BAKAR INUWA 33

Episode 33
……….Yau ta kasance asabar, Ramadhan na gida bai fita ko’ina ba, dan yana buƙatar hutu saboda doctor ɗinsa ya tabbatar masa sugar nashi yayi low, sannan jininsa ya haura sama alamar hayaniya ta fara masa yawa. Shawarar doctor yabi, dan ayanzu yana matukar buƙatar ganin ingancin lafiyarsa fiye da baya, kodan ya samu damar sauke hakkin mutane a kansa. Barcin safe yayi sosai har takai su Raudha basuyi tunanin yana a gidan ba.
Kusan sha biyun rana su Lubnah na baje a bedroom na sama, wanda a tsari shugaban ƙasa da iyalansa ne kawai keda hurumin zaman cikinsu. Zaune suke a baje kowa na sabgar gabansa, ga kayan ciye-ciye da suka saka kuku ya shirya musu, wasuko anyi order nasune a wajaje daban-daban. Su duka ukun babu mai shigar mutunci, daga mai bomshot da best sai mai 3quarter singlet.
A can falon ƙasa, wanda shine na uku a jerin faluka uku da kai tsaye zai kawowa sashen iyalan shugaban kasa Raudha da Basma da Bilkisu ne zaune. Bilkisu na daga gefe tana aikin nata na karatu da bincike-bincike, Basma da Raudha na kallo a lap-top ɗin Basma ɗin cike da shauƙin film ɗin. Sai mama ladi da ke gefensu tana saƙar hannu, wadda alama ya nuna kayan sanyi ne na yara. Sai dai rabin hankalinta nakan television da ake nuna maimaicin labaran daren jiya.
Sanye cikin ƙananun kaya nashan iska ya fito, baƙin trouser dogo mai layin fari guda biyu a gefe da gefe, sai baƙar t-shirt. Kayan sun masa matuƙar kyau kasancewar sa mai hasken fata, sai dai fuskar sam babu ɗigon fara'a alamar barcin da yay bai gama sakinsa ba, duk da dai dama bawai ya cika yin fara'ar bane sai ga wanda ya gadama.
Tsaf falon yake a tsaftace, ga wani ƙamshi na musaman na tashi mai saka nutsuwa da kwanciyar hankali. Da ga can gefe cike tebirin dining yake da kayan breakfast kamar yanda kuku bai gajiya da shiryawa a kullum, duk da bai taɓa ganin alamar wanda akeyi da shi yaci ba sai matar gidan kawai.
Duk da yunwar dake cin cikinsa, maimakon ya nufi dining ɗin kai tsaye sai ya samu ɗaya da ga cikin kujerun falon ya zauna. Yana ƙoƙarin kunna television su Lubnah suka fito daga corridor ɗin bedrooms na Raudha suna kwasar dariya.
Turus sukayi a tsaye suna duban wanda basuyi tunanin gani ba zaune hakimce a falon. Yayin da Ramadhan yay tsam shima domin shigar muryoyin dariyar ƙanen nasa cikin kunnensa da shi sam baima san da zamansu a gidan ba ko yace ya manta da batun zuwansu.. Duk da kuwa Maa ta jima da sanar masa zasu dawo nan da zama kafin ta dawo. Amma jin Bappi da Anne babu wanda ya masa maganar ya sashi ɗaukar mahaifiyar tasa ta janye batun duk da a yanzu haka tana ƙasar England ita da Pa.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zuba musu, tare da watsa musu wani irin gigitaccen kallo daya gama kiɗima su gaba ɗaya har fitsari na neman kufcema wasun su, dan a rayuwarsa yayi matuƙar tsanar shigar banza. Shi ko akan iyalinsa ne bai cika son ganin matarsa da ƙananun kaya ba anyhow.
Sanin dokarsa ya saka Lubnah da Muneera kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito, yayinda Aina ta daburce matuƙa, dan tun randa ya kamata a U.S tana aikata abinda bai dace ba suke wasan ɓuya, ta kuma haramtawa kanta zama duk inda zasu haɗun tunda ya dawo NAYA. Ko maganar haɗata aure da ake da shi, tana matuƙar buƙatar hakan, dan tana mutuwar son Ramadhan tunba yanzu ba, sai dai tana fargaba da sanin mawuyacin haline ya amince da aurenta, shiyyasa tafi yarda da zuga mahaifiyarta (Adda Asmah) akan tarwatsa auren Ramadhan ɗin kawai.
Tun kafin abinda ta hango a cikin idanunsa ya fita a fatar bakinsa ya sake gigitata ta kai durƙushe ƙasa, sai kawai ta tafi da rarrafe dan batasan taya zata miƙe ma tayi gudun ba tsabar rikicewa..
Wani irin numfashi Ramadhan yaja na tsananin ɓacin rai, lip nashi ya tura cikin baki ya cija da ƙarfi, yayinda zuciyarsa ke ambaton sunayen ALLAH domin son yin controling fushinsa. Tsahon mintuna biyu ya buɗe idanunsa, tare da miƙa hannu ya ɗauka telephone ɗin dake bisa copy table na kusa da shi. Sai kuma yay shiru da tunanin wayar ina zai kira?.
Telephone ɗin ɗakin Raudha ya kira. Sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Siririn tsaki yaja, tare da maida akalar kiran zuwa ta falon ƙasa, dan iya nan yasan zata iya zama inhar bata bedroom da nan falon upstairs
Da sauri Mama Ladi data ɗaga kira ta mikoma Raudha da suka maida dukan hankalinsu a kallo ita da Basma kan wayar. Ta ɗago da sauri tana duban mama ladi dake miko mata kan wayar, suma su Bilkisu ita suke kallo. “Ranki ya daɗe inaga daga sama ne kiran nan dan ba'ai magana ba”.
Komai Raudha batace ba ta kai wayar kunnenta da tunanin kosu Lubnah ne.
“Ameenatu! Ki sameni yanzun nan”.
Duk da ba kowa ke kiranta da wannan sunan ba hakan bai hana gabanta faɗuwa ba tai saurin duban Upstairs ɗin a ɗan firgice. Jin ƙarar ajiye wayar da yay ya saka Raudha mikewa har tana cin tuntuɓe da ƙafar Basma ALLAH dai ya hanata kifawa Bilkisu ta tareta.
“Yi a hankali aunty Raudha karki ji ciwo”.
Kai kawai ta iya jinjinama Bilkisun tai ƙoƙarin fara haura steps ɗin da ɗan gudu-gudu, duk da hakan bai hana bayyana nutsuwarta a tafiya ba, wadda ta zame mata halitta tun bayan da sayyadi Abubakar ya saita mata rayuwa.
Ramadhan dake zaton ganin bullowarta dama daga downstairs ɗin ya shiga watsa mata kallon da tunkan ta karaso hanjin cikinta suka fara barin jikin sauran kayan ciki suna kaɗawa. Tana masa kallon mutum mai ƙarancin kirki amma kallon da yake jifanta da shi a yau yayi tsanani da yawa, gashi batasan akan mi yake yi ɗinba kuma. Dan koda wasa bata taɓa kawoma ranta tunanin zaman su Lubnah a saman zai iya fusatashi ba tunda taga dai ƴan uwansa ne ai.
Bilkisu ta ture books ɗin gabanta ta miƙe da sauri tana gyara gyalen jallabiyar jikinta. Dan bata raba ɗayan biyu su Aina'u ne. Upstairs ɗin ta fara haurawa da sauri-sauri itama. Dan haka Basma ta miƙe tabi bayanta.
Hawowar su Bilkisu saman yayi dai-dai da ƙarasawar Raudha daketa ambaton sunan ALLAH gabansa, dan bata taɓa cin karo da irin kallon muzanci da yake mata ba a wajen wani mahaluki......
Turus Basma da Bilkisu sukai ganin wanda basuyi zaton gani ba suma. Dan duk zatonsu su Aina ne ai sukai kiran Raudhan ta landline. Ganin fuskar yayan nasu ya tada hankalin su Bilkisu dan kowa yasan idan yay fushi fita hayyacinsa yakeyi. Duk da dai basu san dalilin kiran Raudhan ba, amma tsoron da suka gani akan fuskarta ya sakasu shan jinin jikinsu suma. Cikin ƙarfin hali Bilkisu ta ambaci sunansa cike da ladabi da shakka.
“Yaya!”.
Wani shegen kallo ya watsamata itama, sai dai kafin yace komai wayar jikinsa ta hau ring. Yasan Maa ce, dan haka ya ɗaga yana jan numfashi da ƙyar tsabar ɓacin rai, baya raba dayan biyu su Muneera ne sukai kiranta. Ba wata magana ta bari sukai mai tsayi ba, dan bata bashi damar cewa komai ba ta yanke wayar.
Ransa ne ya ƙara ɓaci, Yana ajiye wayar Bilkisu data fahimci wadda ta kirasa saboda sunanta daya ambata a farkon wayar takai zaune gabansa a ƙasa. Cikin tausasa harshe ta ce, “Am so sorry Yayanmu. Wlhy ba laifin Aunty Raudha bane ba…..” tsaf ta zayyane masa komai a randa sukazo. Komai baice ba, sai dai ya tura hanunsa cikin gashinsa, tare da jingina bayansa da kujerar ya wani lumshe ido. Tsahon minti ɗaya kafin ya buɗesu a hankali suka sauka akan Raudha da Basma ta riƙema hannu gam-gam saboda lura da yanda jikinta ke rawa ɗazun. Tasan dolene taji tsoron yayansu a irin yanayin nan tunda ba taɓa gani taiba maybe, kosu da suka saba gani a duk sanda ya birkice irin haka tsananin tsoronsa suke.
Janyewa yay ya maida ga Basma. “Kiramin su”.
Kanta ta jinjina masa, kafin ta zare hanunta da cewa “To”.
Da hannu ya nunama Raudha kujerar gefensa. Zama tai a ɗarare tana cigaba da ambaton sunayen ALLAH.
Babu wani jimawa suka fito su duka kowacce da zabgegen hijjab kamar matan liman. Gabansa duk suka ƙarasa suka zube kowacce kai a ƙasa. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Raudha ba. Duk da halin da take ciki itama a ranta al'ajabin yanda suke tsoronsa takeyi, gasu dai manya da su suma. Ita dai tana zaune a inda take, yayinda har Basma a yanzu take a gabansa duƙe.
Bai wani tsaya tambayarsu kojin ta bakinsu ba ya fara magana a nutse amma muryansa a kausashe. “Na baku mintuna goma kacal ku tattara komatsanku ku koma sashen baƙi. Idan kuma har na kuma ganin wata da ƴan iskan kaya a jikinta wlhy-wlhy bazata sake taka ƙafarta gidan nan ba harna barsa ƴan iska kawai. Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya tare da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”.
Daga haka yay musu nuni da su miƙe su bar wajen. Sosai Raudha tai mutuwar tsaye akan furucinsa na ƙarshe. *_“Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”_*. (Minene dalilinsa?). Bata da mai bata amsar nan, dan haka taɗan saci kallonsa ta gefen ido. Ta janye a hankali saboda wani shegen nishin takaici da taji an saki a kusa da ita. Muneera ce, ta watsa mata wani irin kallo na zaki san komu su waye tabi bayan su Lubnah da tuni sun nufi ɗakunan nasu tattare kayansu.
Dafata Basma tayi ganin kamar ta tsorata da abinda Muneera tayi, cikin raɗa yanda Yayansu bazai ji ba tace, “Karki wani damu kanki babu abinda suka isa miki, dan wlhy duk tsoron Yaya suke kamar mutuwarsu. Iyakar iskancinsu na bayan idonsa ne. Kuma tunda muma muna gidan ko kallon banza suka miki sai yaji”.
Kanta ta girgizama Basmam a hankali itama tace, “A'a dan ALLAH karku ƙara faɗa masa Basma. Wannan ma da kun bari na masa bayani yanda bazai zargesu ba”.
“Tab wai tsoronsu kike ji? To wlhy kima cire, dan su aunty Lubnah wutar karane sai da izo. karki yarda suga rauninki zakisha wahala. Gara ki fito musu a mara kunya kema dan nan gidankine kowa yazo zai zaunane karƙashin ikonki. Yanzu dai ki samu Yayan ki bashi haƙuri, dan yana son idan yay fushi koda baka da laifi ka bashi haƙuri”.
Duk da maganganun Basma sunyi tasiri a ranta sai bata nuna ba. Harga ALLAH kuma tanajin daɗin zama da Basma da Bilkisu a gidan
Ganin kowa ya fice a falon harsu Aina riki-riki da akwatina yasa Raudha yanke bin shawarar Basma. Sai da ta ɗan ƙara jan sakanni da fitarsu kafin ta dubi inda yake kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki. Duk da yaji alamar idonta a kansa bai motsa ba, Raudha dake a zaune kanta a ƙasa ta ƙara damke bakin ɗankwalin atamfar jikinta data yafo a kanta sannan ta ɗan zamo jikinta a kujerar kaɗa. Zani da rigane sun mata matuƙar ƙyau dan anyi ɗinkin dai-dai jikinta.
“Dan ALLAH kayi haƙuri baza'a sake ba”. Tai maganar a hankali kamar kuma zata fashe da kuka.
Anan ɗin ma baiko motsaba. Sai dai yajita sarai dan shi mutum ne mai ƙarfin ji shiyyasa Anne ko gulmarsa batayi indai yana gidan. Tsawon mintuna biyu, har Raudha ta sake buɗe baki zata sake bashi haƙurin sai tai shiru saboda ɗagowar da yay daga ɗan jingina jikinsa da yayi da kujera yana sauke mayatattun idanunsa a kanta. Zata iya jure zama wajen da yake, amma bazata iya jure kallon da birkitattun idanunsa suke mata ba. Saboda sunada wani irin kaifi da kwarjini a gareta na musamman.
Kallonta yake sosai kuma kai tsaye wanda ta rasa mi yake kallone a jikin nata. Dan ta kasa dubansa ita. Tsabar kunya ji take kamar ta nutse a wajen ta huta. Sai da yay mai isarsa ya janye idonsa ya maida ga agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Batare da amsa ban haƙurinta ba ya ce, “Ina bukatar abinci”. Daga haka ya sake ɗauke kansa ya maida ga television ɗin dake ɓaɓatu a katafaren falon da yafi kowanne falo haɗuwa da tsaruwa a gidan.
Numfashin daya toshe mata maƙoshi taja da karfi ya wuce cikin ciki ta fesosa a hankali tan mikewa. Sai kuma wani irin fargaba ya ɗarsu mata a zuciya dan tasan dai akwai breakfast ɗinsa a dining, tana shakkar nuna cewar zata haɗo wani bata san amsa mizai biyo baya ba. Rashin mafita ya sakata nufar dining ɗin ta shiga buɗe abincin wajen kusan kala uku. Sam hankalinta bai kwanta da su ba, dan haka ta sake dawowa inda yake zaunen tana kai durƙushe gabansa yay mata nuni da kujera.
Babu fuskar yin musu, sai kawai takai zaune a ɗofane kamar ɗazun. “Dama zance ko a duba lunch dan wancan sun huce”.
Shiru bai amsa ba, hakan ya sata ɗan ɗago ido ta saci kallonsa, sai taga ita yake kallo, sai dai tana ɗago ido ya janye nasa cike da basarwa.
“Duk yanda kikai yayi”.
Ya bata amsa tunkan tace wani abu. Tsam ta miƙe a wajen ta nufi downstairs. Shi kuma ya cigaba da kallonsa zuciyarsa na kissima masa wani abu daban akan Raudhan. Baya buƙatar ɓuɗewar idanunta da yawa, sai dai a matsayinsa na shugaban ƙasa yana bukatar matarsa ta zama mai buɗaɗɗen brain kodan mu’amula da mutanen dake a cikin gidan dama masu shigowa. Bai cika son macen aurensa mai ƙarancin shekaru ba, amma shawarar Bappi tasa hakan baya damunsa yanzu kuma.
Cikin sa'a Raudha ta iske kukus ɗin gidan na shirin tsara abincin lunch ogansu tsaye akan mai shirya abincinsu duk da dama wannan kitchen ne da iyakar su da wanda ya shafi sashen kawai akema girki, dan haka ta dakatar da shi akan a tattaro breakfast dake sama, zataima shugaban ƙasa lunch da kanta. Kuku yaso yin magana sai dai babu fuskar hakan, sai ya miƙa mata book ɗin dake ɗauke da tsare-tsaren abincin da Ramadhan ke ci saboda yanayin lafiyarsa.
Tana tsaka da dubawa Bilkisu data wuto a falo ta shigo, dan iya su Lubnah kawai aka maida sashen baƙi da ke a falo na biyu. Cikin ƴar tsokana Bilyn dake hawa saman cabinet na kitchen ke faɗin, “Uhm yau da alama amaryarmu da kanta zataima babban yaya ango girki kenan?”.
Murmushi da kunya ne suka lulluɓe Raudha lokaci guda. Tasa book ɗin ta ɗan kare fuskarta. Littafin Bilkisu ta amsa tana dariya itama da sake faɗin, “That's good my sweet aunty. Dama naso na baki shawarar nan tun randa mukai na dare ɗin nan. Inaga yana da ƙyau ragamar girkin mijinki ya dawo hanunki bawai ki barma kuku ba tunda ke special first lady ce data banbanta dana baya, tunda naga Yaya yafi bukatar ganinki a gida kawai ko muryanki baison fita.”
Murmushi nan ma Raudha tayi kawai. Bilkisu taci gaba da faɗin, “Yaya mutum ne mai tsantsami, shiyyasa baya cin abincin kowa sai na Anne. Dan na sashenmu ma yasan ƴan aiki keyi.”
Cikin jin daɗin shawarar Bilkisu da ganin mafitace ma ga fargabar shirin su aunty Hannah data rasa yanda zata ɓullo masa yasa Raudha faɗin, “Insha ALLAHU zanyi ƙoƙarin hakan Aunty Bily. Nagode sosai”.
“A'a mune ai da godiya tunda za'a kula mana da yayanmu”.
Nanma Murmushin kawai Raudha tayi. Daga ƙarshe Bilkisun ce ta taimaka mata sukai komai yanda ya kamata. Sai kuku ya zama ɗan kallo, dan bilkisu gwanace wajen sarrafa girki. sai kuma tambayoyi da sukan masa akan na'urar da basu gane ba ko idan suna buƙatar wani abu da basu san inda yake ba.
Basu wani ɓata dogon lokaci ba komai ya kammala. Suka bama kukus daketa aikin haɗa sauran abincin waje....
…………Kasancewar an kwashe abincin breakfast dake a dining ɗin ɗazu ya bama Raudha damar shirya wanda suka shigo da shi ita da Bilkisu da Basma. Har yanzu yana a inda suka barsa. Sai dai saɓanin ɗazun da yake kallo yanzu yan aiki a system ne. Har sukai suka gama bai ɗago ya kallesu ba. Sai da su Basma suka sauka Raudha ta ƙaraso inda yake.
Bata mance abinda yay mata ɗazun ba, dan haka takai zaune akan kukerar dake facing nashi a ɗofane. “Ga abincin an shirya”. Ta faɗa cikin sanyin muryarta dake da matuƙar tasiri ga Ramadhan batare da ita ta san hakan ba.
Kansa kawai ya ɗan jinjina mata batare da ya ɗago ba. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya miƙe ya nufi dining ɗin. Itama Raudha baya ta dafa masa tana mai satar kallon yanda yake taku cike da ƙuruciya da mazantaka irin ta masu shekarun da basu gaza nashi ba, alamar akwai lafiya da ƙarfin jini a tattare da su.
Duk yanda Bilkisu ta bata shawara haka tayi, duk da ya ɗanyi mamakin yanda tayi komai kai tsaye bakamar waccan ranar ba da dare sai ya danne, cikin nutsuwarsa ya fara cin abincin bayan ya kalli agogon dake ɗaure a hanunsa. Raudha tai ƙoƙarin barin wajen dan a matuƙar takure take dama.
“Ji mana”.
Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi, dan a tunaninta ko abincin ne bai masa ba. Ta dawo da baya tana ƙoƙarin haɗiye fargabarta. Abincinsa ya cigaba da ci tamkar bashine yay kiranta ba. Sai da yaja kusan mintuna biyu a hakan.
“Ba’a ajiyemin abinci a wuce a barni a wajen sai kace mara gata har sai na kammala”.
Idan ta fahimci zancensa yana nufin dai dole ta zauna a wajen har sai ya kammala. Kai mutumin nan zai illatata, shi bai san a takure take da hakan ba? Nasihar Bilkisu data Anne ta sata komawa ta zauna, a ƙasan ranta tana ƙara ganin laifin su hajiyar birni da ko nasihar yanda zata rayu da miji basu mata ba. Sudai kawai farin cikinsu zata auri shugaban ƙasa ɗan babban gida.
Ita dai tunda ta koma ta zauna kanta a ƙasa, shiko laokaci-lokaci yakan ɗago ya kalleta, sai dai komai baice mata ba harya kammala. Shiru wajen ya sake ɗauka, shi bai tashi ba shi bai mata magana ba har kusan mintuna uku da wasu sakanni. Sai dai kaifin idanunsa dake kanta ba karamin kassara duk wani ƙwarin gwiwa na Raudha yake ba. Ji take tamkar ta fasa ihu ta huta.
“Na fahimci komai sai na koya miki shi a gidan nan?”. Ya faɗa a hankali tamkar bada ita yake ba.
Da sauri ta ɗago ta kallesa dan furicinsa yazo mata a bazata. Ya kaɗa bata ƙwayoyin idanunsa masu rikita mata lissafi. “Miye burinki a rayuwa?”.
Babu shiri ta maida kanta ƙasa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ganin baida alamar sake maimaita tambayar balle ta tabbatar da abinda tajin a farko ya sata ƙarfin halin faɗin,
“Karatu. Na addini dana boko”.
Karan farko a duk yinin yau ya saki murmushi, sai kuma ya ɗan kauda kansa a kanta ya maida ga ƙaton hotonsa dake manne a falon, irin wanda a duk wani office dake ƙasar NAYA shi zaka gani manne.
“Wane mataki gareki duka a yanzun?”. Ya faɗa batare daya ɗauke idonsa ga hoton ba.
Sai da ta juya maganarsa sau uku kafin ta fahimci inda ta dosa. “Nayi saukar Al-qur’ani watanni bakwai da suka wuce. na haddace littafin arba’una hadith tun shekaru uku da suka wuce, a yanzu haka akwai hadithai sama da talatin da bakwai a kaina bayan arba’una hadith, sai sauran littatafai suma wani na ƙarisa wasu ina gab. A fanin boko secondary na kammala, sai dai ko result ban amsa ba”.
A hankali ya janye idanunsa daga kan bakinta dake motsin masa lissafin cike da nutsuwa. Ya ɗan haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi tare da kai hannunsa ya shafi gashin dake kwance a fuskarsa. Jin baice komai ba itama sai bata sake cewa komai ba.
Miƙewa yay kamar zaibar wajen sai kuma ya ranƙwafo kanta. A ɗan rikice taja kanta baya jin saukar numfashinsa kusa da ita.
Cikin magana irin ta masu raɗa yake magana saitin kunenta. “Shiyyasa kike zubamin ustazanci a gida ashe”. Yana gama faɗa ya janye jikinsa baya yabar wajen, dariyar yanda ta diririce na cinsa.
Da ƙyar Raudha ta iya sauke numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya da kai hannu ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta ta dafe.
Shin mike damunsa ne wai? Mike son faruwa da ita ne? Ta taɓa so a baya akan ya sayyadi, sai dai akwai banbanci da abinda takeji a yanzun game da Ramadhan. Mike nan hakan?. (Yana miki kwarjini ne kawai, da abunda bakiyi tunani daga garesa ba) wani sashe na zuciyarta ya faɗa cike da tabbatar wa.