BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

……….inna Anna ta tafi?????

Gyara kimtsi, mai zamani dan sarki jikan sarki, Buzu jinnin sarauta, yaro mai zamani, taka lafia bijimin sarki, taka lafiya gagara gasa, kai ne na uku baban Rabatima, ka shigo a hankali yarima, taka sanu sanu sarkina

Kirarin da jakadiya ke yi masa kennan tunda ya tunkaro dakin mahaifiyarsa,

 dan dakatawa ya yi har ta yi gyaran murya kafin yake saka kai da salama a bakinsa

Dago kanta ta yi tana murmushi ta amsa shi, a hankali ya karasa yana wata irin tafiya idan ya daga kafa daya kafin ya daga dayar sai ya jima

Dukawa ya yi har kasa kansa kasa ya ce” ta gode Anna, ta gode Amy (Wato mahaifiyar Wardugu aminiyar matar sarki….da Amy suke kiranta bisa umarnin mahaifiyarsu,) 

Murmushi take sakar masa kafin ta ce” oh son tashi mana, amynka ce fa ko dan ka daina zuwa wajena ne?

Yana murmushi ya mike ya zauna saman kushin dake wajen cikin nustuwa suka shiga gaisawa da harsen freinsh domin ita ce kawai yaren da zasu yi su jima suna hira cikib gane abinda suke fadawa juna

Dan jim ya biyo baya kafin yake cewa ” Amy ya labarin Oga ne? Na yi na yi ya siyar min da wata mota aman da yake yan rigimar a kansa cewa yayi aa motar ba ta yara bace, ki ji fa Amy

Dariya suka saka gaba dayansu, Ayya ta ce” Wardugu, Wardugu baya jin magana Aghali, sai hakuri da murdaden halayen Wardugu

Mahaifiyar Aghali matar sarki ta ce” Kawata, wai ina labarin aban Wardugu ne? Ni kam ina mamakin lamarinku, kawai daga wannan dan laifin?

Ayya ta dago tana kallonta, a ranta ta ayanna ban ga laifinki ba, ku baku dauki haka a matsayin laifi ba, 

A fili kuwa ta ce” manta

Murmushi Mahaifiyar Aghali ta yi, Ayya akoy mulki  wannan da gidan sarauta take da an ji jiki domin mace ce mai mulki da isa, ga jan aji, da yake an dauko hirar da bata so daga haka ta katse hirar ta mike tana yi masu salama dan tana son shiga ciki ta kirayi number Wardugu rabonta da shi tunfa suka karaso jiya ba shi ba labarinsa

………..rashin Comment ne kawai zai saka ni daukan matakin siyar da novel din nan ko na tsayar da shi, ????

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        9⃣

Ayya na zuwa dakin da aka sauketa zauna ta jinginar da bayanta jikin kujera ta daga kanta sama, 

Ta jima tana tunani, kafin take sauke ajiyar Zuciya a fili ta ce ” *MARAHUT*, ina ka shiga? Ka san komai ka tarwatsa rayuwarmu, Marahut ina tausaya maka sai dai mutuncina darajata ba zan yarda ka zubda mini ba! Ka zabi wancen rayuwar ko? Ba komai ka je sannu duniya zata koya maka hankali,

Ranta ne ta ji yana suya, yama aka yi ta tabo mata wannan mikin, ta sani da gangan ta tuno mata da maganar domin ta fi kowa sannin abinda ya faru, ita kadai sai Wardugu suka san takamaimai abinda ya faru aman zatana tuno mata da shi , ita so take sai ta yi hakuri bata san ta rufe babinsa ba kuma ko da jaraba sai ya saketa dan bata fatan idan ta mutu ya kasance shine alwalin gawarta (Toh fa???? tubawa akoy zuciya)

Aghali, dan me ba zaka kara aure ba? Matanka biyu yarka daya mace sai matan daki , ko a cikinsu har yanzu ba wace ta samu ciki bayan ina kula da irin zubin da ake maka ana canzawa du wace ta kwana biyu, ko dai baka zuwa inda suken da gaske? Domin na ji kishin kishin cewar wannan matar taka ta shanye min kai,

Mahaifiyar magajin sarki ce ke fada kan ya ki karo aure bayan tana son ya tara yaya

Murmushi ya yi ya ce ” zan kara aure, ki kwontar da hankalinki, 

Ajiyar zuciya ta sauke kafin take miko masa yar akwati tana murmushi ta ce” ka ga Amynka ta kawowa wannan mumunar ( wato yarsa jikarta)

Hannu ya saka ya bude ya gani, sarka ne da yan kunaye na zinari masu kyau sosai kirar yara, murmushi ya yi ya ce” zata je ta gaisheta sannan ta yi godiya…….. wannan kennan

Sai da ta bude lulubarta suka ga mace ce bayan ta fada masu ita mahaifiyar Gaishat ce , suka je suka shaidawa sarki ya bada izinin a shigar da ita bangaren Gaishat din yana mamakin zuwanta da fadawa zuciyarsa ba lafia ba domin shekara kusan takwas da aurensu bata taba takowa ko aiko da kannen Gaishat din ba duda tana yarta ta fari, itama bata wani zuwa gidan du ta takura rayuwarta da tsoronsa ta mayar da kanta ta daki duda kuwa irin yanda yake daukaka martabarta fiye da iyayen yayansa

Tana shiga dakin ta nemi waje nan kasa ta zauna ta sada kanta , da kujeru da komai aman ta fi fanewa zama a kasan nan 

Da sauri ta fito jin sakon Sarki wai mamanta ce ta zo

Tana fitowa ta karaso da gudu ta riko hannayenta a rikice ta ce” Anna lafia? Anna wa ya mutu? Anna na shiga uku me yake damunki? Anna me ke faruwa? Me aka maki Anna? Anna…..

Shiiiiit anna ta fada tana dora yatsarta saman leben Gaishat, itama tana kare mata kallo, yarinyar bata wani karu ba a jikinta na da, sai dan girma daga fuska da ta kara, duda jikinta bai nuna alamar wahala ba aman tana da rama, kanta daure ,

Kunyar Gaishat din ta ji ta kamata, dole ta rikice domin bata taba zuwa alkhairi ko tashin hankali ba, itace ma ke yin kokari idan ta san Abansu baya gari ta leko a tsaitsaye ta koma shima ba wani zantawa suke sai dai su bi junna da ita

Tunani ta afka shin fada mata zata yi ko kawai ta yi shiru ta juya

A hankali Gaishat ta dago habar mamanta, dara daran idannuwanta na gado ta saka cikin nata ta ce” Anna, me ke damunki? Ki fada mani kin ji? In sha Allah ko bani da maganin damuwarki zan taya ki da adu.a

Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Gaishat, Algabitt ne….ya samarwa su Mariama mazajen aure wa.inda bama a niger din suke ba, kin san bani da labari tghmass ita a niger din ma aka bayar da ita, jiya Fatimata ta dawo, mariama fatimata ta kamu da cutar rashin rike fitsari , kin san ba maganinsa a kauye sai asibiti, baki ga fatimata ba, ta dawo wata iri,

Ga irin tsanar Agaishat (BAK’A) , ya sako yarinyar a gaba tamkar ya kasheta dan ya san gardawan da yake zuwa da su dan zaben mata ba zasu zabeta ba, shi ya sa nake kara barinta da datinta, mai yiwuwa ita ta tsira daga muguwar rayuwar da yake saka mini yaya

Shiru ta yi kanta sade tana gursheken kuka daga ita har Gaishat din,

Ajiyar zuciya Gaishat ta sauke ta ce” Anna zan zo gidan kin ji? Sai mu samo abinda ya samu mu samu shiga asibitin

Ido Anna ta zaro ta ce” ta yaya zaki fita Gaishat?

Gaishat ta yi murmushi ta ce” Anna, ki daina damuwa da damuwata, ni na dorawa kaina, tabas Aba ya yi auren dole da mutumin da bana so, mai mulkin garina aman shi mutumen jira yake in nuna bukatata a wani abin jiki na rawa yake yi min ko menene , bana tunanin fita zata zama damuwa tsakanina da shi

Anna ta sauke ajiyar zuciya, ta dago habar Gaishat ta ce” me ya sa toh ba zaki kyautata masa ki kontar da hankalinki ba? Shekarunnan ba fa kwanaki bane, ya ci ace kin zubar da komai kun fuskanci juna, ke Allah ya taimake ki kina cikin konciyar hankali kar ki bijirewa Allah mana

Gaishat ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Anna na kara nade jikinta da fuskarta wato dai tafia zata yi, ita ba zata ki su dawama a nan suna hira da mahaifiyarta ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button