BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Sarki ne ya amsa gaisuwarsu kafin yake kai dubansa bukar Sofo,

Bukar kanta ta tsufa du ta zuzube sai abinda ba za.a rasa ba, ga dati sosai a dan nesa da wajen domin an yi rasuwa baka bata samu zuwa ta share masa ta gyara masa ba,

Ruwa kawai take zuwa ta dauko masa ta koma 

Nuna masu wajen ya yi bayan ya samu ya shiga ya tarar yana zaune saman buzunsa da carbinsa yana ja ya kurawa waje guda ido yana ta istighfari(Allah ka bamu nitsatsen tsufa in muna da rai wanda zai kara kusanta mu da kai ya Allah)

Gaishe shi ya yi ya juya inda sofo ke bin kofar da kallon mamaki, me ya kawo Sarki har wajena? Kuma hayaniyar me nake ji haka?

Ku shigo;

Sarki ya fada yana dubansu

wardugu ya ce” anya kuwa? Me zai hana ya fito???

Ayya ta kallo shi ta ce” Wardug…..

Da sauri ya yi gaba ya fara nufar yar bukar sofon a ransa yana ayyana ai idan Ayya ta nadaka toh fa tana yi da kai

Shishiga sukai banda sojan nan, 

Walyn na saka kanta ta yi baya tana kakarin amai da coshe hanci, a fili ta furta” kai ina , ba zan iya ba!

Ayya ta karasa a hankali kusan tsofon dake zaune ya zuba masu ido gaba dayansu yana mai binsu da kallo, ko gezau bai yi ba daga zaman da yake sannan yana jan carbinsa cikin nutsuwa 

A hankali ya amsa salamar Ayya da ta nufo shi cikin nutsuwa ta tsugunna dan nesa da shi aman suna facing din juna

A hankali ta ce” lokaci mai tafiyar da abubuwa, lokaci mai bayanna abubuwa, lokaci mai rarabe abubuwa, 

Baba tsufa ya zo haka? Allah ya sa mu cika da kyau da imani

Murmushi ya yi na gano wacece ita, tabas ya ganeta, idan ba zai manta ba shekaru sun kai talatin da suka shude ya sha kai mata magannin athsma na yaronta da bai fi shekara hudu a lokacin ba tana karbar masa aman ya ki karbar komai da sharadin sai yaro ya samu lafia

Murya na rawa baba tsoho ya ce” y’ata ke ce a garin timiya? Ya jikin yaronki? Na koma ban same ku ba sai na yi adu.ar Allah ya sa ya warke 

Ayya da murna ta janyo hannun Wardugu dake tsaye kikam ta ce” baba ai gashi, kana ganni soja ne, cikin ikon Allah magannin nan mun ji dadinsa, nima a raina kake, na nemeka Allah bai yi ba, kwanan nan na yawaita mafarkinka, a sifarka ta da hakan ya daga hankalina na saka aka nemo min inda kake, shi ne na zo na yi godiya sannan na yi salama kamar yanda na dauki alkawari, 

Baba na murmushi yana kallon wardugu wanda shima zuwa lokacin ya risina, yana kallon tsohon yana kidaya shekarunsa a ransa, ya yi imanin a kadan ya linkasa uku da rabi, 

Baba ya maido kallonsa wajenta, kafin yake bin dakin da yake zaune da kallo, ya yi murmushi bai ce komai ba

Ayya ta ce” Baba ka yi magana mana, 

Baba ya dago yana dubanta ya ce” kaya y’ata, ki dubi dakin da nake ciki a zaune a yanzu, me ya rage min? Me zan yi da arziki? Kyakyawan karshe kawai nake nema, shekaruna dari da ashirin da uku a duniya a hasashe mai yiwuwa na fi, 

Kallonsa kawai suke suna masu adu.a a ransu, adu.a suke da Allah ya datar da su da irin tsufan nan, wanda zaka yi ram da kai da carbinka, 

Jikin ayya ya yi sanyi sosai , a hankali ta zauna a kasar dake dakin tana kallonsa, murya a sanyaye ta ce” haka ne baba, Allah ya sa mu cika da imani……

Aman na so na yi maka wani abin da zai faranta maka, da zaka aminta ma da mun tafi da kai mun kula da kai

Baba tsofo da kansa ke kasa cikin rawaninsa ya dago yana kare masu kallo, ya yi imanin wannan matar da muguwa ce da bata bi bayan alkawarin da ta yiwa talaka futuk kamarsa domin ta san bai isa ja da ita ba domin zamani ya zama mai abu shi ne sarki, shi ya isa shi ke da magana ya dora doka, aman du ta manta ta tako ta ci gari da gari, ta ratso sahara du dan ta yi masa godiya sannan ta cika alkawarin da ta dauka,? Sannan ya san ba yar yankan kai bace domin ba da kansu suke nema ba kawo masu ake har gida, shi kam ji yayi gaba daya ya samu nutsuwa a zuciyarsa da shawarar sa,

Murya a sanyaye ya ce” tabas ina da bukata mau girma baiwar Allah, sai dai ban san ta inda zan fara ba, banma san ko za.a dace ba, 

Hankalinta ta maida kansa ta ce” Mecece ita?????????????……..

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        1⃣5⃣

Baba cikin yannayin damuwa ya ce” me zai hana na baki auren y’a? 

A nitse ayya ta ce” Auren Ya baba? 

Baba tsoho ya ce” eh, domin shi kawai zan nema a bada yarinyar dindindin , 

Aman baba wace yarinya ce wannan?? 

Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce” yarinya ce mai tarbiya mai ladabi da biyaya, yarinya ce mai nutsuwa, bata da kwaramniya, inda aka ajiyeta ta zauna kennan sai an ce ta tashi, yarinyar nan ina jinta a raina tamkar yar da na haifa, a kulun damuwana na mutu na barta a wannan hali, tana cikin halin matsi dan kawai Allah ya yita *BAK’A*  sai dai ni murnar hakan nake domin fatarta ya sa har ta kai warhaka sai dai har yanzu bata samu mijin da zai aureta ba a kauye ta girma sosai shekarunta goma sha takwas a duniya , 

Jim Ayya ta yi tana kallonsa, kafin take cewa ” me dinka ce Baba?

Baba tsofo ya kalli Sarki dake kallonsa shima cike da rausayawa, da wani ne duda tsufanda in dai yana iya magana yana gane wasu abubuwan da gudu zai karbe makuden kudin da aka baza masa, sai dai shi bawan Allah ta yarinyar fake tare da shi tun tana yar shekara shida a duniya yake, irin tunanin da iyaye zasu kwana su tashi da shi na gannin yayansu sun samu mijin aure mai nagarta wanda zai kula da yayansu, toh haka baba tsofo yake kasancewa, du motsinsa itace a ransa, tambayar kansa yake ina? Ta yaya? Wanene wanda zai rike masa Agaishat mudin ranta cikin mutuntawa da kauna? Ya hanga ya hango bai samu ba, har almajirinsa ya tuntuba aman ya watsa masa kasa a ido, hakan ya saka shi dukufa wajen kai kukansa wajen Allah, yana rokonsa da ya bili masa da hanya ta inda baya zato baya tsamani, ya bilo masa da hanyar da zata zamo alkhairi gareta,,,,

Sarki ya ce” kanwar matana ce, Sunnanta *AGAISHAT* 

Kana nufin farar  buzuwa?  Ayya ta tambaya

Sarki ya ce” buzuwar ce tabas, sai dai ita wannan Bak’ar buzuwa ce, 

Ayya ta kai dubanta wajen Baba Tsofo da ya yi kododo yana kallonsu, kallonta ta maida wajen Wardugu dake tsaye ya tsareta da ido yana jiran jin me zata ce,? Ya san halin mamansa, ya san Ayya da daukarwa kai, ! 

Murya a sanyaye ta ce” Warduggggggggg……….

Fuskarsa a hade ya ce” Lalalalala, 

Daga haka ya tamke fuska yana kallon su 

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa ta afka tunani (Tabas a al.adar Tubawa ba.a yiwa namiji auren dole, bake Wardugu, sannan idan namiji ya yi aure sai matarsa ta yi haihuwa kamar uku zuwa hudu kafin ya yi mata kishiya idan kuwa bata haihun ba sai ta dauki shekaru kafin ya yi mata kishiya, wannan haka ne ba ja, haka al.adar garin yake, ) Ayya ta kuma kallon su, ya zata yi? 

A hankali ta ce” baba, wannan yaron shi daya Allah ya bani a duniya, 

Sannan bai jima da yin aure ba,

Ban ki ba, ina so idan da hali a bani yarinyar a matsayin yar rikona, yar amanata, in sha Allah zata ci abinda na ci ta kwonta a makwoncin da na kwonta ko wani iri ne, kafata kafarta Har Allah ya bata miji, zan yi dukan abinda ake yiwa ko wace y’a na kaita gidan miji sannan zan bi dukan lamuranta a gidan miji mudin raina

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button