BAK’A CE Page 11 to 20

Kallonsa take dan gane idan har dan hannun ne? Ko kuwa? Domin sunna taka tsantsan sosai bisa umarnin hajiarsu, dan ta fada masu au kula fa, kar su yarda wani mai bakin cikinta ya yi masu rami su afka, domin abin nan hoda ce, hoda ta shaye shaye,
Jikin wardugu wando ne wanda ya dan dara gwuiwarsa, sai bakar riga wace bata da zanen komai a jikinta, sai hular baka itama wace bata nuna ko ta meye ba ya dorata saman gashin kansa wanda yake da dan tsayi kadan ba dayawa irin na samarin nan dai na zamani, yannayinsa ta karewa kallo, girkeken namiji, bai yi mata kama da police ba, in ba police ba kuwa wa zai zo masu leken asiri? A tunaninta, dan haka sai ta ce” oga, ka kawo carte din ka ko kach zaka biya?
Wardugu dake zaune a aljihunsa ba kudi, sai dai a mota, carte dinsa kuwa idan ya bada za.a iya gane ko waye shi tun kafin ta karasa wajen,
Yana tunanin mafita Mu.azam ya mita tasa carte din ta bank,
Karba ta yi ta karanta sunnan,
Kallonsa take shima, a take ta ayannawa ranta yan hannu ne, wani lokacin likitoci na zuwa siyen abinnan su dai basu san ko me suke da shi ga,
Juyawa ta yi ta tafi dan kawowa ,
Wardugu ya hade jimkaken hannunsa da wanda yake bude ya shiga murza su a tare,
Sannan yana kara bin wajen da mutanen wajen da kallo,
Table sun kai biyar da ya hango suna fan dukawa su ja wani abin da yake kyautata zaton hodar maye ne a saman plat dan karami mai ruwan zaiba mai shegen kyau kafin su dago su dora daga inda suka tsaya,
Abin mamaki harda yan mata, kananun yan mata wanda a cikinsu sai ya yi rantsuwar akoy wace bata kai 18old din ba!
Wajen a da kafin ya dawo haka yake etablissement privé, wanda etat gwomnati ta san da zamansa ta bada amanar a bude shi, bisa takardun fa aka gabatar a da an gabatar ne kan irin wancen tsarin na wajen hutun yara da iyayensu ranar da ba.a karatu, aman a yanzu ta sauya zani wanda shi dai da hannunsa bai saka hannun a bude haka da shi ba,
Kansa ya girgiza, yau ko uban wa ya daure masu zasu ci ubansu!
Dubansa ya kai waje, nan ya hangi su Alhinayet suna fan taba hira da Agaishat,
Idannuwansa ya tsaida kan Agaishat wanda bai ma san ya yi hakan ba, kallon me yake mata? Sho kansa bai sani ba ko yannayinta ne ya fi yiwa idannuwansa dadin kallo?
Yana tsaka da kallon nan nata aka gabatar masa da harakar gabansa harda abin ja,
Ajiye carte din ta yi ta juya,
Wardugu ya dago hannunsa ya shiga dubawa da kyau, lale kwarai ita ce, ta ina? Ta ya aka yi take shigowa kasar? A ina take samu? Ita ke oder ko mijinta ya canza yake samo mata? Wa yake basu? Ta wace hanya ake bi a kawo har nan? Ina polisawan dake bincike a bakin titi ba dare ba rana?, ina tsaron da yake takamar ya baza a sauran garuruwa ma bale a garin da yake ciki?, ya aka yi ya yi sake haka har wannan lamarin ya cin masa da ransa da lafiarsa?
Yana tsaka da tunanin ne sai gata ta shigo,
Mace har mace, farar buzuwa mai shegen kyau, ta sha wasu mahaukatan sket da riga kanta ko dan kwali babu, ra sha wani dogon takalmi mai tsini, tana tare da wani balarabe ya sha jalabiyarsa hannunsa rike da makulin mota ,
Wani na biye da su da jaka baka suka shige tana dan dadagawa mutanen da sukai sabo hannu,
A hankali Wardugu ya mikowa Mu.azam ky din motar da suka zo da ita,
Murya a bace ya ce” ka tashi ka dauki yarwn can ku koma gida, minti talatin na baku ku shige gida da abin hawan nan, ko ku je gidan su Alhinayet dan ya fi kusa da wajen nan, domin idan kame ya ritsa da ku sai kun kwana a cel!
Ido Mu.azan ya zaro, kame a karfe uku na yama? Gashi ranar asabar ne ranar da mutane da yawa kan fita dan shakatawa, aman me ya sa zai yi kame har cikin gari bayan a cikin nan ne ake badalar?
Yar karamar wayarsa ya dauka ya dana kira,
Daga dayab bangaren aka daga ana mai fadin’ Chef????????♂️ (Sir),
Wardugu ya ce” ina so yanzu ka yi kira wajen Gn na Gendaremeri, sannan ka hado min mahaukatana, ina son motoci masu yawa su cika gari, ina son mahaukatam su karaso nan Wardugu place, kana jina da kyau, polisai su kama du wani wanda ya yi masu shige da suspect, ba zancen takardunka ko wani abin yau kamun yannayin mutun nake so a yi! Na fitar maka da iyaye mata wa.inda suka bayar da kwakwaran hujar daga inda suke, sai wa.inda suka kai yarensu wani wajen, bayan su a kama a cike mani cel!
Da a vos ordre ya amsa yana katse kiran ya mike ya shiga aikatawa ba jira,
Mu.azam mikewa ya yi da sauri ya fice ya tisa su a gaba da adu.ar Allah ya kai su inda zasu je lafia kar abin nan ya ritsa da su , duda motar Wardugu ne, da lambar shaida shi ne, ba zai hana a bincike su ba domin matarsa ta saka ya dora dokar ko motarsa a ringa bincikawa a gari! ………
Share this
[ad_2]