BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

A wannan rana an jima ana wasa wanda Walyn bata bar wajen wasan nan ba sai da aka gama sai da ta ga karyar ko wace yar karya kafin take mikewa ta dauki jakarta kawayenta masu mata fada suka biyo bayanta har sai da ta shige dankareriyar bakar motarta bayan ta wankesu suma da kudi ta tayar ta halba bakin titi a lokacin har karfe goma sha daya ta buga na dare

Garin niamey capital ta niger du wanda ya taba shigota ya san gari ne dake baje ta ko.ina da polisai

Basa wasa kame suke tun karfin su, in dai ka kuskura ka taka doka toh fa zasu damke ka ne ba sasauci

Tukinta take cikin nutsuwa,

Danja ce ta tsayar da ita bakin inda polisai shida ke tsaye suna duba takardun mota na mashin, da kuma takardar shedan kai wanene 

Hankalinta konce take jira danja ta saki domin ta san sun san number motar general ko sun kurbi giyar bera ba zasu tunkareta ba koda kuwa ta taka dokar domin ta tsira tunda ta hau motar *DOKA* gabadaya

Kwonkwonkwon karar kwonkwasa motarta, 

Da mamaki ta dubi wajen 

Wani saurayin police ne fuskarsa daure tamau ba alamun wasa a tatare da shi

Da yannayin rashin mutunci ta sauke gilashin motar ta sauke masa idannuwanta masu nuni da baka da wayo

Shima fuska a daure ya ce” madame vous etes en état d’arrestation, veillez sortir calmement nous nous occuperont  de la voiture (Madame mun kama ki  ki fito cikin nutsuwa zamu kula da motar)

Da mamaki take yi masa kallon sakarai, baki bude ta nuno shi da yatsarta ta ce” kai aman kai sabo ne ko? Waye kai? Ka san ko wacece ni?

Sadowa ya yi sosai ya saka idannuwansa cikin nata ya ce” eh mun san ko ke wacece, umarnin mijinki ne in dai kika kai karfe bakwai a gari du wanda ya hadu da ke ya kai ki cel ki kwana da safe karfe goma a sake ki daidai gari ya cika kuma a rubuta a jarida!

Dum dum dum take jin maganar tamkar saukar aradu, quoi? (What), ita? A cel? Prison! Ita Walyn? Wardugu wardugu ta fada tun karfinta tana dukan sitiyarin motar ta ………

                      Ohk

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                           7⃣

Ita Wardugu xai yiwa wannan wulakancin? Ta kwana a cikin kaso, batai sata batai komai ba? Dan kawai ta cika dare? 

Wayarta ta warta a cikin jakarta ta shiga laluben numbersa wace ta sam zata same shi

Ta yi kira ya fi a kirga daidai lokacin polisawan sun zagayeta tamkar dai ta yi wani gagarumin laifi

Hanjaki kwonce ya daga domin lokacin yana hakimce kan gadon hotel din da ya sauka ita Ayya tana can gidan sarkin Agadez matarsa uwar gidan ce kawarta ta kusa sosai, shi kuwa ya ki sauka a nan ya je hotel , bayan ya gama harkar kasuwancinsa ne kiran Walyn ya shigo wayarsa, domin Wardugu na sana.a.o.i ya san dadin nema , yakan ce ba dole ya nema ba shi mai Ayya da Walyn

Murya irin ta yan duniya ya ce” adibinira (wato matata ) (readers kar ku manta a wannan nvel yare hudu ne, buzanci, tubanci, french da kuma hausa ) 

Murya ta sasauta tana tura hannunta cikin kannanuwan kitson da ta sha domin dai tubawa basa wasa da kitso ta ce”  Haba mijina ya haka wannan tsatsauran hukuncin?

Murmushi ya yi jin yanda ta sasauto, kennan dai sai yanzu ta nufi gida ko? Muryarsa yanda take ya ce” hukuncin ya yi tsauri ne? Ko bai kai daidai da laifinki ba?

Idannuwanta ta lunshe tana jinsa har cikin ranta ta ce” matarka guda a prison? Ko laifi na yi ina tunanin na fi karfin nan sai dai ka hukunta ni a gida a dakin mu a saman gadon barcin mu ka rungumeni ka matseni ka haukatani da lamuranka , na san ina cika dare kuma baka so aman mutun ai ajizi ne, ka yi mini uzuri Wardugu

Murmushi mai sauti ya sakar mata, ya ce” bara dai mu gwada wannan idan ya so na dawo daga tafiar da baki tsaya kin ji ina zan je me zan je yi ba zamu yi magana

Fashe masa ta yi da kukan kisa , ta ci gaba da lalaba shi dan ya yarda ya yi masu magana su sakar mata hanya ta karasa gida dare na yi

Lumfashi ya sauke ya ce” ki bani daya daga cikin su

Cike da murna ta mikawa wanda ya fi kusa da ita tana zabga masa harara

Yana kara wayar ya kame yana sara masa tamkar yana gabansa

Murya a kausashe ya ce” wasu sutura ne a jikin matata?

Murya a ladafce ya ce” aa oga, mu mun isa mu kali matarka? Bamu kala ba bamu san irin suturar jikinta ba

A ransa ya ayana han, kafin yake cewa” idan ta ki ta fito ku zauna da ita a nan har safiya ta yi , har karfe goma sha biyu na rana kowa ya kasance ya ganta, sannan ku gayaci jarida ku bada cikaken labarin abinda ya faru, kar ku taba jikinta aman bata wahala, ka rike wayarta a hannunka sai goben ka bata! Sannan kar ku nuna mata wasa idan ta so kawo maku tsayaya ku tsoratata da bindiga

Da ” a vos ordres ya amsa kafin yake katse layin ya saka a aljihun rigarsa

Wa ya ga zafi biyu ????

Karfe uku ne fa na dare aman ji kake gam gam gam ana dukan yar kofar gidan nasa

Da sauri *Tibillal* wato mahaifiyar su Agaishat mata a wajen *ALGABIT* mahaifin su Gaishat ta zabura ta kai dubanta wajen *AGAISHAT* dake zaune tsuru tun bugawar farko ta fara tana kallon kofar shigowar su

Mayafinta ta ja da kyau ta fito ta nufi dakin mijin nata

Tana zuwa ta tarar da shi a kwonce tamkar mai baci bayan ya farka ya yi tsuru daga kwoncen yana tsoron mikewa ma

Girgiza kafafuwansa ta fara ta ce” Algabit, Algabitt, ka tashi ana ta buga gidan nan

Hannunsa ya saka ya bige nata ya ce” naki na tashin, bayan a gari an san na amshi kudin auren yaranna , in na bude wani mugu ne fa? Koma waye ya yi hakurin safe mana aman a wannan tsofon daren? Ba zan bude ba!

Gannin ya tashi sai balbaleta yake da fadan da hujojinsa na karya ta mike ta nufi kofar wanda ya saka ya hantsilo ya rarumi wukarsa ya ja tunga yana fadin” kar ki bude mana, koma waye a daren nan ba bakon alkhairi bane! 

Janye sakatar ta yi ta bude kofar,

Fado mata ta yi a jiki tana kuka, jikinta du sai rawa yake, ga sanyin garin aman wata yar ficiciyar riga ce a jikinta, mutumin da ya kawota a rakumi ne ya ce” na ga gidan zan dawo da safe a bani salamata!

Da tashin hankali Anna ta janyota cikin gidan tana ta kokarin kara dagota tana duba fuskarta dake da balshe ko.ina a tsannanin tashin hankali ta ce” *FATIMATA* fatimata , fatimata

Gaba daya mutanen gidan suka fito jin muryar Anna cikin tashin hankali

Da sauri Algabitt ya karaso ya janyota ya ce” Ke Fatimata, meye haka? Daga ina kike? Ya haka a tsiyace jiki a lalace? Ina mijin naki yake????

Dago kumburanrun idannuwanta ta yi ta sauke su kansa, da haushi haushi ta budi baki tun karfinta ta ce”‘””” Aba, sai na kashe shi, kuma ko zaka kashe ni sai na hana ka kara bada kannuna a irin auren da ka yi mini! 

Idannuwa ya zaro ya daga wukar nan nasa ya. Nufota ya saro daidai ita sai aka yi rashin sa.a Anna ta saka hannunta ta tare wukar ta yi mata muguwar sara a gefen hannunta ta yanketa sosai nan da nan jini ya bale 

Ihu yayan suka kwasa, da sauri mariama ta karbe wukar ta yi jifa da ita ta hayayako masa da mugun bacin rai da nuni da zata iya aikata komai ta ce” ka je, kar jini ya biya jini!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button