BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Haka tataunawar Wardugu da Rhissa ta kare, kowa na ji da kansa da kuma ikirarin kansa,

Rhissa ya san abu guda Wardugu ba wai cika  baki yake ba, yana fadin abinda zai iya aikatawa ne, ya san da in dai suka yarda ya ci masu kamar yanda ya fada ne sai sun gwamace mutuwarsu da rayuwarsu a hannunsa, Wardugu ya ga damar ya fitar da su jeji su fuskanci juna wanda hakan kuwa ba zai gyara su ba!

               Wannan kennan

Bayan kwana biyu …….AMERICA

Docteur Mu.azam ne ke zaune yana dadana computer, 

Can ya dago kansa ya duba time, 

A hankali ya ajiye ya mike ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa 

Yana fitowa ya dauki kayansa ya saka ya saka vest dinsa ya dauki agogonsa ya daura ya fito fallonsa dan madaidaici ba wani tarkace sai kujeru da dan table da tv tankamemiya, sai hoton wasu fararan mutane mata da miji ga dukan alamu suna murmushi a hoto

Kamar yanda ya saba zuwa ya yi ganan hoton ya tsaya ya ce” Abi, amy asalamu alaikum, yauma na tashi lafia, sai dai har yanzu ya kasa hakuri ya daina fushi da ni, gashi aiki ya taso min a kasarsa banda shi da mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka dauke ni tamkar dan cikinsu bani da kowa, 

Zan kuma gwada kiransa ku taya ni da adu.a daga inda kuke, ina mai kara yi maku adu.ar Allah ya sa kuna cikin Aljannah

Shi kadai ya tsaya ya yi zubarsa kafin yake zuwa wajen wayarsa ya zauna yana dan murmushi ya shiga doka kira

Yana kallon wayar na haske ya ki dagawa, Walyn ce ta fito daga wanka ta zo ta mike abinta saman lafiyayan bed din hotel din itama tana duba saman screnn din dan gannin wa ke kiransa yake sharewa haka?

Murmushi ta yi ta juya abinta ta shiga neman baci a kasan zuciyarta tana ayanna toh fa da shima yana gaba bare ni? 

Can dai ya daga ya saka a  handsfree

Soja kake

Ya fada yana danne dariyar farin cikin ya daga kiransa

Murya ciki ciki ya ce” Docter kake, kuma dan rainin hankali kake

Murmushi ya yi ya ce” baka hakuri ne? Baka mantuwa ne???

Wardugu ya kawar da kansa ya ce” haka, ka san ba nine na watsa taron aurena ranar aurena dan wani gudiri nawa na shirme daga shiga ka ga amarya kafin a daura aure zaka fito ka watsa taro? Kai mahaukaci ne! Mu.azam baka da nutsuwa

Mu.azam ya bushe da dariya ya ce” Wardugu, abinda ya sa na tsalako fararan fatar, na yi doguwar tafiya niger ba dan ina son na samu *BAK’A* bane?, ni bak’ar mace nake so, ita ce ra.ayina, ita nake son zaman aure da ita! Kar ka manta ni likitan mata ne, idan ka ga na kuke abu kaima ka gwada abokina

Tsaki wardugu ya ja ya ce” kiran na menene?

Mu.azam ya kuma yin dariya ya ce” kai ka dena jin haushina mana, ai ni ban shaki mahaifin matana ba

Da sauri wardugu ya kai dubansa wajen Walyn wace ke kwonce, ta ji sarai dan haka ta yi saurin mikewa tana kallonsa,

Fuska ya hade idannuwansa cikin nata ya ce” eh haka ne na shake shi, domin a lokacin ban san mahaifinta bane, kuma na tarar da shi ya zabgawa mamanta mari , idona ya rufe ban tsaya wata wata ba na shake shi, kai dan ubanka sai yanzu ka tina?????

Ajiyar zuciya ta sauke, tana tine da ranar …..dalilin wannan action din da yayi na ta haukace kansa, wardugu jarabar duniya….komawa ta yi ta kwonta ta ja bargo tana rufe jikinta 

Wardugu ya fice a dakin , yana fita ya ce” Mu.azam??

Mu.azam ya amsa da na.am?

Wardugu ya ce” kana son kashe min aure ne? Tana jinka fa

Mu.azam bai ji dadi ba aman ya ya iya har ta ji, dan tsam ya yi kafin cikin yannayin mamaki ya ce” Wardugu yamzu tsareka ake idan zaka amsa waya ko me? Lale dole na auri batuba 

Kai banza ka nutsu ka ji!!

Mu.azam ya yi murmushi ya ce” dadina da soja zagi, ni dai ka fadawa Ayyata in sha Allah ina nan ina faman gama abinda nake zan shigo Niger, ka san bani da masauki sai kusa da ita dan ita ta iya kula da cikina, zan zo ba zan dawo ba sai na samu macen aure na kuma gama abindq zai kawo ni

Wardugu ya ji dadin haka dan haka ya amsa shi da murnar hakan

Satin su wardugu hudu a garin Agadez yana faman aikinsa wanda tun Anna na fada har ta kawo ido ta zuba masa, gashi ta yi ta yi aminiyarta ta barta ta koma wani wajen ta kiya ta ki fir sai ma fada da ta dauka cewar masarautar ai girma ne da ita, ba ita ba ko baki ta kawo suna da wajen zama har lokacin da suke so a masarautar Agadez

A yau suke saka ran komawa bayan ya fada masu su kiyaye, ya basu magungunna, ya kafa masu sharuda kan lafiar Fatimata,

Jirgin da ya kawo su an basu takarda dan haka suka kai aka saka su a layin wa.inda zai mayar garin agadez bisa jagorancin docter Fannata

Sun sauka lafia inda Fatimata ke dan takawa a hankali daga nan suka nemi abin hawa dan karasawa Timiya…………

Timiya…..me aka kwaba? Me aka yi me ba.a yi ba? Me ake cikin yi? Timiya gari mai abin mamaki, Timiya garin bak’a,

Duka na kawo wuka a yanka Algabitt ya yi mata bisa taki shafa man da ya fitar da kudi ya saya, 

Rai bace ya ce” sai na tsine maki in dai baki shafa man nan ba

Cikin kuka ta ce” Aba, ka yi hakuri ka ji? Bana son canza kalar fatana ka yi hakuri Abanna

Ni ban haifeki ba, ke ba abin alfaharinki bane yau har na yi hakuri na dube ki na nemi intaki aman ki butulce min? Uban wa ke hure maki kune ne ni?

Aba ba kyau, ba kyau, mu ji tsoron Allah

Hannu ya saka ya dake bakinta ya ce” ki rufe mini bakinkin nan mai bakin jaraba! Ke sai kin shafa

Kokarin shaketa yake dan ya shafa mata Mariama ta fito da gudu tana ihu tana nuna dakinsu

Dakatawa ya yi yana binta da kallon meye ke kuwa

Hankali tashe ta ce” Ashta ce, ashta ce, tun da ta ce maka in dai ka yi mata auren nan sai dai a kai gawarta kai kuwa kace sai me ba dai ka daura mata auren ba? Ita ce gata can sai wani abu take daga baya ta fasa motsi

Fancakalar da Bak’a ya yi, shi da amaryarsa suka nufi dakin da gudu

Daidai wannan lokacin Su Anna da sukai doguwar tafiya suka shigo gidan da salama bayan su Dogarai ne da suka tarbo gimbiyarsu wace sarki yake hakimce yana ji tamkar ya zo ya tarbi abinsa

Jin kururuwa ya saka gaban Anna ya yanke ya yi wani irin faduwa, cak ta tsaya tana sauraron magangannun dake tashi, ihun kuka yayanta biyu suke inda Bak’a ke jingine jikin garu ta daga hannunta ta dora saman kanta ta yi tamkar status tana kallon kofar dqkin nasu , 

Muryar amaryar Algabiitt ce ta tashi ta ce” ta kashe kanta, ta kashe kanta

Wani irin luuuuu Anna ta yi wanda ba wanda ya ganta sai faduwarta da aka ji , nan mutanen gidan suka ankara da dawowarsu wanda nan da nan gidan kai dama anguwar ta cika da dukan jama.a ana ta daga maganar, tabas Ashata ta rasu, ta rasu ne da bakin ciki, tana da ciwon zuciya ne wanda ya yi mata tashin kai tsaye, wanda amaryar Algabitt ta yi kazafin ta kashe kanta, 

         Tashin hankali!

Mota ce katuwa irin ta sojoji, direba mai iya janta kawai ya dauka kai tsaye suka karasa gidan Sarki

Ayya na zaune tana gyara akaifunta labari ya zo mata cewar ta fito su tafi

Mikewa ta yi fa hanzari tana murnar yau kam Allah ya sa , 

Tafia suke cikin mota, Walyn na zaune tunda ta cewa Ayya ina kwana bata kara magana ba sai shanshan kamshi take domin da yar tsamarsu da Ayya, gani take Ayya ke zige mata miji yana wulakantata

Tafia ce suka yi mai tsayi, cikin jeji ne sosai kafin suke shigewa sahara gaba da baya

Wani kara motar take a cikin kasar nan tana cin tafiyar wace kana ganni ka san karfi ne ke aiki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button