BAK’A CE Page 1 to 10

Abimcinta take ci kanta a sade tana ji yanda Fannata ke aikin tambaya a kanta, tsoro take kar a je mugun kyankyaminta kamar yanda mutanen garin ke yi ya saka take son sannin ko ita wacece dan ta kara samun damar ci mata mutunci, hakan ya sa take sauri dan ta gama cin abincinta ta kara gaba , so take ta siyarwa SOFO goro na dala biyar, ta saka dala goma asusun da take tarawa dan ta bawa Ba ko ya daina tsanarta, Gomar kuwa itama ta ci wani abin
*AGAISHAT*
ta ji sunnanta a sama sama yana yawo, sunnanta na gaskiya aka kiraya,
Da dan sauri ta dago sukai ido hudu da Fannata,
Fannata ce ta kirayi sunnanta na ainahi ba bak’a ba………….
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4⃣
A hankali ta kai idannuwanta kan Fannata dake kara matsowa kusa da ita
A hankali fannata ta saka hannunta ta dago na Agaishat, kallon hannun take tana jujuyawa, fannata ta fahimci bayan bakinta na halitarta da Allah ya yi, akoy tarin dati ga kuma karin bakin turkudi,
Da sauri Ta janye hannunta tana kokarin mikewa daga cin abincin cike da tsoron menene kuma Fannata ke taba mata hannu?
Fannata ta ce” kin ga, ba abinda zan maki
Kallonta take da mamaki domin da hausa radau Fannata ta yi magana bayan Agaishat kadan kadan take jin hausar itama baba Tsoho ke dan koya mata dan abinda ya iya, yakan ce ba.a san gobe me zatai ba
Goshinta ta dafe ta kalli wajen iya ta ga sai faman gyara Sansanninta take(tabar buzaye), tana dan kukulewa da zare tana ajiyewa gefe tana yin kulin kadago kadago (dala biyar biyar )
Kurumci Fannata ta shiga yiwa Agaishat,
Ta yi mata nuni da hannayenta da fuskarta gaba daya,
Ta yi saurin taba ruwa ta nuna mata alamar bata wanka ne?
Agaishat ta shiga faman saka tsohon takalminta na soso tana faman guduwa domin ta saka a kasan zuciyarta wannan abin zai kare ne a wulakanci da tozarci
*WaRDUGU*
Ta fada tana mai daga murya kamar zata kaiwa gabjejen mutumin dake tsaye a gabanta duka,
Ta kuma cewa” WaRDUGU Odon jidu anna indahan yuna yugusnan gwa ( tun kana yaro yake fama da kai)
Kansa ya dafe, ya kai dubansa kan agogon hannunsa, kallota ya yi ya yatsina fuska, can ya ce “Ayya (wato mama), Ayya inda medi mundu tam (wato mama ke rigimarki ta yi maki yawa)
Hannunta ta dora a goshinta ta shiga kai kawo, kai take tana kawowa, can ta dauki wani ihu ihu tamkar tana buda, ta je ta dawo ta je ta dawo, ta kallo shi cikin yaren hausarta da bata fita da kyau ta ce” shikennan rayuwar bariki (gayu) ta lalata min kai, shikennan na zama uwar da ina fadi ba.a saurarena, ko nima zaka kula zazafar gabar da ni ne kamar yanda ka kula da Abbanka (mahaifi)?
Hannayensa ya jimke ya daki garu da su, kafin yake juyowa wajen mahaifiyarsa,
Taku ya yi zuwa gabanta kafin yake sada kansa, shima cikin yaren hausar sai dai tashi ta fi dan goguwa ya ce” Ayya ba dai saboda wajen wannan bugudin (tsofo) ne kike daga hankalinki harda hada kanki kike min da wannan Bugudin (wato mahaifinsa)?
Kanta ta kawar ta ki bashi amsa hakan ya sa ya mike ya fito daga falon
Yana fitowa ya nufi wani dankareran mashin *ROUTIER* jibga jigban nan masu shegen tsada domin daga million daya abinda ya kai har million shida ne, kuma mashin ne ba mota ba…gudunsu ma daban yake da kananun mashin
Bakin gilas dinsa ya fitar ya saka ya tayar da mashin din ya yi masa wani irin ja wanda kana ganni tamkar dambe ake da mai jan da mashin din domin mugun karfi ne da shi ga kyau
Hangame gate mai gadi yayi don kar ya jawa kansa bali wajen Wardugu
Yana fitowa daga anguwa *Plateau* a birnin Niamey ya nufi *Francophoni* inda gidansa yake
Yana karasawa shima tuni an hangame kofar ya shige da gudun tsiya ya silala wani waje da nan ne ma.ajiyar abinda ya shafi mashin da motoci
Dira yayi ya juya da sauri sauri ya shiga hawa matatakalar bangarensa domin bangare daban daban ne da matarsa mai sunna *GALayn*
Wata yar karamar carte ce ya dora mai dauke da hotonsa ya dora daidai wani detecteur ya bada dan kara titeeee kofar ta bude
Caicaicaicaicaicaicai wash, gidan tubawa kamshi, wayo gidan batube ni.ima, bale mai auren gimbiya hajiar hajia, sarkin tsafta, sarkin ado, kwaliya ba dai a nuna mata ba, ta kasance cikin kamshi wanda indai kai ka ce zaka kwaikwaya sai dai ka tashi da mura (gaisuwa yar baba)
Sanyi mai hade da kamshi ne ya buso shi, sanyi mai sanyaya zuciya
Terrace din dakin fara kal kal kal haka take daukan ido ta sha guga,
Tafka tafkan salon ( kujeru) ne irin na zamani masu kalar fari kal kal sai dan coussin kananuwa sosai su kuwa masu kalar baki kamar yanda mauquette (capet)
Rido (wato labulaye) yen dakin suma kalar fari ne, sai dai farin ba kar ba kamar yanda kujerun suke , shi ya fi ruwa da kalar peinture (colern) dakin, shima an saka abinnan na daure labule baki wanda kana ganninsa ka san ba karamin kudi bane dakin ba wani tarkace aman komai ka kai dubanka ka san karshe ne sannan ya bada kala ta mamaki,
Nan ya yada zango, ya daga kansa sama ,
Iska ya furzar yana jin yanda takalmin matarsa ke tahowa kwaskwaskwaskwas
Kamshin da take fitarwa shima na daban ne, ta shafa turaruka har ta gaji,
Tunda ta fito take kallon yannayin fuskarsa, a cikin ranta ta ayanna” wani masifafe kuma ya hargitsa min yannayin miji?
Bata yi kasa da gwuiwa ba ta karaso kusa da shi ta daga damatsunnan hannayensa ta shiga masaging a hankali tana kara kallon yannayinsa
Murya can kasa ya ce” *ADIBIRA* (Matata)
Tsai ta yi tana kallonsa kafin ta ce” qu’est-ce qui ne va pas mon Bb? (Me ke faruwa Baby?)
Kansa ya kawar gefe kafin ya janye hannunta a hankali ya mike ya nufi uwar dakansa
Bakinta ta tabe, Galayn akoy saurin fushi, mace ce iya mace aman bata tunnanin zata tsaya tana wani bibiyar namiji ko waye shi balatanna wardugu? Wardugu zuma ne ga zaki ga halbi, wardugu ko a cikin tubawa tsoronsa ake, mutumin da idan ransa ya baci idan bai samu ya damki mutun ba yake suma? Mutumin da ya wawuri ogansa ya daga sama ya nana da kasa ogan nasa bama na niger ba domin a niger ba marichal, bako ne da kowa ke tsoro yana shayi, gardama kadan ta hada su General Wardugu ya daga shi ya nana shi kasa a gaban yaransa da kuma yaran general, wannan abin ya jaza masa da mukaminsa da komai shugaban kasa ya tsaya kai da fata aka tura shi daji can wajen mali sai da ya yi wata hudu ya sauko, aman maimakun abin ya yi sauki sai kara gaba da yayi, mutumin dake gaba tukura da mahaifinsa , fada yayi gwa da gwa cewa abansa ya kiyayi hanyarsa kan laifin da ya boyewa kansa sai shi sai mahaifiyarsa suka sani, ita a wa zata tsaya ta bi bayan wardugu da idan ransa a bace ka bashi hakuri yake hucewa kanka? Du irin yanda yake ikirarin shi yanzu ba ruwansa da fada da mutun na gugar jiki karya ne ! Ka yarda ka yi gigin kai masa wargin baya ce masa komai ya ciro daya daga cikin wukaken dake jikinsa ya burma maka idan ya so a kashe shi, Wardugu nada zuciya ta ainahin tubawa….