BAK’A CE Page 1 to 10

Baba tsoho ya jima yana nazarin maganarta, baya shakun za.a bada AGaishat in dai sarki ya yi magana, damuwar shi ne: Agaishat zata so bin bakin fuska duda irin matsin da take ciki? Gida fa gida ne, sannan mahaifiyarta zata yarda da radin kanta a rabata da yarinyarta budurwa ba da wani dalilin aure ba ko dangi na jini haka kawai a tafi da ita tare da mutanen da bata sani ba? Ko wannan karon ma isar za.a nuna mata a kuma kwace mata *Y’A*?
Duda haka baba ya kai dubansa wajen sarki,
Irin kallon da baba ke yi masa sai da ya saka ya ji kunya, ya ce” abinda za.a yi, zamu kama baba a je da shi da ku baki daya ga mahaifiyar yarinya da mahaifinta, du yanda hali ya kama zuwa ya fi aike
Sun lamunce da hakan inda Wardugu ya kama baba a hankali ya mikar da shi sarki ya kama masa suka fito yana dan dingisa kafarsa har suka karasa wajen motar inda sojan nan ya bude wardugu ya daga baba a hankali ya saka shi gidan gaba sarki ya shiga suka shishige gaba dayansu Walyn da binsa da kallon meye kuma haka? Shima kallon Ayya dai yake,
Basu zame ko.ina ba sai kofar gidan Algabiitt
…………………. ……………..
Anna, ki yi hakuri haka kin ji? Ki daina damuwarnan kin ji Anna?
Agaishat ta fada tana miko mata gurasa ta kasa da aka kawo sadaka gidan mutuwar
Anna ta lumshe idannuwanta bata karba ba ta bude tana kara bin yayan nata da kallo,
Mutuwar nan da aka yi bai saka Algabiitt ya yi sanyi a lamuransa ba, ya sako Agaishat gaba dole sai ta yi shafe shafe itama ya samo mata miji kamar yan uwanta tamkar damuwarsa ta yi auren ne,
Yarinyar bata isa ta wulga ba sai ya dura mata zagi
Ya hana a yi zaman makoki sai yayanta dake zagaye da ita
Amarya kuwa idan yau wannan ya zo ta ce dan uwanta ne , gobe sai wancen ya zo ta ce kaninta ne, ta mayar da gidan filin kawo kwartayenta ba tare da wani dar ba domin mai gidan ya bata lamuni….
Anna murya a shake ta ce” bana so ya kashe mini wani cikin ku,
Mariama ta juyo fuska du ta yi mata ja abin kuka ta ce” to ki biyo mu mu bar masa gidan mana, dan mi ba zaki bi mu mu yi tafiarmu ba? Kin san abinda ke daure mu a nan ke ce,
Hankalinta tashe ta ce” a duk lokacin da kuka ambata mini abubuwan nan biyu asalina da barin Algabiit bara ku ji na fada maku yau abinda nake ji! Ji nake tamkar lumfashina zai tsaya idan na ji an ce na bar inda Algabiit yake in dai ba da yawunsa ba, ji nake zan fada halaka, ji nake duniyara shi ne, ji nake in ba inda yake ba ba ni! Wani duhu ke rufe mini ido kaina ya dauki nauyi idan na takura sai na tuno wacece ni? Nakan fada damuwa mai tsanani juwa ta ringa dibana du idan aka yi maganar dangina, kun ji damuwata
Suke suke kallonta, Agaishat (Bak’a) kanta na saman cinyar Gaishat, Mariama na zaune gefensu, Fatimata na jingine da garu tana facing dinsu,
Jiki a sanyaye Fatimata ta ce” me ke damunki haka Anna? Wannan ba soyaya bace,
Mariama ta kallota ta ce” wace soyaya? Ai koda an yita a baya a yanzu Ya kasheta da kansa, Me ke damun Annarmu?
GAISHAT ta buda baki zatai magana sai ga Algabiit bugum ya fado dakin yana dan dudukewa dan tsayi
Direct ya zarce gurin Anna bakinsa na rawa ya ce” sai dai su tafi da ke da tsinaniyar yar ki! Ba wanda zai kama ni, ba abinda na yi!
Da sauri ta mike tana dafe kirjinta, tsinaniyar yarki ke mata yawo a kwakwaluwa, wacece kuma? Me aka yi? Su wa zasu tafi da su?
Bata kai ga tambaya ba ya duko ya dago Bak’a da gashinta ya mikar da ita,
Yawun bakinsa ya tatara mai cike da warin Sansani ya tofa mata a fuska ya ce” ga dan iskan tsohon da kike wuni wajensa tare da sojoji, to ki sani sai dai su kama uwarki
Janyeta Anna ta yi da karfi sannan ta yo fallon nasu da sauri dan jin lafia?
Gaba daya yayan nata suka biyota inda Algabitt ya labe yana leke yana kuma sauraron abinda ake fadi
Da kallo Anna ke bin su, sukai mata salama suka shiga gaisar da ita da yaren buzanci,
Ayya ta kalli wardugu dake karewa kowa na wajen kallo, ta ce” ban san bama da wani yare zamu tatauna da ita da alama buzanci kawai take ji
Anna dake tsaye ta ji komai abinda aka fada da yaren da ba zata ce ga sunansa ba, kuma ba yaren da suka yi da likitan nan a asibiti bane……………………………………..
Share this
[ad_2]