata taba saurayi ba, kuma batasan dadin soyayya baGenevieve ta dau tsawon shekaru tana rayuwa cikin yanayi mara dadi, saboda matsalar lafiyar kafa da take fama dashi

Wata budurwa ‘yar shekara 70, mai suna Genevieve, wacce bata taba kusantar wani ba, duk ba ita ta zabi hakan ba; sai dai a cewarta haka rayuwa tayi da ita, Legit.ng ta ruwaito.

Genevieve tana fama da matsalar gurgunta, hakan ya tilasta mata rarrafe saboda bazata iya amfani da kafar ta ba; bata taba tafiya ba a rayuwarta.

Kuma bata taba saurayi ba ko samun ilimi ingantacce.

Yayin zantawa da Afrimax, gurguwar budurwa ta ce, an haifeta a shekarar 1952.

Sai dai, a lokacin da iyayen ta suka farga diyar tasu bata iya tafiya, cigaba da rarrafe tayi. Sun yi zaton lamarin zai canza idan ta kara tasawa, amma hakan bai kasance ba.

Budurwar ta bayyana yadda tayi fama da cuta a lokacin da tana yarinya, wanda hakan ne ya shafi kafarta, kuma yasa ta zama lalura ga iyayenta.

Iyayen Genevieve basu tura ta makaranta ba, saboda basu da kudin siya ma ta kujerar guragu, sannan ba za su iya kai ta da dawo da ita kullum ba.

Baya ga rashin samun damar neman ilimi, halin da take ciki ya hana ta samun masoyi.

Daga labarunhausa

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button