BAK’A CE Page 11 to 20

Sosai ya so rage muryarsa, sosai ya yo yaki da muryarsa ya ce” kin ce baki tsufa ba? Da yaren tubanci,
Juyowa ta yi ta murguda masa baki ta ce” eh da saurana,
Wani tsadaden murmushi ya sakar mata yana dan juya kansa, ya kamo dayan hannun nata cikin nasa ya ce” kin san du duniya ba a yi ba ba kuma za.a yi ba macen da zan so kamar mahaifiyata ko?
Ta kawar da kanta bata bashi amsa ba, ya ce” in dai kina irin abin nan sai in fara tunanin na bani Ayyana ta fara tsufa,
Hannunta ta warce ta dungure kansa kamar yanda takan yi idan ya hasalata ta ce” ni ba wani tsufa ko rashin tsufa bane, ina jin haushin irin yanda kuka dauki al.adar yahudawa kuka mayar naku, tun da safe take gidan nan
Wardugu ya ce” Mu.azam ya gayace mu baki daya mu raka shi ya ga gari,
Ayya ta yi tsam tana kallon sa, Mu.azam ya gayace ku?
Wardugu ya gyada mata kai,
Hannunta ta kai wajen wuyansa ta taba wai ta ji da zafi,
Kalau ta ji wuyansa, ta saki ta dafe habarta da mamaki, ta ce” yaushe mage da bera suka fara shan innuwa daya har shawararsu ta fara zama daya? Me ke damunku? Shirin naku kuma ya fara bani tsoro,
Wardugu ya saki hannun nata yana murmushi ya karasa ya ce” ku fice mu je ta fito idan an gama shiryata, kai yama zaka hada mana fita da karamar yarinya? Yanzu fa dole ka saka mutun ya rike bakinsa gaban yara!
Mu.azam dake biye da shi yana dariya Alhinayettt kuwa da naci ta zauna sai da Ayya ta nadawa Agaishat ta saka takalminta plat, suka kamo hanya Agaishat ta mugun yi mata kyau a idannuwanta, sai ta fito kamar wata chocolate color din balaraba, ta hade ta yi wani sihirtacen kyau
Haka suka karaso suka bude bayan suma suka shiga, ita dai Agaishat kanta a kasa, irin kalon da mu.azam ke jifanta da shi ke bata kunya, sai ta rasa me ya sa yake irin kallon nan,?
Alhinayettt ta mika hannu ta dauko wayar Wardugu ta dawo ta shiga nunawa Agaishat hotuna suna dariya,
Wardugu ya ce” ina muka nufa oga?
Mu.azam ya ce” ka kai mu Bienvenu a Wardugu place,
Wardugu ya taka wani wawan birki, ya kalo shi ya ce” wasa kake?
Mu.azam ya ce ” aa can nake son zuwa, yana mai hade rai shima ya mayar da dubansa gefen titi (BIENVENU a Wardugu place, waje ne da mahifin Wardugu ya buda da sunnansa tun suna tare suna ganewa juna kafin abinda ya hada su ya hada su su bar shi da mumunar rantsuwa a tsakani, an ce yanzu matarsa da ya aura take kula da wajen wai ita Aisata ,……mugun tsama ne tsakanin wannan family masu matukar kaunar junansu a da, kuma har yanzu da daya kwal da ya malaka dai Warsugun ne……….)…..
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣5️⃣
Wardugu da ya mayar da dubansa gefen titi ya kai hannunsa yana shafa kansa a hankali, tabas Mu.azam yana tako shi kwanakin nan, in sha Allah shi kuwa zai yi iya yinsa dan gannin ya faranta masa…
Motar ya tayar ya dauki hanya, tafiya ce suka yi mai dan tsayi kafin suke karasowa wajen,
Daga mu.azam har Alhinayettt sun yi mamakin yanda ya yarda ya zo wajen,
Mu.azam ya ji wani girman Wardugu ya karu a idannuwansa , kaunar aminin nasa ya linku a zuciyarsa, adu.a ya yi masa da fatan alkhairi …
Sai dai me, suna shiga da motar suka fara hango wasu abubuwa,
Yan mata ne da muguwar shiga, shiga ta kananun kaya sosai, da samari suna kai kawo suna dan badalar su,
Gaba dayansu kalon wajen suke da mamaki, Wardugu ya jinjina kansa a ransa ya ayanna, *Abinda ka zabarwa kanka kennan Uban Wardugu!*
Mu.azam ya yi tsam ya ce” Wardugu , ko mu juya dai? Domin wajen shi har ya fara bashi tsoro irin yanda ake shiga ana fita ana wasu abubuwan,
Wardugu ya juyo bangarensa, ya saki dan murmushi ya ce” ai mun zo sai kun shiga,
Ya bude ya fice bayan ya dauki hularsa casquette dan baya so kowa ya gane ko waye shi,
Jiki a sanyaye suke bin bayansa har ya karbi tikect din su hudu wanda zai basu damar leka ko.ina sannan su ci abinda ransu ke so, du tiket daya jika talatin ne, a wajen ba abinda babu, a da da aka bude shi an bude shi ne dan yara da iyayensu ranar weekend kawai ake bude shi, sannan ka.ida ne sai ka zo da mahaifiyarka ko da mahaifinka zaka shiga, ba.a barin budurwa da saurayinta shiga domin wajen an kawata shi da su piscine, su kayan lilo na zamani wajen game, wajen hutawa, da wajen cin abinci,
Aman a yanzu sai ta canza zani tunda ta karbi wajen da nufin zata kula masa da shi ta canza komai banda sunnan wajen, domin dalilin sunnan da ta bari doka ke tsalake su, Wardugunma bashi da labari , a yanzu wajen ba.a barin yaron da bai kai 18 shiga ba, sai gaga gagan yan duniya, sannan ba abinda ba.a yi a ciki, kan masu bushe bushen su, sai masu aikata zina a fili (wa.iyazubillah) shi kansa mahaifin wardugun bai san takamaimain abinda ake aikatawa a wajen ba, hasalima baya zama tunda abinnan ya faru da iyalansa ya ji niger din ta fice masa a rai, dan haka yake yawonsa yana kasuwancinsa a duniya, idan ya zo niger ba dan ya jima bane, koda an kawo masa korafi bai wani dubawa dan kuwa baya so ya baiwa yan tsunguri tsoma damar kawo masa korafin gidansa,
Jikin Agaishat haka yake rawa, gannin irin abinda baba sofo ke fada mata cewar ba kyau yawo jiki a bayane haka sannan ba kyau aikata zina, Ayya ma ta yi mata fadan ko a tv ta ga sun saka mace na namiji na rungumar juna ta canza tashar ba kyau aikata zina sannan ba kyau kallon tsiraicin wani banban zunubi ne ,
Wajen cin abinci Wardugu ya zame da su, domin daga nan du wani abin hange zai hango shi.
Suna zuwa suka zauna a tsararun kujerun wajen, kamshi sai tashi yake, yayan sangartatu , yayan masu hannu da shuni, da kuma masu hannun da shuni, yayan talakawan da suka zabi rayuwar hutu da zama a inda Allah ya ajiye su, sai bushasha ake ana tafiyar da lamarin cikin tsarin yan gayu…..
Menu ne aka kawo masu aka aajiye masu, nan Wardugu da kansa ke a dan duke dan kar wani ya gane shi ya dauki menu dinya kare fuskarsa da ita,
Alhinayet da gabanta ke faduwa na yannayinsa, jikinsa ya nuna ya hau, yannayinsa ya nuna ransa a bace yake,
Ta kali Mu.azan da ya rapka tagumi bai taba Menu din ba ta kuma mayar da dubanta wajen Agaishat ta ga du a firgice take sai sada kanta take bata son kallon mutanen wajen , abin bako ne a gareta,
Hannunta ta kama ta ce” Agaishat, tashi mu je,
Ai kuwa tamkar jira take ta mike ta bi bayan Alhinayettt suka fito daga dakin cin abincin suka zauna a wata farar kujera inda suka baiwa wannan lamari baya.
A hankali yake karanta menu din, harda porc, da giya kala daban daban, sannan abinda ya fi daukan hankalinsa wani abu da aka zana fari shi kuwa aka rubuta masa kudi , shi idan dai ka dauke shi dole sai ka biya, kudi masu yawa haka,
Kiran serveuse din mai dan bingilin sket ya yi da hannunsa,
Tana zuwa tana wani irin juyi fa tafia ta karaso ,
Ta saman gilas dinsa ya kare mata kallo, kafin yake mika mata menu din ya nuna mata abinda yake so,