BAK’A CE Page 11 to 20

Wardugu ya daga kafada ya ce” daga kauye, can cikin kauyen kauye fa ta fito, inama ta ga man bale ta shafa? Allah dai ya sa idan ta dan waye ta zama dan kauye ya fi na birni shegantaka….
Alhinayettt ta ce ” sai dai idan ba tare da Ayya take ba, Ayya ce zata wani bari haka ya faru? Yarinyar ce innocente, dan Allah ka hada ni da ita mu zama kawaye,
Wardugu ya waro ido, a fili ya furta” kawaye? Ki kirani aboki kuma ki yi kawance da wannan? Aa!
Alhinayettt ta yi murmushi tana kai masa dan dukan wasa ta ce” ina son ta zama kanwata ne Wardugu, ina son na kara nuna mata shafe shafe karma ta saka kanta, sannan na kara wayar da ita……
Kafadunsa ya daga irin ita ta gano, kafin yake bude mata motar ya yi mata nuno da ta shiga
Dariya ta yi ta shiga , ta kunna wato dai ta ishe shi da magana ko?
Hannu ta daga masa, ya yi mata nuni da sai ya zo , ta tayar da dankareriyar motarta ta kama hanyar makarantar kannenta dan ta dauko su ta mayar da su gida
Komawa Wardugu ya yi, yana shiga ya tarar da su sai labari suke suna dariya abinsu, Mu.azam kuwa ya kasance du motsi sai ya kali Agaishat dake zaune tana kallon Tv kuri, ita har yanzu mamaki take mutane a cikin wannan allon suna ta magangannu suna komai abinsu, har bayan take lekawa wai ko zata gansu ta nan ta sha yiwa Ayya tambayar kuma yanzu idan suka fito fa? Yanzunma Ayya ta kuna mata wakokin dandali, kalo take tana ta sakin murmushi kumatunta na lotsawa dimple har biyu a fuskarta, wani wajen sai ta rufe fuska idan namiji ya fara rawa, sosai take dan gane hausar da suke tana kara koya ta nan, shi kuwa abin na birge shi, sannan ya yiwa Ayya tambayar wacece ita? Da french, ayyarma ta shiga kora masa bayanin komai…..ya sha mamaki, ya ji wani lamari a tare da yarinyar, yana son inganta rayuwarta……
Wannan kennan.
Wardugu na zuwa ya ce” tashi mu je,
Mu.azam ya mike ya bi bayansa suka nufi dakin Mu.azam din , Ayya ta yatsina fuska a ranta ta ayanna mai yiwuwa ya yi fushi????.
Suna shiga Wardugu ya ce” c’est bon, maintenant tu me dit la verité sur ce qui t’arrive ( ya isa, yanzu sai ka fada min abinda ke damunka!)
Mu.azam ya tsare shi da kallo, a hankali ya zauna saman kujera yana kallon Wardugu,
Wardugu ya karaso ya zauna shima, ya ce” ka san dai kana iya yiwa kowa karya banda ni! So ka fada min tun kafin na hasala Mu.azam, wata irin cuta ce wannan wanda baka taba yi a gabana ba ta zugeka haka? Me ya samu kasan gashinka ? Kana tunanin ban lura ba? To gashinan kasan gashinka a aske! Sai ka janyo sauran ka rufe, du ka zama wani iri? Ka duba fa ka gani wandon vest ne a jikinka ka dauko riga rose (pink) ka saka sai kace mace? Hannunka ba agogo, yannayinka na nuna kama tare da damuwar da ta fi karfin furucinka, ina hawa aiki karfe goma na dare, ka fada mani na juya!
Mu.azan da wata irin murya ya ce” Cancer du cerveau ke damuna….. (cancer ta kai)
Wani irin tsam Wardugu ya yi, ya kaste maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurbat ya mike yana duban Mu.azam, hannayensa duka biyu ya saka ya dafe kansa, baya baya yake ja ya……
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣4️⃣
Wani irin tsam Wardugu ya yi ya katse maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurbat ya mike, duban Mu.azam yake da wani irin kallo, hannayensa duka biyu ya kai saman kansa ya shiga yamutsa gashin kansa , baya baya ya shiga yi da kafafuwansa, bai fi taku hudu ba ya tsaya ya juya ya juyo, hanunsa ya jimke ya daki dayan da shi,
A hargitse ya dawo wajen Mu.azam, so yake ya zauna aman ya kasa…… murya a cinkushe ya ce” yaushe, yaushe? Yaushe ka sani? Ya aka yi ka sani?????
Mu.azam ya mike yana dan sakar masa murmushi yana kokarin ganin ya saka shi ya dan nutsu aman ya kasa kama shi, dan haka ya tsaya yana kallonsa ya ce” Wardugu, har na kai wajen da gashina baya zama fa, ya jima a jikina ciwon ….nima ina gannin alamu a matsayina na likita sai dai ina turewa na ki maida hankali, ya kai ni sai na suma na yi awani a sume, na daina shiga tiyata ba yau ba, ina zuwa asibiti ne dan kar imanina ya yi rauni, ina zuwa ne dan haduwa da wa.inda suka fi ni damuwa, ina yi mana adu.a a tare, Wardugu idan na jima a gabannan na kara shekara hudu a duniya,…
“C’est faut!,(KARYA NE!) Wardugu ya fada tun karfi yana nuno Mu.azam da yatsarsa,
Taku ya yi wajensa ya ce” idan kai ka fada, idanma wani sakaran likitan ya fada na fada karya kuke, karya ne Mu.azam, ku baku isa ku fadi abinda Allah ya boye ba, ba wani mahalukin da ya san ranar mutuwarsa , mutuwa bata shawara, bata fadi sai an ganta, mutuwa na zuwarwa bawa a lokacin da bai sani ba, sannan a lokacin da bai shirya ba domin a kulun bawa baya cikin shirinta,
Wardugu ya yi shiru, gaba daya ji yake jikinsa ba karfi, a hankali ya kai kasa ya zauna nan kasa, waje guda ya tsurawa ido kafin ya ci gaba da fadin” sannan Allah kadai ya san gawar fari, ba wai dan wane bashi da lafia wane lafiarsa kalau za.a ce sai marar lafiar nan ya rigayi mai lafia rasuwa,
Mu.azam da ya karaso , a hanakli ya duka ya dora hannayensa saman na Wardugu, murya a raunane ya ce” ban taba tunanin wani abin zai girgizaka haka ba Wardugu, menene a ciki? Ko dan abin ya shafeka ne baka so ka ji? Wardugu ka yi hakuri, ka daina tayar da hankalinka kan maganar nan, nima na fada maka ne dan na ji sanyi sannan na samu wanda ya san ciwona, Wardugu ka….
Bai tsamaci lamarin ba, sai jinsa ya yi jikin Wardugu, Wardugu da dan ya tsokane shi yake ce masa sai sun yi gaisiwar larabawa, yau gashi da kansa ya rungume shi,
Murya a cunkushe wardugu ya ce” bana so bana so…..
Kasa karasawa ya yi kuma ya saki Mu.azam ya mike ya fice da wani irin sauri …….
A hankali Mu.azam ya hade kansa da gwuiwarsa, , tabas mutuwa Aya ce, duk mai rai mamaci ne, tabas ba karamar ni.ima bane da Allah ya boyewa bayi ranar mutuwarsu, shi gashi, hasashe ne aka yi, likitoci sukai a kansa, rayuwar turai da za.a fada maka komai kwaro kwaro ne, sun kiyasta lokacin da suke gani zai kai a raye a doron kasa sun fada masa, wai basu fada masa rana da lokaci bama aman gashi du ya firgice ya fice a hayacinsa,
Idannuwansa ya lumshe yana jin saukar zazafan hawayensa, zuciyarsa ce ta ci gaba da fada masa” ka zo kasar nan je dan ka kara ninninka ibadunka, ka kara yawaita sadaka da aikata abubuwan alkhairi, ka zo kasar nan ne dan ka samu ka raya sunnar ma.aiki idan Allah ya nufeka, mutuwa kowa yi zai yi Mu.azam, ka daina karaya ka yi hakuri har Allah ya yi ikonsa a kanka,
Wayarsa ce ta dauki kuka ya kai dubansa wajen wayar ya mike daga tsugunnin nan ya daukota ya daga,
Docter me ka yi kennan? Na zo wajen aiki na tarar da takardar barin aikin ka? Saboda ni kake son yin nesa da aikinka ko saboda na fada maka ka yi hakuri a yi maka aikin nan? ……
Kansa ya shafa yana sauraronta, masoyiyarsa wace ke nuna masa kauna, tana son Mu.azam tamkar nama daya na cikin miya, tana son kasancewa da shi, labarin rashin lafiarsa ya gigitata har itama ta kwonta, nan ne ta yi ta fadi tashi har ta gano ana iya yi masa aiki a cire wajen, aman aikin ne keda hatsari sosai, yana iya samun tabuwar tunaninsa, ko ya kasance ya shiga coma wace shigekan daga ita ba zai tashi ba, ko idan Allah ya aminta ya yi jinya sumul ya samu sauki aman shi ya kara kai da kasa ba zai harda a wani buda kansa ba a dawo kuna ba wani succes,