BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Mu je zuwa labarin *BAK’A CE*

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                      5⃣

Mikewa Galyn ta yi ta fice itama ta bi ta babar kofar danma ya san ta yi tafiyarta ta je ta kara bada turaren ruwa a jikinta ta fito ta je wajen da kys din motoci suke ta dauki guda ba tare da ta tsaya zabe ba domin kuwa kaf ciki manya ne

Tana fitowa ta shige motar ta tayar ta fice abinta wajen auren kanwar kawarta tana mai duba carte dinta ta bank dan ta tsaya ta ciro yayan banki na kari a wajen wasa…. 

      Wannan kennan

Ya yi kai kawo ya fi a kirga, ya dafe kansa yana tunanin irin nacin mamansa kan abu, ita yanzu dan wani tsoho can daban zata dame shi kan sai ya kaita, shi ya san wani bai isa ya bashi lafiya ba aman har fadi take shi ya taimake shi yana yaro, an dai dudura masa itatuwa haka kawai za.a kashe masa kwayoyin jiki

Tsaki ya ja mai karfi, ya mike ya shiga cire kayan jikinsa masu nauyi ya rage masa culotte kawai

Da dan gudugudu yake kara taka matatakalar benen bangarensa har ya karasa bangaren da piscine dinsa take

Ba tare da wani tsaye tsaye ba ya fada cikin ruwan nan ya shiga iyo tamkar wani kifi yana kai yana kawowa ba wani alamun gajiyawa a tatare da shi

Ba ita ta kai gidansu ba sai can dare har wajen karfe tara abinka da jeji shiru garin sai kukan tsuntsaye sai jefi jefin samari da yan mata ana tadi domin sukan kai har goma suna tadinsu

A hankali ta shige gidan nasu ta samu ta leka kanta 

Fitilar kwai a kunne, sai dai tana jiyo minsharin Abansu dan haka a hankali ta kutsa ta nufi dakinsu yan matan gidan

Mahaifiyarta ta gani zaune saman abin sallah, da alama ita take jira duba da irin yanda ta tsareta da ido 

Jiki a sanyaye ta karasa kusa da ita kanta duke ta ce” ANNA

Bata amsata ba sai kureta da ta yi da kallo,

Ta jima duken nan, aman bata mike ba domin ta san wani abu guda da mahaifiyarta keda na buzaye tamkar wata yar gidan sarauta koda yake du buzuwa ko buzu haka ne dadaya ne basu da shi wanda mutane ke jifansu da sun cika *Ashak* ,

Can kamar ba zatai magana ba ta ce” kin ga, ko wani hali zaki shiga, ko wace rayuwa zaki fuskanta *AGAISHAT*, ki guji sabawa mahalicin ki, ki rike mutuncin ki , ki ci gaba da hakuri watarana sai labari

Kanta take gyadawa, kuma wani dadi ta ji har cikin ranta, ko ba komai ta san a duniya bayan baba Sofo Annartama bata kyamatarta, tana kawar da kai a lamuranta ne dan gudun fitina, irin yanda Abanta ke binta da shari kwararo kwararo ya sa mutanen garima haka, ba mai kulata da daraja, ko magana za.ai mata ba.a mata ita a mutunce, ya kasance ko gaishe da mutun ta yo sai ya yi mata yatsina domin Abanta bai barta haka ba har shari ya yiwa annarta kan cewa ko dai wajen baba Sofo take zagayawa gannin irin yanda ya damu da ita ?

Wannan wutar kafin ta mutu sai da aka sha tashin hankali, baba tsoho ya yi kuka sosai aman bai daina kula Bak’a ba domin tana da mutunci yarinyar, shi Allah bai azurtashi da yin auren bama domin bashi da lafia ko ya yi ba anfani hakan ya sa yake jin yarinyar tamkar yar da ya haifa, itama tana mutunta shi tamkar mahaifinta

Mamanta na gama fadar haka ta yi shiru kanta itana a saden tamkar tana gaban sarakuwarta

A hankali ta mike ta nufi dakin su

Tana zuwa ta tarar du sun yi baci abinsu dan haka ta dauro alwallah ta shige ciki ta tayar da sallah ta shiga ramuwar wa.inda batai ba , tana so du rintsi ta ringa samun gurin sallah sai dai tana tsoron mutane da kwagirar su, yanzu za.a wulakantata dan haka take bari idan ta zi gida sai ta yi wanda bata samu ta yi ba

Tun karfe takwas na safe Aba ya fice bayan ya canza rawaninsa daga baki zuwa maroon turkudi sabo fil, ya sayi tufafi ya sayi rawanininka harda waya, ya fito sabo kudi sun fado shikennan a haka zai fada su tamkar wuta shima ya dankaro aure daga an cinye kudin shikennan ta gudu abinta

Bai jima sosai a wajen ba ya dawo,

Daidai lokacin Anna na fitar da dawar masararsa a ruwa wace ra jika dan tana son yin garin tuwo

Bai yi mata magana ba ya zarce dakinta dake baban daki idan ka cire nasa a gidan, daman dakuna uku ne, da nasa da na Anna da na yan matan gidan

Bai yi wata wata ba ya shiga kwasar kayanta yana kaiwa dakin yan matan yana jibgewa gefe guda, 

Ba wanda ya tanka shi ko ya yi mamakin lamarinsa domin sun san halinsa, haka yake du idan zai yi aure dakin mahaifiyar su yake fitar da ita ya hadeta da su ya kawo amarya, bama zai barta a dakinta ba sai dai ya hade su ya kawo amarya su sha shagalinsu ba wanda ya isa ya yi magana yanzu zai cici masa uwa ko waye

Ko kallo bai isheta ba, don ta daukarwa kanta alkawarin in dai ba mutunci ne lamarinsa toh ba zatana kai kanta yana wulakantata ba gaban yayanta. 

Sai da ya gama fitar da komai kafin yake fita ya shigo da magini

Sosai aka gyara dakin ya yi tas da shi 

Tare suka fita , sun jima sosai kAfin yake dawowa

Wannan karon kuwa masu shigo da kaya ne 

Mariama dake wanke fuskarta bayan ta shafa kurkum ta yi tsai tana bin kayan da kallo,

A gaskiya siyayar idan ka yita a kauyen ka isa ne, tun daga gado har kayan abinci na gayu ya kwaso abinsa sai dai abin haushin babu rabonsu a ciki na amarya ne, domin idan ka auri jar buzuwa ko duniya zaka kai gidansu nasu ne ba za.ai mata komai ba sai dai a kawo maka ita daga ita sai butarta (a kauye fa kar a ce inji sajida????)

Sai da suka gama kawo kayan tsaf Mariama ta je faban mahaifinta ta tsaya masa kerere a gabansa, somin kuwa in dai haihuwar rashin mutunci ne ya haifa Mariama ta isa ta iya tsayaya tamkar mahaifinta

Ido tar cikin nasa da yaran buzanci ta ce” Aba ya haka? Na ga ka fara kwaso kaya alamun aure zaka yi? Ya baka fitar da mu ba? Baka ba anna kudin siyayar kayanmu ba?

Kun san wasu iyayen sun fi son yaya masu tsayayar nan, domin Aba yana dan shayin lamarin yar tasa domin a yanda yake gani tama fi shi rashin mutunci dan haka ya dan gyara rawaninsa irin zai yi magana ya ce” wani siyaya kuma? A sanina cikakiyar buzuwa ba.a yi mata kayan daki?

Ta yatsina bakinta ta ce” sai kuma cikakiyar buzuwa ana yi mata sutura

Karya ne Mariama, ya fada yana matsowa kamar zai doke ta, ya ce” ku ne yayan zamani kuke zuwar mana da abubuwan da suke neman fin karfin tunanin mu, ko uwarki haka aka bani ita, haka ake kai ku daga ku sai turkudin amarci da buta, kudin auren ku kuwa mu iyayen ku ke siyan maku kadara mu ajiye maku a nan wanda idan kun waiwaya zaku ji dadin su

Wani malalacin murmushi ta saki tana kallonsa 

Ya ci gaba da fadin” ke da kin ga minister ne ya turo a nemi aurenki, ya saya maki komai, sannan ke da auren wata shida ne zaki yi ki kwashe komai ki dawo mini mu more da kudi? 

Tar ta kara saka idannuwanta cikin nasa kafib take juyowa ta ga mahaifiyarta ta fara daka dawar da ta wanke ta baza a rana ta sha iska tana so ta mayar da ita gari kennan , ta kuma kai dubanta wajen yayarta *BAK’A* dake ta dirzar wankin yan matan gidan harda na su kanenta ita dai burinta idan sun tashi su bata konce, ta kuma kallon mahaifinta dake kokarin shi dole sai ya yi mata wayo, wai wani harda cewa wai ya siyar masu kadara, shi? Kudin aurwnsu bai taba wata a hannunsa ba komin yawansu zai kashe su  ne ya dawo talakansa marar mutunci, yan yatsunta biyu ta hade ta yi tap tap da su suka bada dan sauti kafin ta ce” ka kirga kudi, ina so ka bawa Anna kudi har million shida a cikin kudin da ka karba na auren mu domin na sani cinikinmu kake tamkar abin siyarwa baka amsan kasa da goma, ka bamu shida mu je birni tare da Anna mu siyo kaya mu dawo idan baka yi haka ba zan shiga duniya na saka ka a matsala kai da wanda ya kawo kudin aurena, ka san ni horonka ce 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button