BAK’A CE Page 11 to 20

MU.azam ya ce” Aisha,
Aisha ta ce” ka dawo na roke ka, ka dawo tun kafin lokacin a iya yi maka aiki ya shige,
Ki yi hakuri ki daina kirana Aisha, Mu.azam ya fada da sanyin murya, ya ci gaba da fadin” nawa kuka yiwa aikin? Nawa suka fita? Karshe dai du yawanci daga dakin aikin za.a fitar da su basu san inda kansu yake ba, zasu dawo kulun a jone da inji yana taimaka masu wajen numfashi, da na.urori masu basu abinci, da masu jan fitsari da masu karban kashin su, zasu dauki lokaci a wannan yannayin har ya kasance ko a cire masu na.urorin ko dare daya su tsaya sun daina aiki, su basu dauki kadara suka yi ta ibada suna shinfida a makwoncinsu na gaskiya ba, su basu san a inda suke tsakannin duniya da lahira ba, Aisha, Allah ya dora mani, ba zan kai labari ba! Ki yi hakuri……
Yana gama fadar haka ya katse kiran,
Docter Aisha dake kai kawo tsakannin dakinta da falonta ta dafe kai ta fashe da kuka, yar balaraba kyakyawa da ita, a fili ta furta” innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Mu.azam, in sha Allah zaka warke, sai mun rayu da kai Mu.azam…….
(????????????????????????)
Bayan sati uku
Ayya ce zaune tana nunawa Agaishat yanda ake gyara lale ja domin tana son kunsa mata ne,
Bayan ta tankade shi lukui ta kawo mahanabiya ta zuba masa sannan ta zuba dan madaidaicin ruwa ta kwabe shi sosai ya yi shar da shi ta zuba dan ruwa gefe ta ajiye tana kallon Agaishat ta ce” yi ki wanke kafar mana Agaishat, kin ga yayanki Mu.azam ya ce zaku fita ku zaga gari , ni kuwa na fi so idan mun gama kunshin nan sai ku tafi….
Agaishat ta yi sauri ta shiga darwaye kafar nata ta cire ta dauke ruwan ta kai ta zubar ta dawo ta dauki abin goge kafar ta gogoge ruwan kafin take zama ta tankwashe kafafiwanta Ayya ta shiga daura mata iskwace tana fadin”ki lura dan gobe ki daura abinki kin ji Yar Ayya,
Agaishat ta gyada kai tana murmushi, a kowani lokaci a kowani yannayi ta tsinci kanta tunda ta sauke kafarta a gidan Ayya sai iyayenta da yan uwanta da baba sofo sun fado a ranta, bale yanzu Wardugu kansa da yake yawan hararata a farkp ya daina, shi dai baya shiga lamarinta aman baya hana wani shiga, Alhinayettt ma tana lekowa wani sa.in idan Wardugu na gidan su sha hira da yaren buzanci domin tana jin dadin jin yaren raurau ana hira da ita ba wani kyama, sosai Alhinayettt ke dan gwada mata wasu abubuwan, da hikima take nuna mata wasu yan al.adun yan birni sannan Mu.azam na mugumugun sakata a jiki, yana sakar mata fuska fiye da tunanin mai karatu, idan ta kali kayayakinta, suturun da suke malakinta a yanzu, sai ta ji hawaye na neman zubo mata, tunaninta me yan uwanta suke sakawa a yanzu? Wani hali suke ciki? Jiya i yau ne ki Baba ya canza halayensa?
Sai dai takan bi su da adu.a kawai, itace kadai abinda take iya yi masu a yanzu, kuma tanaiwa iyayen rikonta adu.ar gamawa da duniya lafia, ba.a wani sakata makarantar boko ba domin shekarunta sun tafi shekara goma sha takwas har ta kusa cike sha tara, aman a gida Ayya na koya mata abinda ya sawaka sai karatun islamiya da ta kara zurfafawa sosai tana kara neman ilimin adininta.
Ayya na gama daura mata kunshin ta mike tana leka windows, mamaki take irin yanda yanzu wardugu ya ajiye kafarsa a gidan, duda ta san amininsa na nan dole za yana yawan zuwa aman abin na bata mamaki, bai jima da fita ba fa aman har ya dawo, sannan yanzu basa fada da mu.azam akasin da da sai ta shiga tsakani ko ta gindaya masa doka kan Mu.azam din kafin yake barinsa ya huta, yanzu kuwa bini bini ya shigo ya haye wajen Mu.azam su yi ta hirar da ita bata san ko ta meye ba, yanzun ma tsaye suke su uku, da yar jajar nan Alhinayettt sai hira suke suna dariya,
Rufe windows din ta yi ta juya ta fice ta bar Agaishat na zaune tana jira ya bushe ta wanke kamar yanda Ayya ta fada
Bayan kunshin Agaishat ya bushe, ta mike ta saka takalminta silifas ta yi bayi,
Wanke kunshin ta yi, jan kunshi yayi jajajir, ga mamakinta ya fito sosai a fatarta har ya haska mata fatar kafar da hanayen,
Da sha.awa take kallon kunshin ya yi kyau a idannuwanta,
Ta dauki lokaci a bayi domin sai da rmta yi wanka ta fito ta je bakin madubi tana goge gaban goshinta inda ruwa ya taba kannanuwan kitson da Ayya ta dage akai mata wa.inda sai warwarewa suke dan kansu ,
Turarukanta ta zauna ta shafa na madara masu sanyin kanshi, ta shafa mai kadan a jikinta,
Kwali ta dauka tana adu.a domin har yanzu ta kasa sabawa da saka shi da dadi sai ta yi ta fama, bayan ta saka ta caje girarta, ta dauki wani jan baki mai ruwan lebe wanda Ayya ta fada mata kadan za tana shafawa a lebenta na kasa,
Hakan kuwa ta yi ta shafa kadan kafin take tsurawa madubin ido, tunda ta zo garin nan ka.ida ne a wuni sai Ayya ta tsareta yin wanka sau biyu wataran har sau uku, idan kuwa ta yi wanka dole ne ta zauna ta kula da du wata gaba ta jikinta, tun tana kallon haka a wani iri har ya kasance idan bata yin ba itama bata jin dadi, sannan ta yarda da mutun sai da gyara, wannan mugun bakin da take gani a jikinta a ruwan wanka ta ga yana sauka daga jikinta, tsabar rashin wanka na kirki ne da kuma karin bakin turkidi(tufafin buzaye), yanzu fatarta ta kasance bak’a mai haske, irin bakin nan mai kyau mai birgewa, ga gyara yana kara samu yau da kulun, har santsi santsi take ji fatar tata ta fara yi mata,
Mikewa ta yi dai ta shiga fitar da riga da siket din da Ayya ta rataya jikin abin turaren wuta tun da safe kan su zata saka,
Wani ni.imtacen kanshi suke na turaren tubawa,
A hankali ta saka slipe (pant) dinta, an ta kasa saka breziyar domin har yanzu bata iya aiki da ita ba, kai ita bata ma sonta ne ,
Kayan nan ta saka sket da riga, sun amsheta sun mata cicif a jikinta dinkin zamani ,
Tsaye take tana kallon lufayar da Ayya ta bata, ta nuna mata ta koya mata daurawa sai dai bata iya ba har yanzu (daura lufaya sai a slow),
Gashin kanta kawai ta sakawa ribom ta saka yar bakar hular da Ayya ta hada mata da kayan ta luluba Lufayar ta fice da takalman a hannayenta dan Ayya ta nada mata da kanta,
Alhinayettt karfe nawa ne zaki je wajen auren? ,
Agaishat ta tsinci muryar Wardugu da bata da siri tana tambayar Alhinayettt dake zaune tsakiyarsu Ayya kuwa na wajen table din diner tana gyara shirin da mai aikinta ta yi mata domin bai mata ba!
A hankali ta sauko, ta karaso tana hangen yanda Mu.azan ke sakar mata murmushi,
Karasawa ta yi sosai kafin take gaisar da su a jimila ta hanyar fadin” Ina kwanan ku,
Alhinayett ta amsata tana yaba kunshinta da harshen buzanci wanda Wardugu ya ji me take fada ya yatsina fuskarsa yana girgiza kai.
Mu.azam ya kai dubansa wajen agogo ya maido wajenta ya ce” Agaishana, yanzu ne safiya, duba karanto min karfe nawa ne? Na ga ko kin gane yanda na koya maki,
Ai kuwa ta juya wajen agogo ta shiga nunawa da hannayenta tana irgawa tana faman fada masa lokacin Ayya ta karaso ta kama hannunta ta ce” a bar y’a na gama shiryata, ita da bata yi safiyar zuwa wajen namiji ba ai ba lale ne ta gane safiya ce ko rana ko yama ! Ayya ta karasa tana murguda baki irin na tsofafin nan masu rigima ta kai dubanta kan Alhinayettt, wato dai da Alhinayettt ake,
Wardugu ya mike ya karasa wajen Ayya, ya kasance sun saka Ayya a tsakiya shi da Agaishat wace hannunta ke cikin na Ayya tana so ta warware mata Lufayar nan ta nada mata,