BAK’A CE Page 1 to 10

Kanta a kasa ta ce” ki yi Hakuri iya, zan kara kaimi wajen siyarwan ki zuba min kadan yanda zan iya siyarwa
Kanta ta girgiza ta mike ta dauki kwarya ta zuba mata nono dan madaidaici ta mika mata, ita Allah yana ganni dan tana jin tausayin yarinyar ne aman tana da masu siyan nononta a hannu a hannu domin shannunta suna da yawa
Dauka ta yi ta fice a gidan, tana tafe tana jin wata irin juwa na daukanta, bata karya ba, bata ci komai ba sai yanzu ta tuna
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu gu ta dan rakube ta daga kanta sama ta afka tunani
Mu je zuwa ci kin labarin *BAK’A CE*
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3⃣
Suna tafiya ya shigo dakin,
Yanda ya barta tunda ya dungure mata kai haka ya tarar da ita
Ransa bace ya nunota da yatsarsa ya ce” ke,
A hankali ta dago kanta ta sauke kansa tana kallon sa
Y.ayana biyu sun samu miji yan albarkana
Wani abu ta hadiye a makogwaronta, a hankali ta ce” wannan karon wa ka siyarwa yaran?
Da mamaki yake kallon ta, mayar masa da magana ne ta yi? Shi?
Da izgili ya karasa kusa da ita ya nunata ya ce” ke balagazar mace, ke har kin isa ki dube ni ki fda min cewar ni ina siyar da yara? A me kika dauke ni kennan? Matsiyaci? To bara na tuna maki a gidannan daidai da sansannin ( tabar buzaye) da zaki gumtsa sai kin taba tawa ba zaki iya siya ba dan bakya saye bakya saidawa zaune kike dabar ta.kar duwawu komai sai an yi maki,
To yaranna sun samu mazaje sun yi min kyakyawan tayi! Kuma na fada maki idan har na aurar da yaran nan gaba daya ki kuka da kanki ke da yarki dan kuwa ba zai yiwu ya kasance ina ciyar da yar da ban yarda cewa tawa bace bama
Har ya gama bata kara tofawa ba , ya juya ya fice a dakin
A hankali ta zauna kusa da mahaifiyarsu, itama farinta har daukan ido yake,
Hannunta ta kamo ta rike gam ta ce” zan so ki fada mana tarihinmu kafin muma mu tafi kamar su aunty a daina jin labarin mu, ba labari ba aike ba wani motsi…..Allah kadai ya san halin da suke ciki idan suna raye! Ba yace auren wata biyu kawai zan yi, idan na cika wata biyu na kwaso masa kudade na dawo ko ya sake ni ko bai sake ni ba sarki zai hana shi shigowa garin …….. ki daure ki fada mana tarihin rayuwarmu Anna (mama)
Su waye mu?
Ina ne asalin asalin mu?
Su waye dangin mu?
Bamu da kowa ne sai mu da ku?
Idan muna da mai ya sa ba wanda ya taba zuwa inda muke? Ina son sani ANNA
Jajayen idannuwanta ta sauke kan *Gaishat*, wai ita nan mai damar ce domin ita bata hantarar Bak’A, sannan tana kamanta bin iyayen su ba kamar sauran ba
Kwace hannunta ta yi ta hade rai ta yi mata nuni da kofa
Ta san kan zancen dan haka ta mike ta fice daga dakin
Kallonta yake tunda ya kirayeta ta zo turakarsa tana zuwa ta tube du wani abin da sunnansa sutura a jikinta, ta tsaya masa a gabansa wato gashi ka yi ka gama na koma
Kansa ya girgiza kafin yake tsareta da idonsa, ya juyar da kansa ya kuma kallota
Can ya ce” Nadia, haka zamu yi ta rayuwa? Ke ba zaki taba saukowa ki bani kulawar da nake bukata ba?
Saurin zubewa ta yi kasa ta ce” ka yi hakuri Uban gidana, ban san zan bata ranka ba kar ka hada ni da Ba (Aba)
Idannuwansa ya lumshe, a gaskiya Allah ya jarabe shi da matsanancin son yarinyar,
Yarinyar ce ko a cikin bugaje (buzaye) ta fita daban, ta hadu iya haduwa ko ba wanka Nadia mai kyau ce, dalilin haka ya amshi tayin aurenta da Ba dinta ya yi masa bisa sharudan kawar da ido da toshe kunnuwa kan karansa da za.a kawo a cikin garin kan yanda yana tafiyar da rayuwar gidansa, aman ya kasa samun nutsuwa da ita……..ya kasance komai zatai masa tana yi ne dan tsoro ba dan soyaya ba
A hankali ya dagota ya jata zuwa ainahin turakar domin yanda yake kwakwarta shi kansa mamaki yake, yanzu dai shekara biyar da aurensu bayanta ma ya kara auren mace biyu ya saki gudar aman har yanzu ta kasa fice masa a rai a kulun yana mai jin zumudin kasancewa da ita…..aman ita ta kasa kontar da hankalinta ko dan matsayinsa na sarkin garin ta murza mulkinta aa tana rabe rabe ne a gidan mijinta
Nadia kennan babar yar *BA*
Ke kin san nawa ne million daya? Jika dari dari har goma fa, an ce Gaishat har million goma sha hudu mutumin ya bada kudin aurenta,
Ke ki rufe min bakin ki, ke fa haka birge ki yake ko? Kina ganni yanda yake aurar da yayan nasa daga sun tafi shikennan ba labari, kudin ya zo bai yi masa anfannin komai ba, daga an kwana biyu ya kashe sai kuma ya fara harin wata a cikin y’ayan nasa, ai sun kusa karewa zamu ga kuma idan wada ya tsanar zai yi shelar ya siyar
Mahaifiyarsu da ta shigo da Buzu (salaya) a hannunta ta kale su ta ce” ke Amina, ki tashi maza ku je ku yi sallah, wannan maganar kun cika yinta bayan kun san ya zama abin gasa a garin nan, sai kun jaza min abinda ya fi karfina ko? Kuma da hakan bata faruwa da ku dan Ba din ku bai yarda da hakan ba, ku kun fi kowa sanni gidajen da basa haka basu fi a kirga a garinnan ba aman zaku zauna mamakin kwaya daya? Kowa ya yi da kyau kai nasa! Ku mike ku bace min a wajen nan kar ku yarda maganar nan naku ta yi tsayi ya zo ya tsige mu baki daya domin ku kun san waye shi !
Sumui sumui suka fice dan zuwa yin alwallah su gabatar da sallah
Sai yama sosai ta kamo hanyar gida,
Tana tafe ne tana dan jin dadin yannayin garin domin sanyin yama ya fara busawa sosai ita kuwa gwanar son sanyi ce sosai
Ba ita ta kai gidan iya mai nono ba sai kusan magariba, ta kai mata cinikin inda iyar ta bata dala ashirin da biyar ta yi godiya ta mike
Har ta kusa fita iya ta kirayeta ta dawo
Ta ce” kin ga , ga abinci nan ki dauka ki ci mana ni na ci na rage, sauran ki yi min halin naki sai na tabatar kina kyankyamina ne na san irin matakin da zan dauka
Fanata ce ta fito daga daki, kmar kulun cikin mahaukacin gayu mai gigitar da jama.ar garin ….Fanata dai y’a ce a wajen yar uwar iya wace ke aure a cikin garin agadez, mahaifin fanata Babarbare ne shi ya sa sunnanta ya fita daban ,
A da fannata ta kasance ita ba fara kar ba ita ba baka ba duda mahaifiyarta farar buzuwa ce,
Aman kasancewarta a can cikin birni, da taraya da kawaye ya saka take shafa mai wanda ya mugun karbarta ta yi fari kar kar kar harma ta fi maman nata farin,
Fannata akoy kyau ga iya daukan wanka
Tana son garin timiya a rayuwarta domin gari ne mai cike da ni.ima
Tunda ta fito take kallonta da mamaki,
Dubanta ta mayar wajen Iya ta ce” iya, yarinyar nan mai maki tallah ce ta girma haka?
Iya ta ce” eh ita dai ce
Fannata ta yatsina fuska ta ce” to aman har yanzu sunnan da ake kiran nata da shi ne? Wato *BAK’A*?
iya ta amsata da kai
Fannata ta kallo wajenta ta kuma kallon iya ta ce” menene sunnanta na gaskiya ne ita wai?
Iya ta kalli Bak’a, ta kalli Fannata, ta ce” sunnan Hajia ne da ita, karfi da yaji Ba dinta ya mayar da sunnanta Bak’a har ake mata kiranye da haka
Da mamaki Fannata ta karasa kusa da ita tana kallonta,
Yarinyar fa nata wani tsararan kyau, boyeyen kyau, duda mugun bakinta ga bakin turkudi na bugajen kauye????????, ga dati da take fama da shi, aman ita tana hango wani al.amari a tatare da yarinyar, to aman me zai hana ta shafa mai itama? A sanninta ba bakon lamari bane buzu farinma ya shafa mai, kai ba buzu ba yanzu abin ya zama larabawama mai suke karawa shi yasa zaka gan su wani farfarfar da su sunna daukan ido, ba sai dan duniya ke shafa mai a duniyarmu ba, mun dauki mai mun mayar da shi abin kmgyaran fata, ra.ayi ne shafa shi idan ka shafa ba mai yi maka kallon dan duniya a karkarar mu