BAK’A CE Page 11 to 20

Ta koma ta darwaye soson ta kara yin yanda ta yi , ta shiga saba sabulun a tufkeken gashinta na buzuwar usul ruwan nan na dareaye mata,
Abinka da tufkeken gashi wani wajen ya wanku sama sama aman cikin kam da datinsa daskare, haka Agaishat ta yi ta wanka tana sakewa tana jin kanta wani sakayau tana kara balbaluwa a cikin ruwan nan tana jin dadinsa abinka da ba sabanba ta wanke tafin kafafuwanta da abinda Ayya ta nuna mata nanma ta ga dati sai fita yake , har yatsarta ta saka ta debo datin tana kallo da gaske dati ne ta wanke da sabulu tana daga kanta sama ruwan na shiga idannuwanta yana kara ratsa gashinta da jelar ta sako tana yawo du idan ta juya kan
Fitowa ta yi ta dauki kayanta wa.inda sai a lokacin ta ji suna wani irin bugawa da ta rabu da datin jikinta, har ta shiga tunanin ko ta wanke? Sai wani abin yace mata idan kika wanke ki saka me kuma? Mayar da kayan ta yi ta fito ba tare da ta kashe panpan ba domin bata iya ba
Ayya dake zaune tana jiranta domin Wardugu ya tafi abinsa , ta mike tana fadin” eyah Agaishat ki cire kayan nan mana
Agaishat ta yi kasakai tana kallonta
Ayya ta dafe kai ta ce” wani yare kika iya
Agaishat kin iya frencais? Angalais? Ko hausa?
Agaishat dake kallon Ayya ta ce” Ayya, hausa kadan kadan
Ayya cikin itama dan yaren hausar nata ta ce” ouf , mun samu na gaisuwa, ki fida kayan nan ki canza wasu kin ji
Agaishat ta gyada kanta tana kallon wa.inda Ayya ta nuna mata, sannan ta juyo dan gannin a gaban Ayyan zata saka sai ta ga Ayya ta nufi kofa abinta
Ajiyar zuciya ta sauke ta tube kayan ta dauko wa.inda aka ajiye mata
Tsayawa ta yi tana kallon doguwar rigar abaya baka wace bata san ina ne gabanta ko bayanta ba sai dogon wando wanda ta daga tana ta jujuyawa irin na maza ta ayanna a ranta sai dai ba irin na mazan garinmu ba domin wandunnansu tamkar buhu……..
Da daurin kirjinta tana tsayen nan Ayya ta dawo ta ga bata saka kayan ba
Nufota ta yi ta ce” aa ya baki saka ba?
Agaishat ta mika mata ta ce” Anna ban iya ba
Ayya ta yi murmushi ta shiga nuna mata ta juya ta saka wandon da kyar domin ya yiwa jikinta kadan duda fadinsa da yanda kuma yake jayuwa,
Ta dora rigar ta kule yar igiyar dake ciki
Ayya ta juyo tana kallonta, ba laifi kayan sun amsheta sai dai sam wankan nan bai yiwa ayya ba , gani take bata wanku ba da saura duda yanda du wani jirwayi na turkudi da fari fat din nan ya fita
Mai ta miko mata ta shafa , ta miko mata turare ta tayata shafawa
Agaishat bata san tana sakin murmushi ba sai da ta waiga wajen madubi
A hankali ta taka ta karasa, hannunta ta mika ta taba madubin tana kallon kanta, a hankali ta juyo wajen Ayya ta ce” na gode Anna
Ayya ta karaso da dan kalabin rigar ta kama kanta da bai karasa bushewa ba ta saka mata ribom ta daure mata sannan ta nada mata dan kwalin ya zagaye fuskarta
Kwali ta dauko ta nuna mata da ta shafa , Agaishat ta ce bata iya ba , hakan ya sa Ayya ta saka mata idonta ya fara ruwa ruwa abin rashin sabo Ayya tace ta jure karta murje ta kuwa juren
Abin maskara ta dauka ta fitar da shi ta saka wani mouchoir (kyale) ta goge bakin jikin tas tas, ta dauki jagira mai ruwan baka ta gogoga a jikin abin ta samu ta caje girar bak’a, girar ta kwonta tsaf a inda ya kamata ba kamar da farko yanda take wawatse ba
Ayya ta juyata wajen madubin ta ce” Agaishat, Tsafta, kwaliya, ya zama wajibi ga macen da ta san ciwon kanta, ki rike wanka , ki kasance mai tsafta kin ji??
Kai Agaishat ta daga tana kallon kanta da mamaki, tamkar ba ita ba, ta sawaya hancinta ya wani tafi zuwat, wai a nan Ayya bata gamsu da wankan ba jira take dai su karasa Niamey ta dauki lamarin a hannunta……….
Karfe sha biyu da minti arbadin suka fito daga masarauta suka nufi aeroport, ita dai Ayya bata san yanda wardugu ya yi ya samawa Agaishat waje ba bata tambaye shi ba
Sauran minti biyar suka karasa, suna zaune Ayya na kallonsa yanda ransa ke bace, bata ga Walyn ba bata tambayi inda take ba domin ba wani shiga lamarin juna suke ba, bata san zuwanta ba sai da ta ganta daga ina kwana wani abin bai kara shiga tsakaninsu ba sannan dan yanzu bata ganta ba itama ba zata wani tambayi inda take ba , Allah ya basu zaman lafia ita da mijinta ba abinda ya shafeta da zamansu haka kuma ba zata shiga dan wani gyara ba!
Ba.a jima ba suka mike domin an fara kiraye kirayen sunnaye,
Ita dai agaishat tunda aka haliceta bata taba gannin jirgin bama bale wai har ta shigeshi
Ta dai bi bayan Ayya da ta kama hannunta ta shiga nuna mata yanda zata taka matatakalar ta hau suka hau tare tana kara rike Ayya da kyau dan kar ta fadi har suka shiga
Kallon tsarin cikin jirgin take a ranta ta ayanna ba irin na mota ba ,
Nan Ayya ta tsaya sai da Wardugu ya shige kusan madubin domin sam ya hannata zama a nan in dai tafiar jirgi zata yi, ita dai sai dai ta yi murmushi kawai irin yanda yaron nata ke sonta ke kokarin kareta har mamakinsa take ,
Yana shiga sai ta saka Agaishat ta shige tsakiya , shi kam bai yi magana ba domin ransa a kololuwar bace yake, wai Walyn ta bi jirgin damagaran gobe ta bi na niamey ta karasa, shi zata nunawa zuciya ko? Han……
Ayya ma ta zauna ta ja ceinture ta sakawa Agaishat sannan itama ta saka bayan ta kashe babar wayarta ta android
Ba.a jima ba aka shiga fadin a daura ceinture a kashe waya da yarurukanmu na niger da kuma french da inglish duka , bayan an gama jirgin ya fara tafiya wace suuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu ne saman doguwar hanyarsa har ya zo wajen hatsarin wato tashi da saukar jirgi ba,
Cikin adu.a a bakin Ayya
Nan fa ake yinta domin abin tashin jirgin nan, kun san ko wanda ya saba sai ya ji cikinsa ya yi kasa bale wanda shigarsa ce ta fari kuma sha.af Ayya ta sha.afa da fada mata abinda kan iya zuwa sannan tace da ita tashi zasu yi sama, ita kuwa a kauye baba sofo ya taba gaya mata akoy harda wani abin mai tashi sama a birni sunnansa jirgi ,
Ai gaba daya ta shiga jijiga ta damki cinyar wardugu dake gefenta na dama ta damko ta ayya ta bude baki ta……..
???????????????? ku taro su kauyawa a birni????????????????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣0️⃣
Ido Wardugu ya zaro, ya kai kallonsa kan hannunta wanda ke dauke da dogayen akaifu domin ba wani cire su take son yi ba sai baba sofo ya sakata gaba take yanke akaifunta sai tace nai ai susa take da su,
Wardugu bai gama tantance meye haka ba ya ji wani irin ihun da ya yi barazanar tarwatsa masa dodon kunne,
A tare suka juyo wajenta shi da Ayya ……
Ayya cikin yannayin tashin hankali da yaren tubanci ta ce ” Wardugu Wardugu tsoro ne take ji na manta ban fada mata ba, kuma ban riketa ba , mai yiwuwa bata taba ganninsa bama bale ta shiga;
Bak’a da jikinta ke bari gaba daya ta kwalallo idannuwanta, daurin dan kwalin nata ya kunce , hawaye tuni sun kama zarya, ihu kawai take tana ambatan innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!