BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Duda a cikin mota suke aman sun yi budu budu da su domin kura sosai ke tashi sanadiyar gudun da suke a motar da kuma kasa

A hankali ya ratsa yar gadar da ta kai mutun cikin kauyen, wato *TIMIYA*…………..

        YA RAYUWAR ANNA?

ALGABITTTT FA? 

BAK’A?????

SU WARDUGU DA AYYA DA WALYN ME YA KAWO SU TIMIYA??????? MU JE ZUWA …………………………………………………..na yi imanin da ba dan Allah na sakawa bawa hakuri da dangana a zuciyarsa a lokacin da ya rasa wani mutun mafi kusanci da shi da Anna ta samu tabuwar hankali ga wannan lamari na mijinta, kar ku manta na fada ba labarin mutun na dauko ba aa labarin abinda ke faruwa ne, (YA FARU!)……

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        1⃣4⃣

Bayan sun shiga garin timiya mutane suka ringa gudu suna kururuwa, wasu na fadawa gidajensu wasun kuwa na nufa gidan sarki wasu kuwa na kokarin neman hanyar da zata fitar da su daga garin ta barauniyar hanyoyi domin dai garin ba wani rufe yake ba

Da mamaki suke kallon reaction din mutanen, Warsugu da sojan dake jansu ne kawai basu yi mamaki sosai ba duba da yannayin garin motar lafia dai bata shiga sai ta sojoji ko kuwa motar mugayen mutane masu zuwa su kai hargitsi su kashe mutane

Kallonsa ya maida wajen Ayya wace ta dafe habarta ta wara idannuwanta tana mamakin nan yake mutumen kuwa? Aman gudun me suke?

Labari ya kaiwa sarki a yar fadarsa, 

Tabas gabansa ya fadi da jin wannan lamari, ba a taba ba, mota har nan bata fara shiga ba,

Mikewa ya yi da dukan kokarinsa ya tatara karfinsa inda dogarawa suka shiga kabara sunai masa kallon jarumi mai tausayin talakawansa da kuma kallon marigayi

Du a bayansa suke inda yake daga kafafuwansa da kyar yana kara tunkarar motar, gannin motar ta sojoji ce hankalinda ya kara tashi, domin dai shi ya san motar tunda yana shiga gari kai gaisuwa fada, kai harma ya tafi kasa mai tsarki, me ya kawo motar sojawa Timiya? Shine tambayar da yake yiwa kansa, 

To ko dai sojojin ne a cikin motar ko kuwa mugayen mutane domin idan sun kai hari ai suna karbe motocin sojawan

Wardugu ne ya bude gefen da yake zaune ya karbe hannunsa daga rikon da walyn ta yi masa ya diro daga cikin motar tsaye kan kafafuwansa 

Jibgi, dankari, in ba wardugu ba zaka shiga kauye sai ka je da wando tree Carter?  Sai rigar sojawa irin body din nan damatsunnan hannayensa a fili, yar karamar bindiga marar karan sautin harbi ce a kugunsa inda ya rufeta da wannan rigar ta jikinsa ya saka belt kalar kayan sojojin ya daure tam abinsa

Kansa sanye da hula baka kalar wandon sai takalminsa sandal wanda ya daura abinsa 

Sun karbe shi, sun amshi jikinsa, sun kawata shi

Taku ya shiga yi da karfin jiki ya nufi Sarki da ya ja ya tsaya jikinsa na bari, ta faru ta kare, jita jitar Ashta kanwar matarsa ta kashe kanta wani ya kai birni an zo kama sirikinsa, mutuwar yau har kwana takwassss tabas wani ya kai, shikennan Alghabiitttt ya bani domin a hoto kuma a tv a birni Yana gannin wannan mutumen, an ce shugaban sojoji ne, shi da kansa ya zo kama algabiit? Algabitt ya ji haushin rayuwarsa, tunanin da Sarki ke yi kennan inda ya daskare da tare da bugun zuciyar ko wani taku na Wardugu dan nufo shi (????‍♀ in ba kauyanci irin na sarki ba, a rasa mai zuwa kama Algabiit karamin kwaro sai Wardugu? Za dai ka san waye shugaban sojojin nan hangensa kake!)

Yannayin shigarsa ta tabatarwa da Wardugu shi ne magabacin garin, dama irin haka idan an zo sarkin gari ko mai garin gari ko kuwa tsageran gari wanda ya gagari uban kowa ke zuwa ya tarbi mutanen, in da karar kwana a kansu ake farawa

Salama ya yiwa sarkin yana mika masa hannu sannan tar yana kallonsa ido cikin ido

Jiki na bari Sarki ya karbi gaisuwarsa yana tambayarsa hanya da zarcewa da magana kamar haka” mai gida, na san ba auren iri ka zo nema a wannan jeji namu ba? Koma wa ka zo kamawa ka yi hakuri, a yi mana sasauci kar a kashe mu, a kama iya mutumen a tafi, ni kaina inada kankannan yara da mata, idan aka tsame masu ni wa zai ji da su?

Da mamaki Wardugu ke kallonsa , aman da yake Wardugu dan duniya ne sai ya ce” Kai, baka san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi ba?

Ai kuwa gaba daya sarki ya haukace, jiki na bari ya saki kuka ya duka kasa ya rike kafafuwan wardugu ya shiga magiya

Ayya dake cikin mota ta dake lebenta na kasa ta kali sojan nan ta ce” ka karasa da mu, na san wardugu wani lamarin ya shiga na tsawatar masa tun kafin abin ya birge shi

Walyn ce ta juyo da sauri ta kalli Ayya, a ranta ta ayanna wai ta tsawatar masa, sai son ta nuna ita kadai ta isa ta juya shi, ta ja tsaki a ranta a fili kuwa ta ce” Hum tana tabe bakinta sosai

Sojan ne ya juyo ya ce” Hajia, ki yi hakuri, nan ya ce na ja na tsaya idan na matsa bai bani umarni ba ni da shi ne

Da haushi haushi ta shiga bude motar wanda sojan bai ankara ba har sai da ya ji ta bude ya juyo da  sauri , har ta sauke kafarta guda ta ga Wardugun ya dawo da saurinsa gefen da take

Yana zuwa ya ja ya tsara mata ya ce” Ayya maman Wardugu, kece ikon mai sanya Wardugu cire wando ta kai, Ayyana kar ki yi fushi kin ji? Koma motar mu karasa sai ki yi masa tambayar ai sarkinsu ne

Da mamaki ta saki baki tana kallonsa, sarkinsu? Aman me ya saka shi kuka da dukawa ya kama kafar wardugu? 

Dan murmushi ya yi bayan ya saka mata lafayarta ciki ya rufe ya bada umarnin su karasa inda sarki yake

Suna karasawa Ayya ta bude tana shirin fitowa sarkin na karasowa ya dan risina yana gaisheta,

Ayya ta kalli wardugu ya dan sakar mata murmushi

Kai ta girgiza ta sauka sosai ta gaishe da sarkin kafin take fada masa abinda ya kawo su

Wata ajiyar zuciya ya sauke a bayane, ya ce” A garinnan Sofo mai bada magani kwaya daya mukeda, ya sufa sosai, gidansa da dan nisa da kasuwarnan sai mun shiga gari sosai

Ayya ta amsawa sarki da ba damuwa su je

A cikin motar nan sarki ya shiga inda yake dan hangen Wardugu ta madubi lokaci zuwa lokaci, ya yarda da ake cewa sarkin sojojin fa masifafe ne , bashi da dar, in ba rashin tsoro ba du irin yanda ake tsoron abzinawa da asiri shi a gabansa sai dai ma shi sarkin ya ji gabansa ya fadi maimakun na wardugun ya fadi, lale yaron ya sha ya jiku ya tada kai , rabonsa da kuka tunda aka zo masa da sakon Gaishat ta tafi baban birnin niger inda ya yi tunanin shikenan ta gudu me ta bar shi…..(wani lamarin dan gyara nvl dina ne fa, sarkin abzin ba wasa walahi????????)

Basu zame ko.ina ba sai anguwar baba Sofo

Suna tsayawa mutane suka cika wajen, tunda sun ga sarkinsu a tare da mutanen ai shikenan sai suka sakin jikinsu da su harma ake matsowa a shafa motar sai a kwala ihu da yaren buzanci a ce” nima na taba, mota mota a garinmu, mota har gidanmu, 

Du ja sukai a lokacin da mutanen ciki suka fito gaba dayansu, suna masu binsu da kallo, girma da yannayin tsarin halitar wardugu ta basu mamaki, suna da mutane dogaye sosai sai dai ba masu fafadan kirji da manyan damatsuna haka ba, sai kuma matan dake tare da mutumen da dayen sojan, kun san dai Ayya gwadar ado ce, bale Walyn farar mace alkyabar mata, walyn farar batuba ce tas tas tas, Ayya ce ma baka domin Ayya baka ce mahaifin wardugu ne farin batube shima tas tas tas , sai sojan dake saye da kayan sojoji komai harda bindigarsa da katon takalmin nan nasu da komai sai muzurai yake

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button