BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 11 to 20

Mutanen dake kusa da su harma wa.inda ke dan nesa da su ne hankalinsu ya fara tashi du aka fara jiyowa wajen su Ayyar da ayyar tambaya da alamun tsoron a fuskokin su….

Daga can kofar masu kula da passenger wata mata mai kulawa da bukatun passenger ta fito da sauri da dan sket dinta, ta sha kwaliya, tana dan sauri tana fadin kowa ya zauna kowa ya kwontar da hankalinsa ba komai bane , sannan tana nufo wajen su wardugu;

Hannunsa ya daga na dama ya shafa sumarsa, a kasan zuciyarsa ayannawa yake wannan wani irin tashin hankali ne? Shi Wardugu da girmansa da irin yanda duniya ta san shi, shine za.a yiwa taro da yar kauyen nan! Merde! merde! merde! 

Juyowa ya yi wajenta, hannunsa na hagu dake kusa da ita ya saka ya janyota jikinsa, ya sakata a jikinsa da hannun nasa ya karkata fuskarta gefen hannunsa na dama , ya saka hannun nasa na damar ya yiwa bakin nata mai ihu wata damka …ai kuwa shiru kake ji ba ihu ba di kira da salamcewa sai dan mutsu mutsu wanda shima da ya kara riketa sai laf tamkar ta lafe ne a jikinsa. (WARDUGU kan keta) 

Tambaya matar nan take lafia ? Me ke faruwa??

Wardugu gannin bakuwa ce yar amerika, sai ya ciro carte dinsa da hannun hagu dinsa ya nuna mata mai shaidar ko shi waye, sannan da lebensa ya yi mata nuni da mahaukaciya ce kar ta wani damu……..????

Ai kuwa ta shiga bada hakuri da iya yi, ta juya ta koma.

 Ayya sai faman ya cika yarinya take aman ya tsareta da ido ya ki yin maganama;

Nauyin da ya ji ta yi ne ya saka shi sasauta rikon, ba.a wani dauki lokaci ba Agaishat ta yi baci sai kace wata baby, bacin tsoro da tashin hankali, bacin wahala, gashi daman daren jiya ba wani bacin kirki ta yi ba dan tsoro da zulumi, sai ajiyar zuciya take saukewa du ta goge hawayenta a jikin rigar wardugu.

A hankali wardugu yake kokarin kwontar da ita jikin kujerarta, Ayya ta zabga masa harara ta jinginar da Agaishat a jikinta tana kara tabata dan tabatarwa in ba suma ta yi ba.

Murmushi Wardugu ya yiwa mahaifiyarsa na alamun bada hakuri kafin ya jingina yana duba agogon hannunsa domin tafiar idan Allah ya yarda ba wata mai tsayi bace a jirgi tsakannin Agadez da Niamey.

Allah ya sauke su lafia, Wardugu da kansa ya tuka motar da ya je da ita ya ajiye aeroport ,

Bai zame ko.ina ba sai gidan Ayya.

Suna zuwa Ayya ta yi hamdallah ta kamo Hannun Bak’a wace ke kallo da baki da hanci da ido gaba daya

Fitar da ita ta yi ta ce” mu tafi yar gidan Ayyarta

A hankali ta fito itama kamar yanda Ayya ta koya mata ta bi bayan Ayya tana waiwayen Wardugu da ya fitar da kafarsa guda waje yana ta faman yamutsa gashin kansa, wayarsa ya ciro yar karama ya dannawa abokinsa kira wato docter DOCTER MU.AZAM

Yana dagawa ya ce” Ranka ya dade oga *Wardugu Marahut* 

Wardugu ya ja tsaki ya ce” Mu.azam ni za ka yiwa rashin mutunci? Yaushe ka fara karya?

Mu.azam ya yi shiru, ……tamkarma ya kashe kiran.

Wardugu ya duba ya ga kiran na tafia, ya kara karawa a kunnensa ya ce” kai! 

Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya ya ce” abokina, ka yi hakuri ka ji? Jikina ne ya tashi aman yau nake fita asibiti in sha Allah da na huta sai na kamo hanya.

Wardugu da ya gama jin abinda ya fada, cikin mutuwar jikin da bai san ko na meye ba ya ce” me ke damun ka ne harda kwonciya hopital? (HOSPITAL) 

Mu.azam dake kallon karin ruwan da aka saka masa ya lumshe idannuwansa, jiki a mace ya ce” idan Allah ya kawo ni zan fada maka koma menene,

Wardugu ya sauke ajiyar zuciya, bai bashi amsa ba ya katse kiran ya rufo motar ya tayar dan ya samu ya karasa gidansa ya huta 

……………………..

                        TIMIYA

Rana ce, karfe biyu na rana ne, aman da dan lulumi kamar yanda garin ya saba, 

A kasan innuwa suke zaune su uku suna yamutsa garin kwakwi da mai da yaji da manda (gishiri), 

Fatimata ce mai kwadawar, Ayya na yiwa maryama susa a kanta

Mariama ce ta dago ta ce” Fatimata kar ki hade yajin nan duka ki ware min a robar nan kuma kar ki zuba mai iya shi din sai mandan ya isa kin ji?

Fatimata ta amsata da kai, Ayya dake mata susa kuwa a ranta take tambayar kanta Mariama ko ta daina cin yaji ne? Kai ina Mariama da yaji ai akoy amana.

Fatimata na gama warewa, Maryama ta mike ta dauki dankwalinta ta daura, ta dauki robar ta nufi wajen tulun Anna kwaya biyu dake cike da ruwa ta dauki guda ta dora saman kanta ta kama hanyar fita,

Kallonta suke da mamaki, Fatimata ta ce” Mariama ina zaki tafi kuma? Ki bari mu ci mana.

Mariama ta juyo ta ce” ki ware min nawa, zan je wajen Sofon nan na Agaishat na dubo shi ne,

Murmushin da Anna ta jima bata yi ba ta saki, sanyi ta ji a ranta daman tana ta tunaninsa halin da yake ciki mutumen kirki

Mariama oga kennan, Mariama ba daukan raina,

Bata zame ko.ina ba sai majalisar mahaifinta,

Tana zuwa ta mika masa hannu ba alamar wasa ta ce” kudi nake so Aba,

Bakinsa ya yatsina, Mariama fa ta fara isarsa da wannan ya bata ya batan, tunda ya karbi kudin aurenta take tatikarsa, idan ya nuna ba zai bada ba kuwa a ji su, 

Rai bace ya saka hannunsa a aljihun rigarsa ya ciro dala dari ya mika mata a ransa yana adu.ar Allah ya sa ta karba kar ta ce ta yi mata kadan! 

Karba ta yi ta maida tulunta da robar saman kanta ta juya ta nufi gidan mai goro….

Nan ta sayi goro har na dala Ashirin, ta sayi man zafi na ciwon jiki ta sayi yar tsintsiya, dauka ta yi ta nufi runfar baba Sofo.

Tana zuwa ta yi salama har sau biyu kafin take jiyo muryarsa can kasa yana amsawa;

Shiga ta yi tana wara idannuwanta dan ganni da kyau domin ta biyo rana idannuwan nata duhu suke ganni.

Yana kwonce fuskarsa na dubinta, ya takure ya kara yamutsewa da cazbaharsa yana ja kuwa,

Bata yi masa magana ba ta karasa inda ta ga tulun ta jawo ta fitar da shi ta wanke shi tas ta juye ruwan nan na cikin tulun Anna, 

Ledojin da suka shihigo da kararuwa ta tatare ta fitar kafin take juyowa ta shiga share bukar inda baba sofo ya samu ya zauna yana binta da kallo da mamaki a kasan zuciyarsa; wannan ai yayar Agaishat ce, mai fadan nan, ikon Allah kawai yake fadi a kasan zuciyarsa.

Tana gamawa ta dauko robar abincin ta debo ruwa ta dawo ta darwaye hannunta ta zauna, ruwan nan ta kara yayafawa garin dan ya kara yin laushi sosai, tana yi bata ko kallonsa dan ta yi imanin ya tsareta da ido ne,…………

Sai da ta kai bakinta ta ji idan mutun yace tsotsama zai yi tsaf zai tsotse abinsa ta dago da dubanta a hankali ta kai wajen baba Sofon dake kallonta ta ce”””

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        2️⃣1⃣

Ta ce” ga abinci, ina magurjinka? 

Hannunsa dake dan rawa ya saka ya fitar da magurjin ya mika mata yana kallonta dai,

Mikewa ta yi ta wanko magurjin da goron, sannan ta dauko wata yar roba mai marfi da ta amso wajen mai siyar da goro ta kara darwayeta itama, ta dawo ta zauna ta saka yar farar leda a kasan abin gurzawar ta shiga gurza goron nan manya har uku; 

Robar ya saka hannunsa ya janyo, bismillah ya yi har zai fara ci maganar Bak’a ta dawo masa inda take cewa < ka ringa wanke hannunka Sofo, ka ga jiki na iya daukan dati mai yawa banda ciki ka ji sofona? >

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button