BAK’A CE Page 1 to 10

Murmushi ya sakar mata ya jawota jikinsa ya ce” na yarda, in dai ta dawo fara sai in baki ki kai a siyo dan ubanta sai ta shafa ko bata so
Dan ture shi ta yi tana jin haushi a ranta, dan jaraba sai ya kama ya jajagulata shi ba wani nisa yake yi da lamarin ba du ya hargitsa mata tunani ya barta, haba ta yi aure ta bar jarumin maza saurayinta, aman yau sai ta gayato sho gidan nan
Dan dukan kirjinsa ta yi ta ce” ina so wani dan uwana ya zo mu wuni tare yau Algabiiiiitttttt
Ta fada tana jan sunnan
Da ido ya tsareta, wai itama nan ta iya bariki, murmushi ya yi, shi dai burinsa ta dauki ciki fa? Ina ruwansa inma 2a zqi dane mata ruwan ciki, shi dai in ta yi cikin ta haifar masa kace komin jaraba ya rike abinsa ko a shekara goma ne ya saida ya kara kama daloli, shi kam haihuwar yaya mata ta yi masa rana ( wani abu zai baku mamaki a lamarin nan, irin yanda Algabitt baya kishin matarsa? To bara ku ji readers , ban ce duka buzaye ba, ba zan ce duka ba domin mahaifina buzu ne dan tsananin kulle da yake yiwa matansa ko gidan mutuwa da ta shafi gidansu zasu je shi ke kai su da kansa ba direba ba kuma ya tsaya su fito rufrufruf uwa matan ninja baka gannin komai na jikinsa ko.ina a rufe ruf ba damar ganninsu komai kusancinka da su, sai dai kuma akoy buzayen da basu san darajar matansu ba, sam basa kishin matansu, sai su ga matarsu kwonce saman bed da kato su fice abinsu ko a kwalar rigarsu, baya hana suma in an jima su taketa abinsu doki ce dan haka suke zaune da ita ba wani abin ba! Gaskiya ce a fadeta????????♀)
Murmushi Algabit ya yi mata ya matsota sosai cikin yannayin rada ya ce” ke , kar ki damu da fada mini fan yan uwanki maza zasu zo, in dai zaki zauna da ni ki haifa mini mata masu kyau? To na baki dama!
Ai kuwa da murna ta rungumeshi ta shiga bashi kulawa daidai daukar hankalin tsufansa ????♀
Wannan kennan
…………………………………………
A hankali ya jona wayar abinda zai dafa masa ruwan zafin dan ya kada madara ya sha
Komawa ya yi jikin bed ya zauna ya shiga karanta messages din Walyn, daya bayan daya,
Na farkon farkon du yannayin ranta a bace ne, harda baya jin kunyar a ce matarsa guda ta kwana a cell? Toh garin niamey ya dauka, ita yanzu kunyar zuwa auren da zata hadu da mata take, a jejefeta da habaici ya nuna ita ba kowa bace a fadin duniya
Sai daga baya kuma ta fara nuna wai ina ya je ne? Ya haka zai yi tafiya bai yi mata salama ba? Ina ya tafi?
Sai daga karshe ta sauko sosai ta yi ta turo masa alamun kuka da nuna ta yi missing dinsa yana ina ne? Tana son ganninsa ta yi missing dinsa
Murmushi ya yi a fili ya ce” Hajia Walyn matar Wardugu, Walyn mai zamani,
Girgiza kai ya yi, kai shi kansa ya sani da ace wani saunan namiji ne da tuni Walyn sai yanda ta yi da shi, kuma ba boka ba malan!
Wayarsa ya kunna wace take kiransa, ya cireta a liste noire (Black list) ya kwonta yana sauraron ruwan zafin na karar ya dafu aman ya yi masa banza, tunani yake, wai shi shugaban revel zai yiwa haka? Ya fada masa gashinnan zuwa aman ya ki zuwa? Har ya je ya yi ta zaman jiransa wai sai daga baya ya yi masa message cewa ba zai samu zuwa ba,? Ya sani sarai waye shi aman ai shima ya san waye shi! In ba dan tsufansa ba da sai ta tafka masa ashar din da zai gigita!
Wayarsa ce ta shiga kara , irin kukan bindiga ratatatttatatatatatattatatatatatatattatatatatatatatatatatatatatat
Muka hannunsa ya yi ya dauko yana karanta sunnan mai kiran
Sai da ta tsinke aka sake kira kafin ya daga bai yi magana ba
Oga, bako ne muka yi, ahi kadai yake tafe cikin duhun nan, ya zo ta hanyar boye , ragar wajen nan ta shaida zuwansa domin ta kama masa hannun shine ya fito yana fada
Kai waye ya zo? Wardugu ya katse shi da kakausar murya
Murya na rawa ya ce” Shugaban Revel!
Wardugu ya lumshe idannuwansa, a nitse ya ce” ku shigo da shi fallon farko, ku juya
Da toh suka amsa suna masu mamakin mai gidansu, yana nufin daga shi sai shi zai ganna da wannan hatsabibin mutumen? Lale Wardugu bashi da tsoro, baya dar, baya tsoron uban kowa!
Kwonciyarsa ya yi bayan ya ji wa ke jiransa,
Can cikin tunaninsa wayar ta kuma daukan kuka,
Da haushi haushi ya mike ya daga da kakausar muryar nasa ya ce” Hello!
Wardu………ta fada cikin sanyin murya
Tsai ya yi bai amsata ba
Kuka ta fashe da shi ta ce” tu me manque (i miss you)
Ajiyar zuciya ya sauke a takaice ya ce” ki bi Nuger airlines gobe ina Agadez hotel din sojoji ki sauka nan ko bana nan ki je dakina
Yana gama fada ya kashe kiran yana shafa gefen fuskarsa da sajensa
DOGON wando ya dora saman gajeran ya saka riga fara kar ta ririke damatsunansa ya fito ya nufi fallon da aka sauke bakon dare (????)
Yana zuwa ya shigo kai tsaye,
Mutumen dake zaune ya sha rawani ya hakimce cikin shiga ta kamala mai daukaka darajar dan adam ya dago ya tsaida kallonsa kan Wardugu, a tarihin rayuwarsa dole ya sako wannan yaro, domin shi ne mutun na uku da ya ajiye shi jira
Murya a kausashe ya ce” Wardugu ba.a tsayar da ni jira
Shima Wardugu kai tsaye ya ce” *Rhissa agbula* ba.a ajiyeni jira!
Murmushi Rhissa ya yi, ya mike tsaye suka gaisa irin gaisuwar musulunci suka baiwa juna hannu suna yiwa juna salama
Wardugu ya ce” ya zaka zo wajena ni daya bayan ka san ya dace a tatauna da kai a bainar nasi kowa na da magana da kai harda mai zuwa da maganar shugaban kasarka
Rhissa ya ce” shugaban kasarka dai, ka san ni ba nawa ba! Sannan ni kaima da na aminta ganninka dan na fafata da kai na yarda tsaurin kanka zai je da nawa, bana musanyar yawu da matsoraci, ba.a daukana a tv haka kyauta sai kace wani sakarai!
Wardugu ya girgiza kai ya ce” ya ake ciki? Wa ke son tayarwa kasata hankali? Ina suke? Menene abubuwan yakinsu? Ana jitajitar kune kuka dawo bayan kun daina aiki a niger kace niger ta yi maka kadan sata yanzu? Me yasa ake samun gawarwakin bayin Allah a gidajensu? Masu aikata min haka baki ne! Da sun san idan na damke su zasuna kururuwar na kashe su da abinda nake masu da basu shiga gonata ba!
Wardugu ya karasa yana dukan table din glass din dake falon ya yi wani jijiga aman bai fashe ba domin irin wannan mai masifar karkon ne, sai bindiga mai tsini ke tarwatsa shi
Rhissa ya mike tsaye ya ce” ba ni bane, kuma ba yarana bane, abinda ya sa na tsayar da hankalina kennan har na baro aikina na garzayo dan ganawa da kai! Kar ka shiga yaki da ni ba ni bane! Na yi bincike tsageru ne, kan harkar siyasa ne, kuma na ga makwoncinsu, suna cancanza waje ne ina son sannin tsarin canza wajen nasu, Wardugu nima sai na yi maka maganninsu
Wardugu ya girgiza kai ya ce…..
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣3⃣
Wardugu ya girgiza kai ya ce” ka taba gannin na nemi agaji? Kokowa ai ya dace mutun yayi abinsa! Ka bani hanya kawai ka barni da sauran ai na san tsarin tsagerancin yan tsagera, idan ka yi yaki a kambacina kana so gobe su afko su aikata abinda ya fi haka? Domin sun san ba zan iya tarbansu ba? Aa ba dai Wardugu ba