BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Tana ji tana gani Anna ta yi mata salama ta fice a gidan tana fatan kar ta hadu da wani a kusan gidan yarta ta fari , haka kawai take jin kunyar haka …….

Da dare, bayan ya gama salama da kowa ya nufo dakin mai motsa zuciyarsa, ya sani ne ta san sarai itace da shi aman taga damar ya tarar da ta rufe kofarta

Ga mamakinsa yana taba kofar ya tarar da ita a bude,

Turawa ya yi a hankali ya shiga da salama a bakinsa

Kanta ta dago duda tana jin kunya , ta yi kokari ta amsa salamarsa cikin nutsuwa tana dubansa

Da sauri ya karasa inda take zaune, da alama har wanka ta yi, na menene? Taba jikinta ya fara yi hankalinsa a dan tashe ya ce” GAISHAT baki da lafia ne? Me ke damun ki?

Dan bakinta ta turo, kafin take dauke hannun nasa ta kara turo bakin, murya a matukar kasalance ta ce” me ya sa ka zabi aurena ta hanyar baiwa Abanna damar ya ci gaba da tafka tsiya a cikin garinka?

Dakatawa ya yi, ya yi tsai yana kallonta, a hankali ya rungumeta a jikinsa ya ce” ba dai za.a yafe min ba du irin hakurin da nake bayarwa? Ki gane dan adam nake mai cike da izgili da sabo a doron kasa, 

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce” ina so ka bar ni na je gida

Da sauri ya zabura ya cikata yana kallonta, muryarsa na rawa rawa ya ce” zaki tafi ki barni kennan? Yau kin fitar abinda ke cikinki shine zaki yi nesa da ni? Me yasa ba zaki yi mini adalci ba? Ina sane da du ranar da zan zo gare ki sai kin sha madaciya dan kar ki haihu da ni, na so daukan mataki a kanki aman bana iyawa Gaishat, ki yi mini adalci mana

Dora dan yatsarta ta yi saman lebensa jajaji abinka da jan buzu ruwan sarauta ko na kauye dawisu ne, ta ce” zama da kai yanzu na fara, ina son zuwa gidanmu ne dan kanwata ba lafia, muna son kaita asibiti, ka bani dama da ikon da zan yi bajinta a lamarin

Ajiyar zuciya ya sauke, ya rungumeta sosai har kamar ta yi ihun zafi, ya mikar da ita yana kallonta ya shiga warware lafayar da ta yane jikinta yanai mata kallon maita, haka ya idasa shigar da ita uwar dakanta cike da zumudi, wa ya isa in ba ita ba? Ita kadai yake tardowa har dakinta, hajia Gaishat mai sarkin garin *TIMIYA* 

Kamar yanda ya yi alkawari haka ya bayar da rakumi har goma, ya bata kudi masu yawa ya lamunce mata zuwa gari dan kai kanwarta asibiti inda gari ya dauka ana ta lale lale gimbiya ta karbi soyayar sarkinsu, abinka da kauye har yar salah aka yi ta murnar hakan ……………….

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        1⃣1⃣

……..Niamey…….

     Gidan Wardugu

Kawata, dan Allah wai da gadke kike? Gaki ga yan kaso wa.inda suka aikata mugun laifi? Gaskiya oga ya san kan mugunta

Walyn ta ja tsaki ta ce” ke, a dakin nan a nan suke fitsari, mata sai kawai ki ga an dage buje an tsirara fitsari a tsaye, basa kunya basa kyankyamin wajen , kai gaskiya Wardugu ni da shi akoy tashin hankali, ba ni ya wulakanta ba, walahi sai na rama!

Me zaki yi masa? Wardugu ne fa? Kin manta waye shi? Ko mu da muke gari bama rayuwa da shi mun san waye shi, koda kina kema jinnin tubawa ba lale ki iya da rigimarsa ba, ya hada abubuwa da yawa ne, kin ga shine da daya kwalin kwal a wajen iyayensa, shine Wardugu mai sunnan rikitatu a cikin ku, shi ne Batube, kuma shi ne Soja! Wardugu kakarfa, tsayaye, isashe, hamshakin……

Ke meye haka? Walyn ta fada tana kallon kawar tata, 

Ta ce” ya zaki tsaya kina koda min miji sai kace wata mai son min miji? Toh bara ki ji mu a yarenmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta cika wa.adin yin hakan, duka duka shekarana biyu da aure da mijina, ko na kai shekarun da yana iya kara wata Wardugu haramiyar wata mace ce a nan duniya, ban ki ba lahira idan ya dace da aljanna!

Murmushi ta yi tana kallonta ta ce” dadina da ke saurin hawa , toh yi hakuri ni ban kai abin can ba ……….

Bakinta ta tabe ta ci gaba da shafa cream dinta kan kurajen cizon sauron da suka yi mata cin balaki a cikin cel din nan, rabonta da ta saka kafarta kofa tunda abin nan ya faru, gashi ta rasa Wardugu a waya kwata kwata, !

Dogo ne fari kar, datijo ne christa sunansa Docter Lucien, kwararen likitan mata kennan wanda ya karanci abin kuma ya lakanta,

Allah ya taimaki su Anna sun samu gannin Docter Lucien a dasha kuma tausayin irin ciwon da ya gani bayan ya sha fada ya karbe su ya shirya shiga tiyata da ita a washe gari wanda cikin ikon Allah sai da ya dauki awa shida kafin yake fitowa daga dakin tiyatar da ita shi ya hada zufa hakama masu kama masa wanda ba.a jima sosai ba aka gurgurota a gadon mararsa lafia aka kaita dakin da ake kontar da masu yoyon fitsari

Jigum suke zaune suna mamakin wai asibiti ce haka, su kam tunda suka shigo garin a tsorace suke da yannayin tsarin gari, gini ne kala daban daban bene kai kasa na cin kudin masu kudin birni ….

A hankali ta shiga bukar tana dube dube kafin take kallo shi, a kwonce yake , idannuwansa a rufe kamar marar lafia

Da sauri ta karasa ta ce ” Sofo?

Firgigit ya buda idannuwansa ya sauke saman kanta,

Kokarin tashi yake wanda da kyar abin tsufa ya samu ya zauna yana kallonta, murya na rawa irin ta tsufa ya ce” ina kika shiga? AGAISHAT zuciyata ta rikice na rashin gannin ki, na damu na kasa baci, kin ji har zazabi nake dan bana ganninki yata, ina kika je kwana biyu? Kin san ke nake gani ina jin dadi, kece mai daukana tamkar mahaifi, zo zo na ji me akai maki? Wa ya taba min ke ?

Karasawa ta yi tana sakar masa murmushi ta kamo hannunsa ta damka masa goron da ta siyo masa tun wancen ranar, murya a nitse ta ce” mun fuskanci matsaloli ne a gida Sofo, aman yanzu alhamdulilah mun gode Allah, Su Anna sun tafi birni Sofo, muma watarana zamu je? Zaka tafi da ni nima na ga birni? 

Ajiyar zuciya ya yi jin ba abinda ya sameta na tashin hankali, ya lalubo karfen gurza goronsa ya mika mata ta mike ta darwaye ta dawo ta raba goron hudu ta maida hankali ta gurje masa shi tas ta mika masa ai kuwa ya hambuda yana tsotsa yana dan juya kai irin ya ji dadin goron

Can ya ce” Birni garuruwa, 

A birnima akoy garin da dadi ne da shi sannan akoy wanda sam ba zaka so rayuwa ciki ba indai kai din bako ne

Birni tana tatare da abubuwan firgitarwa, murane sun yiwa abin hawa irin mashin mota yarda, sun yarda da su suna halaka su

Tagumi ta yi ta ce” suna halaka su kamar yaya?

Ido ya dan zaro ya ce” zaki ga dan birni idan zai yi tafiyar da ba wata nisa ba, ba jeji ba, ba abin tsoro a hanya ba, dan tsabar sangarta da son jiki sai ya dare abin hawa abinsa ya tafi a dan kankanin lokaci in abin ya zo da karar kwana sai ya juyeka tamkar tuwon masara nan zigib ka mace shikennan sai kiyama

Murmushi ta yi ta ce” toh ba kace ajali na tarda mutun du inda yake ba? Mutuwa ai kai ka fada min ba.a gudunta kuma ba.a boye mata, kuna Anna ta ce ita mutuwa lokaci ne idan lokacinka ya yi ba tsumi ba dabara zata daukeka ne ko waye kai ko me kake , kai ka ce min mutuwa mai yanke kauna, takan raba da da uwa, miji da mata, kuma kace min kowani bawa da ajalinsa a duniya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button