BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Yana tsaye bami bude har ta fice a gidan, kallonsa ya dawo wajen Anna, da sauri ya karaso ya ce” kina jinta kika yi tamkar baki gani bayan kin san tana jin nauyin zuciyarki? Ko ke kika kitsa mata a taru a cuce ni? Har million shida? Ai kudin sun kusa karewa idan na baku haka! 

Bata bashi amsa ba ta ci gaba da dakanta , nan ya juya wajen Agaishat ya ga shi take kallo

Ke dan ubanki daina kallona da wasu tula tulan idannuwanki masu kama da na mayu, shegiya da aka kwaso cikin ki a waje aka yayaba min, dan bakin jini ko almajiri na yiwa tayi guduwa yake, zan zo in kwakwale miki idannuwan nan in baki a hannayen ki ki je ki kaiwa tsohon dan iskan nan da kike zuwa kina wuni wajen shi wama ya san ko me yake maki a bukar nan

Da sauri Annan ta juyo wajen shi, ta kai dubanta wajen Agaishat da ta sada kanta jikinta na bari, tausayin yarinyar ya kara dirar mata, nan ta kara gane shi ya sa idan ta fice take cika dare dan kar ta hadu da mutumin dake mahaifinta aman ya zamo makiyinta , ta rasa da wata kalma zata kirayi mutumin dake miji a gareta, ta san ya yi karatu, sai dai son kudinsa ya fi imaninsa yawa

A hankali ta ce” ki je kawai zan idasa maki aikin

Da sauri ta ajiye wankin ta warware mayafinta na bakin turkudi butubutu da shi ta yane jikinta gaba daya ta fice har tana hardewa tana waiwayen gidan nasa

Bakin wata bishiyar mangwaro ta zauna ta fashe da wani matsanancin kuka mai karfin gaske

             Ku mu je a labarin Bak’a ce na sajida

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        6⃣

Kuka take tana murza goshinta a kan cinyarta dake lulube da turkudi, hawayen nan ya jika turkudin ya yayakune sannan ya gogun mata a fuska ya kara rinar da fuskar ya kasance wani waje ya fi wani wajen duhu sosai fuskar du ta yi jirwayi da ita

Sai da ta ci kukanta har kanta ya fara ciwo kafin take yin shiru, mangwaron nan ta kuma kallo gannin du ya yi jajajir ya nuna ya saka ta mike ta gyara zaninta da kyau ta kama kokarin hawa ,

Da kyar ta hau bakibakin ta kamo wa.inda ke kusa ta tsintsinka ta diro ta zauna nan tana gogewa da hannunta sai kuma ta sha abinta, yau bama zata iya zuwa wajen tsoho ba ta san yana da ruwa goronsa kuwa ta kai masa gobe sai ta yi safiya ta je wajen shi

        Wardugu, yanzu yanzu?

Kansa ya dafe ya ce” Ayya ko kin fasa tafiyar ne? 

Da sauri ta mike ta nufi dakinta tana dafe kanta, yaron nan akoy kagauta , bashi da hakuri yanzu in ba rigima ba a kai tsayen nan ya zo yace su yi tafiyar da a yanda ake bata labari garin can cikin jeji ne? Aman ba komai irin yanda take mafarkin mutumin nan abin ya tsaye mata a rai, tana tune sun yi da shi idan yaro ya samu lafiya sai ta bashi salama da abinda ya sawaka sai dai ta zo tana yiwa Wardugu magani da magungunnan aka tashe su daga garin aka maido su Capital tun daga shi bata kara ganninsa ba domin ta neme shi sosai, sai kwanan nan take jin lanarin yanzu tsufa ya kama shi sosai baya yawo yana garinsa na haihuwa harma an fada mata sunnan garin , tana son sauke nauyi domin kuwa tun daga kan maganin wajensa Allah ya aminta wardugu bai kuma Huka ba sai tana gannin haki ne ta je ta sauke ba wanda ya san gawar fari

Nade ta fito da lifaya mai ruwan ja da kyalkyalin zaiba, lifayar sai baza kanshi take , Ayya ta  kwana biyu a duniya aman karshe ce, akoy iya ado da sannin hakin turare, idan ka ganta sai ta birge ka gata da saka zinare tamkar ba da kudi take siya ba, danta ya bata damar murza mulkin da ta ga dama

Tafiyar manya ba.a kwasan tufafi, mai aikinta baturiya ce ta fito da wata yar valise (yar akwati) yar karama wace a ciki ta saka du wani abin bukatarta ta nufi kofa dan kaiwa cikin mota

Gaba ya yi yana amsa waya da aminiyarsa, kawarsa, wace du duniya itace babar kawarsa sai wa.inda ba za.a rasa ba, itace basa fada, ta iya tafiyar da lamarinsa ta iya zama da shi , sannan du irin yanda ya ki jinnin jajayen buzaye ita wannan baya iya kyamatarta , ba.a shaifar mutun aman shi zai bigi kirji da halayen *ALHINAYETT* 

Kana nufin yanzu yanzu? Bama zan yi maku bankwana ba?

Wardugu ya ce” Alhinayettt bafa wani jimawa zamu yi ba, ke dai ki yi mana adu.a

Yana fadin haka daidai yana zama cikin motar Hilux tamkar wani daki tana fa fadin waje, 

Sai fa ya gama wayar ya dubo AYYA da ta tsura masa ido

Kallonta yake da alamar mamakin kallon domin irin kallon nan ne na tsare mutun idan ya yi karya

Bakinta ta dan turo ta ce” kuma ka ce ba budurwarka bace, mutunci ne bakwa wata soyaya da ita, 

Murmushi ya yi do.in daman ya saka a ransa wannan ne, ya dan sasauto ya riko hannunta ya ce” Anna, aa, Alhinayett aminiyata ce, wace bani da amini ko aminiyar da ta kai ta 

Yatsina fuska ta yi ta ce” karyar banza wai aminci mace da namiji ? Ai ba shi sai idan soyaya ake

Kawar da kansa ya yi ya ce” kin ce a lokacin da ya baki magungunnan da aka dura min ma tsofo ne, kuma har yanzu kina da tabacin yana raye? Ni din ma fa na jima a duniya

Murmushi ta saki ta mika hannayenta masu saye da zobunnan zinariya ta dankwashe masa kansa dan ta san yana so ta yi zuciya ne ita kuwa ba zata yi ba, halayensa tana gannin sai dai ta fada masa domin tun bai san kansa take tafe da shi ba

Sun Dauki hanyar airport dan  zuwa garin Agadez daga nan kuma ya nemi abinda zai kai su garin da suka nufa

Mali yaro ne ke wasa a wajen auren kawar Walyn ,

Tunda ta shigo wajen wasan yake kofata da kiran General wande, Walyn kin fice yaro (Matar general),

Tunda ta nemi wajen da tana iya gannin kowa kowa na iya ganninta ta hakimce ta dauki kafa daya ta dora saman daya, ta karkace kadan ya kasance dankareriyar sarkarta ta zinari ta fito sosai, ta dora hannunta guda saman cinyarta awarwarayenta ma suka fito radau da su, takan dan saki dan murmushi hakoran makarta su bayanna, ta dan juya ta kuma juyar da kanta tana karewa mata da yan matan wajen kallo tana auna su daya bayan daya,

Kari ake masa na hauka aman hankalinsa du ya karkata kanta, ya sani ne udan ta zuge bakin wannan jakar nata mai shegen kyau sai ya yi kwasa, jakar a yashe take kusa da kafarta tamkar ba komai na anfani ciki bayan kuwa a cikinta kudane da dankara dankaran wayoyinta na kece raini

A haka har aka fito daga salar isha.i bata mike ta je ta yi sallar ba suna zaune sun zagaye mawakin da yakan silalewa ya bar yaransa da basu san ciwon kansu suma ba ya je ya gabatar da sallah ya dawo ya dora daga inda ya tsaya

Wannan dawowar da ya yi bai zame ko.ina ba sai gabanta domin ya lura yau yan mulkin ne, yan na isan ne, tana son nuna bambanci tsakaninta da sautan matan wajen, 

Yana zuwa ya shiga kodata, yana waketa, yana wake jarumtar mijinta

Kanta ya fashe , ya yi gingirigin

Ai kuwa ta dauki jakar nan ta yage bakinta ta shiga zuba masa masu aku wato jika goma goma tana dangalar masa tana yi irin bata san ciwonsu ba sai da ta karar da jimki biyu wajen ya cika da ihu wata kawarta guda na daukanta vidio dan ta tura mata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button