BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Tsofo yama ta murmushi yana dan barin jikin nan na tsofafi ya dungure kanta ya ce” haka ne Agaishat, Mutuwa gaskiya ce, Allah ya sa mu cika da imani

Ta amsa da amin…., ta ci gaba da fadin ” ka ce a birni suna da wata kalar madara banda irin wannan tamu ta rakumi ko shanu? Ina so idan ka je birni ka kawo mini in kaiwa Anna ta sha ta ji itama

 

Kansa ya girgiza kawai, domin ya lura yau du labari ne a kunshe a bakin Agaishat, wai shi zuwa birni, shi da a yanzu salarma baya iya zuwa masalaci kafafuwa sun kiya, ga tsufa me zai je nema birni? Sai dai idan har kadarar makwoncinsa a can wannan kuwa ya san ko ta wani hali Allah zai kai shi…………..

Dago kanta ta yi ta ce ” ka san me?

Ya gorgiza kai alamar aa

Ta ce” wankana sau biyu, su Mariama sun bani kaya suka saka na yi wanka 

Murmushi yake na jin dadi, bai taba yarda a duniya Allah na hada jinnin mutun da mutun haka kawai sai a kan yar yarinyar nan, 

Jinta yake tamkar jinninsa, sonta yake har bargonsa, baya son damuwarta, fatansa Allah ya bata miji na gari komai talaucinsa domin ba zata kasa ratuwa da talaka ba, a hakan rayuwarta ta ginu, gidansu ba laifi su ba talakawanan tukuf bane domin dadaya ne gidajensu ke zagaye a garin aman ita rayuwarta irin ta yayan talakawan nan tukuf ce masu wadatar zuciya,  

Tana ta zubar ta mike ta shiga dan totona dakin kamar yanda ta saba dan dudubawa da kyau ta kashe kunama, domin kunamu na cikin kasa bakaken nan wa.inda idan sukai cizo in ba.a yi gagawar shan magani ba dafin na saurin kashe mutun , sune a cikin kasar garin kamar me, yan garin sun iya rayuwa da su, domin sun san inda zasu same su sun iya kashe su tamkar yanda ake kashe cirnaku, 

Ta samu ta kashe wajen hudu ta cilar waje ta dauku tulu ta ce” sai na dawo

Hannu ya daga mata yana murmushi ya ce” Allah ya tsare ki

Yana kallonta har ta fice , ya samu kansa da zirarar hawaye, ya ce” ya Allah baka barin wani dan wani ya ji dadi, Allah ka sa , ka yarda, ka aminta , ka bani ikon gannin ta shiga hannu mai kyau kafin na koma gareka …….

                     *Niamey*

Kan Anna kasa take tafiya domin bata son gannin irin yanda mutanen ke cuwa cuwa, a can kauye shiru ne, ba hayaniya , ba komai, sannan mutanen basu fi a kirga ba, hakan ya sa du idan ta fito daga dakin da Fatimata take koda dan ta leka ta ga safiya ce rana ne ko dare ne? Sai ta rikice

Ji ta yi ta ci karo da mutun, da sauri ta dago dan bayar da hakuri sai dai me, gani ta yi ya zaro idannuwansa yana kallonta, a hankali ya nunota da yatsarsa sai dai wani abin ya ce masa Haba docter, haba docter, wacen koda jikin manyanta ya kamata ba zata koma haka ba, kuma ita batuba ce ba buzuwa ba, wannan kuwa buzuwa ce ta sha bakaken kayanta, kai bama zai yiwu ace ita bace, 

Da sauri ya ce” yi hakuri baiwar Allah

Bata san ta ina ta iya hausa ba, bata san ya aka yi ta ce” Ba komai yi hakuri kaima

Gaba ya yi yana dan waiwayenta, shi dai rabinsa da wancen dama familynta tunda aka hana masa aurenta, tun suna saurayi da budurwa, muryar wancen da wannan ba daya ba, sannan kai ka daina tunani kan matar nan mai yiwuwa matar aure ce

Da sauri ya kawar da maganar a ransa ya nufi office dinsa yana dafe kansa a fili ya furta” ya dace na ajiye aikin nan, na jima ina fama har jikin tsufa ya zo….

Tunda ta koma dakin ta yi shiru tana tunani, 

Gaishat ce ta salame sallah ta juyo tana kallon maman nata ta ce” Anna me ke damunki ne??

Anna ta dan yi jim ta dago ta ce” wani yare na yi yanzu Gaishat, wanni mutun na kade ya min yare na bashi amsa tartar tamkar na iya yaren

Da mamaki Gaishat ta taso ta zauna kusa da ita ta ce” me kuka ce?????????

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                    1⃣2⃣

Cikin yaren buzanci Anna ta maimaita mata abinda suka ce

Da mamaki take kara kallon Anna ta ce” kuma baki san sunnan yaren ba?

Anna ta girgiza kai, da yannayin damuwa a fuskarta ta ce” ban sani ba, kuma da dukan alama ba yaren faransanci bane domin likita ya yi ta yinsa a gabana ba wani fahimta nake ba, sannan ba yaren nan da muke ji wajen masu siyar da abinci a garinnan bane wato Zabarmanci, wannan yaren shima daban yake 

Gaishat ta mike tana kallon ledar fitsarin fatimata ta ga bata cika ba ta ce” Anna, ko mu koma wajen mutumen ku kara yin yaren? Anna ko haka na da nasaba da asalinki? 

Nan da nan Anna ta ji ranta ya baci, asalinta? Kennan dai yayanta ba zasu daina daga mata hankali da wannan kalmar ba, rai a bace ta ce” ina ruwanki da asalina Gaishat? Ina ruwanki? Tana gama fada ta fice a dakin don ji take zuciyarta sai tukuki take mata na bacin rai

Da kallo Gaishat ta rakata, haka ne, komai irin dadin da kake ciki da Annarsu in dai ka yi gigin neman sannin wacece ita? Zata fatatakeka ne ko waye kai komai kusancinka da ita, 

Ajiyar zuciya ta sauke ta karasa kusa da Fatimata da yanzu masha Allah sosai take samun sauki dinkinta ana kula da ita sosai, likitan karshe ne , du niger ta wannan fannin da shi muke takama!

 A yannayin nishadi ta fito a gidansu, Abanta ya santalo Amarya yar bariki, irin a nuna masa ana son yayansa har Bak’A bata kyamata tana bata abinci bayan ya cashewa maryama kudaden da ta yi rantsuwar ba za.a shiga da matar ba sai ya bada su ……Algabitt dai na rakashewa fa amarya , yayansa na gefe suna rayuwarsu , inda bak’a ta dan samu inci na kwana biyu a gidansu domin bashi da lokacin wulakantata yana malake da amarya yan uwanta kuwa sosai suka dan sasauta mata tsanar da sukai mata

Yar waka take da yaren buzanci tana saka sunnanta a ciki, fadi take” ni bak’a yau wa zai so ni?

Bak’a nake wa zai rabe ni?

Yar bak’a haka ne sunana!

Dala biyar babu mai kaunata, 

Ta yi dariya ta ce” ni ko a baiwa an rasa mai siyana a kauye da birni,

Agaishat kij cika muni….ta fadawa kanta sai kuma ta yi murmushi tana girgiza kai kawai

Algabittt, yar firit din yarinyar da ya auro ta furta kai tsaye 

Shi kuwa da yake saman gadon karagarsa ya yi dadaya ya kallota ya amsata da um?

Tasowa ta yi tana juyi uwa bishiya ta karaso tana nuna masa gidan manta na shafawa ta ce” ka san yanzu muma a kauye mun yi ido, yarinyar nan jikanyar mai siyar da fura nake kawance da ita, ita na baiwa kudina ta siyo min wannan man,

Na ga fatar Agaishat ta dameka, baka son yarinyar dan bakinta, ni kuwa na hango kyakyawar yarinya ce ta karshe kawai bakin ne ya yi mata yawa, dan haka ga shawara wace in dai ka yarda ka takurata ta yi a hankali zata dawo farar mace itama mu siyar mu samu kudinmu mu yi tafiyarmu birni mu je mu rakashe mu hau mota mu saka gilashi mu dangwali kaji

Wata zabura ya yi daga konce yana kallonta, irin maganar ta fara shigarsa, ya fara aminta da shawarar amaryar tasa

Kara jujuya masa ido ta yi ta mika masa ta ce” ka ga bude ka gani, ai dai ka san wannan uban farin da na kara ba nawa bane wanda har kake son samun irina …………. ka yi mini ciki na haifa maka mai kyau ko? To sai fa wannan, ka bada na je na kai mata a siyo mata ta shashafa ka ga yanda bak’arka zata dawo yar dagwasssssss

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button