BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 11 to 20

Sai da Anna ta yi kuka mai isarta, suba bata hakuri kafin take share hawayenta ta yafito Bak’a sake kukan yan uwanta da mamanta na kuka

A hankali ta taso ta nufo Anna

Tunda ta taso suka sauke idannuwansu kanta

Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayyana ” Eh lale baka ce, tana da baki sosai da kuma kazanta, a rayuwar kauye dole su tsangwameta domin gari ne mai bambace bambance

Kawar da kansa ya yi, jikinsa ya yi sanyi da lamarin uwar yarinyar, tabas akoy bamban al.amari a tatare da ita, da farko ya so ya cakula abin, ya kasance an watse su yi tafiarsu ba tare da Ayya ta kwaso masu wani jangom din ba, sai dai ina yanda matar ta yi yarensa tar tar tamkar nata, sannan ta shiga turanci tamkar yarenta shima, kuma ta furta bata san bama sunnan yaririkan da ta yi, harma ta shiga wani yannayi dan za.a takurata da tambayoyi ya saka shi yin sanyi, a hankali ya furta” sai na san su waye ku! 

Anna ta kamo hannunta ta zaunar da ita daf da daf, ta dago fuskarta, abinda bata taba yi ba irin kusancin nan da yar tata, tana so ta yi tana mugun tsoro da kunya

Murya a raunane ta ce” Agaishat, Ina son ki

Da sauri Agaishat ta kara kallonta, 

Anna ta sakar mata murmushi ta ce” sosai, ina son ki, kuma ina so ki samu canjin rayuwa, bana so ki kare a haka bana so ki kare a ciki duhun rayuwa

Gaishat ta ce” Anna, Anna

Anna ta kallota ta ce” menen Gaishat? Kar na raba ku da yar uwarku?

Na san muna cikin jimamin mutuwa, muna cikin rudu, aman ku kun fi kowa sannin rayuwar da muke , mutanen nan na tafia in dai ba da ita ba na yi imanin ba zai barta ba tunda ya saka wannan lamarin a ransa sai ya aikata

Da wa zai hadata? Ina zata fada? Mai yiwuwa idan aka tsilira da ita wani wajen koda ta so guduwa ishrwa ta kasheta a hanya, 

Agaishat ta fashe da kuka jikinta ya kwashi rawa ta ce” Anna aa, aa Anna, kar ki bada ni haka Anna, ku kadai na sani Anna, kar ki raba ni da ku, kar ki yi mini haka Anna, ki barni ina ganninki har in mutu, ki barni ina gannin baba Sofona ina kai masa ruwa yana kiya mini karatu, ni ba ruwana Aba ya yi ta dukan nawa ba komi Anna in dai ina ganninki ina gannin yan uwanna ina gannin Baba Sofo ya isheni Anna, kar ki rabani da abinda nakeda a duniya wato ku……..

To jama.a ya zama kwashe ne? …………m

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        1⃣7⃣

Anna zuciyarta ta yi mugun karyewa

Hawaye yana shatatar mata muryarta na rawa ta ce ” Agaishat, ki yi hakuri ki bi su, ba mugaye bane

Agaishat ta buda idannuwanta da kyau ta ce” kina da tabacin ba mugaye bane? Kina da tabacin su din mutanen kirki ne??

Jikin Annan ya yi sanyi ta sada kanta

Gaishat dake hawaye itama ta matso ta dafa hannun Agaishat ta ce” Agaishat….

Anna ta dago ta ce” bani da tabacin halayensu, ba zan ce su din mutanen kirki bane kuma ba zan fadi akasin hakan ba

Agaishat, ni da na haike ki, ni da na yi rainon cikinki, na haife ki , tunda kika ji na ce ki je, toh ki je din kawai….ba zaki fahimci girman maganana ba sai ranar da Allah ya nuna maki kin haihu, soyayar dake tsakanina da ke na iya cewa ki je to ki yarda da na yi imani na barwa Allah komai ne, a nan kike ko a wani wajen dama shi ya halice ki, ko wace rayuwa zaki fuskanta shi ya kadaro maki, ni ban isa na hana ko na saka ba sai dai na yi ta kai kukana wajensa ina neman jin sanyi daga wajensa

Agaishat ta rintse idannuwanta, ita bama bin nasu ba, wannan mutumen da suke tare wanda yake tsaye tunda suka zo wanda fuskarsa bata ga saki ko tausayi a tatare da ita ba, shi take tsoro, in dai mugaye ne ta san shine mai yanka mutanen domin wannan da gani shine bamban mugun

Algabiit dake daka sai sintiri yake, haka zata tafi? Ba.a bashi komai na kudin tafia da ita ba? Koda ba yarsa bace ai shi yake ciyar da ita tunda aka haifeta, ya isa a yi shawara da shi sannan a biya shi! Sai dai yana ganin yanda wardugu ya diro daga motar nan ya nufosu, tun a lokacin ya fara sakin fitsari domin shi yama yi tunanin an zo kashe shi ne, ba zai fita gaban wannan mutumin mai kwarjini ya yi wani abin ba, aman ta yarda ta bada Bak’a haka zata gane bata da wayo! 

Bak’a na ji tana ganni, tana gurzan kuka mahaifanta da rai ba babu ba, ba aure ba ba dangi ba aka fitar da ita tana waiwayen Anna da ta koma da sauri ta shige bayi ta rufe ta shiga rizgar kuka, aka shiga da ita cikin motar da bata taba gani da idannuwanta bama bale ta shiga, 

Tana ji tana ganni matar nan ta shiga ta riko hannunta tana dan murzawa Alamar rarashi

Tana kallon baba Sofo har aka sako shi motar shima kafin da kyar sai da Wardugu ya yiwa Walyn tsawa ta shiga motar wai karni take ji na bak’a, ya shiga suka tayar tana ji tana ganni aka bar anguwarsu gidansu yara sai bin bayan motar suke suna ihun murna sun ga mota manya sai daga hannu suke har sai ta bace da ganninsu aka je kofat baba sofo aka tsaya suka sauke shi

Agaishat ta kara rikicewa gannin da gaske sun bar baba Sofo wanda ya tsaya yana daga mata hannu idannuwansa sun kara kodewa alamun kuka yake na zuci sai dai ya fi farin cikin hakan da zamanta a garin

Haka suka dauki hanya ba tare da sun huta ba ko sun sha ruwan garin ba suka dibi hanyar komawa garin Agadez

Kukan take tana fadin”” Anna, Sofo, Anna, sofo

Walyn ta ja tsaki ta ciro ecouteurs dinta ta saka a kune, Wardugu dake gaba ya rufe idannuwansa a tunaninsa zata gaji ta yi shiru ne aman ina sai kara boda Agaishat ke yi Ayya na tausarta tana bata hakuri da tubanci bata san ta dan iya hausa ba ita kuwa bata iya buzanci ba

Juyowa ya yi, da yaren buzanci ya ce” Ke ki rufe mini baki a nan tun kafin na saukeki na yi maki dukan tsiya, shiiit bakin nan naki ya mini shiru ko na ciro maki shi a hannunki

Wa ya ga hadiya, Agaishat hadiye kukanta ta yi, tana zaro ido tana kallonsu daya bayan daya tana sauke ajiyar zuciya, 

Ayya tana magana tana yi mata nuni da ta yi hakuri ta yi shiru ta daina kuka

A hankali Agaishat ke ajiyar zuciya sannan ta damke hannun Ayya wace ke rike da nata itama, tana kallonta, a nan ita kadai ta dan hangi laushi a tare da ita 

Tafiya suke suna ratsa sahara har suka baro suka debi titi,

Agasihat ko dis ba baci a tare da ita sai kallon titin da take , tsoro fal ranta haka idannuwanta suka nuna, mamaki take dama Shukoki na gudu? Domin yanda motar ke gudu sai take gannin suma shukokin gudu suke tun karfinsu

Walyn dake takure tana sakin numfashi sama sama ta shiga yinkurin amai tana kakari

Ayya ta kai dubanta wajenta da mamaki, lale walyn bata da mutunci, yanzu du irin yanda ta fafeshe su da turare tana jan tsaki kuma ta kai amai zata yi dan warin Yarinyar da suka dauko

Ta girgiza kai kawai ko ci kanki bata ce da ita ba

Wardugu dake zaune a ransa ya ayanna Walyn bata son zaman lafia, in dai Ayya ce ta isheki ba abinda ya dame ni! 

Ba su su karasa cikin gari ba sai can wajen karfe goma na dare

Abinka da agadez ma ba wani banban gari sosai bane sai ya kasance shiru garin sai yan mata da samari wasu na tafe a kafa wasu a mota wasu a mashin suna dan yawansu na yau da kulun wasu sun nufi gidan rawa, wasu sun tafi gidan cin abinci, wasu suna yawatawa dan shan iskan gari kuma suna hirarsu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button