BAK’A CE Page 11 to 20

Yauma sun tashi da niyar yin gyaran jikin ne, Ayya ta dadaure mata gashinta da abin nan na saloon wanda idan an wanke kai ake sakawa a dadaure gashi da shi dan ya nanade ya bushe, ta kwaba abin gyaran jikin nan ta samu ta shafa mata ta yi mata hayakin mai mugun zafi wanda fuska kawai ake fitarwa, tana gamawa ta sakata ta yi wanka ta shafa mata na madarar nan suka zauna a fali sunna kallo aman ta hanata magana dan kar na fuskar ya saka fuskar ta yakune……..
Mai gadi ne ya fara shigowa da jaka, Wardugu na biye da shi sai Mu.azam wa.inda shigowarsu ne ya ankarar da Ayya ta warci hijab din Agaishat ta ……
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣2️⃣
Da sauri Ayya ta samu ta rufa mata hijab din inda Bak’a ta yi mutuwar zaune a ranta tana ayana Ayya wayo daman sai da na fada maki Ayya ………..
Karasowa suka yi, Mu.azan na kallon inda aka rufe da hijab yana son sannin ko waye,
Wardugu kuwa kallo daya ya yiwa wajen ya kawar da kai a ransa fadi yake” me Ayya ke son yiwa fatar nan da ta rine?
Da murna Ayya take kwalawa mai aikinta kira da ta zo ta dauke akwatin Mu.azam sannan ta kawo masa tarba,
Ayya ta tarbo shi tana murna ta kamo shi ta zaunar da shi sai murmushi take tana kallonsa ta ce” yarona, yaushe gamo?
Mu.azam dake jin wata nutsuwa na saukar masa ya dube duba irin na mahaifiya, a hankali ya duka kasa ya ce” Ayyana ina yini
Ayya ta kuma kamo shi ta tayar da shi tana kallonsa, yannayinta ya fara canzawa ta kai hannunta wajen wuyansa ta ce” me ke damunka? Ya haka ka rame har haka? Ko dai ka je ka sakawa kanka ayuka ba hutu ne??
Dariya ya saki yana kallon Ayya , kafin yake maida dubansa wajen Wardugu ya ce” freind Ayyana har yanzu akoy yannayin nan?
Wardugu ya yi dan murmushi yana kallon su,
Ayya ta yatsina fuska ta ce” ba wani nan, yanzu tashi ka je ka yi wanka ka fito zan fara yi maka dura ne tunda abin haka ne!
Yana dariya ya mike ya kalli Wardugu ya ce” mu je ko?
Wardugu ya gala masa harara ya ce” a matsayin matarka ko dan jagorarka?
Mu.azam ya yi murmusho yana ji a cikin ransa ya yi missing din abokinsa da mahaifiyar abokin nasa,
Juyawa ya yi ya nufi dakin da ake sauke shi wanda yake a matsayin nasa,
Ayya ce ta dubi wardugu, da idannuwanta ta yi masa nuni da ya tashi mana shima baya gannin mutun?
Wardugu ya daga kafadu ya ki tashin yama mayar da dubansa wajen tv inda ya dauki commande ya canza tasha ya kai Canal plus sport ya shiga kallon ball.
Ji take ta fara gumi , ga kuma ta kage a yannayin zaman nata, ba.a jima ba Mu.azam ya dawo daga wankan da ya tafi ya zu suka kara kasancewa mutun biyu maza kennan,
Ayya ta tashi da yannayin jin haushi ta dunguri kan Wardugu ta ce” ta yi maka kyau!
Wajen Agaishat ta karaso ta kamata ta mike kafarta ta yi mata tsami sosai, ta samu ta saka mata hijab din ta ce” je ki yi wanka Agaishat ki sauko mu ci abinci .
Da toh ta amsa ta bi ta bayan kujerun ba tare da ta gaisar da su Wardugu ba,
Mu.azam da ayar tambaya ya kallo Ayya, bai yi nauyin baki ba ya ce” Ayya ina kika samo wannan?
Ayya ta karasa kusa da su sosai ta zuba jus ta mika masa shima kamar yanda ta mikawa Wardugu ta ce” Me ke damunka tukunnan yarona??
Mu.azam ya shiga dan sosa bayan keyarsa, ya kallo wajen Wardugu, ya kuma kalli Ayya.
Haka kawai wardugu ya ji gabansa ya fadi, shima kure shi da kallon yake kafin ya ajiye yar wayar dake hannun nasa ya zuba masa ido,
Murmushin dai ya kara yi masu, ya ce” na yi rashin lafia ne Ayya, kuma yanzu alhamdulilah na samu sauki,
Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce” na tsorata da yannayinka, ka wani rame, ba komai haka ne idan jiki ya tabu sai a hankali aman yanzu ka zo kennan sai na ga yarona ya koma yanda yake da koma ya fi haka kafin ka bar gidannan,
Wardugu dake kallonsa ya shafa kansa shima kwata kwata bai yarda da maganar Mu.azam ba! Kai haba a irin yanda suka san juna Mu.azam ba zai layance masa ba
Mikewa ya yi ya nufi kofa da wayarsa a hannu inda suka bi shi da kallo,
Mu.azam ya ce” Ayya ya tafi fa kennan??
Ayya ta daga kafadunta ta dan yatsina fuska ta ce ” ya gaishe su!
Mu.azam ya yi dariya yana kallonta, a ransa kuwa dadi yake ji yannayin, kai yana jin dadin zama da su, Wardugu rikitace, mahaifiyarsa ta iya zama da shi, ta kai ta kawo ne idan tama da bukatar ganninsa a wayarsa ya yi mata activen localization, du inda yake idan ta shiga nema za.a nuna mata kawai sai dai ya ganta kuma sam baya gigin kashewa doka ce!
Suna tsaka da tataunawa mai aikin Ayya ta shinfida ledar cin abinci ta kawo abincin ta ajiye, ta kawo kayan zubawa da na sha, ta kawo su jus na gida da Ayya ke yin abinta da kanta ta saka a frij du ta ajiye, Ayya ta umarci Mu.azam da ya sauko bara ta dubo yarta…..
Wardugu ya dawo, bayansa *ALHINAYET* kawarsa ce ke biye da shi,
Salama ta yi ta shigo dakin inda Ayya ta tsaya ta saki baki tana kallon Wardugu da Alhinayet din,
Alhinayett na zuwa ta shiga gaisar da Ayya cikin yannayin ladabi da mutunta mutun,
Ayya ta dan kebe baki, ta amsata ta juya dan dubo Bak’a
Mu.azam dake zaune ta juyo ta dafe habarta ta ce” su likitoci ne a garin namu???
Mu.azam ya sakar mata murmushi ya ce” lauya, lauya, lauya mai kunce mai laifi , zamani lauya iko, lauya mai saka kato ya duka,
Kai ta dafe ta ce” wace ni, rufani ka sayani, ai ba dan an san ni aminiyar *Aboki* bace da an fige ni a Niger!
Mu.azam ya ce” kai ai rigimama ta san waye *Oga*
Wardugu ya girgiza kai yana zama ya ce” *ALHIN* ki zauna mu hau wannan abubuwan kafin ku ci gaba da kirar da kuka koya!
Alhinayettt ta je kusa da Wardugu ta zauna tana fadin” General ka duba lamarin nan je ten conjure…………….(plz)
Wardugu ya kaleta zai yi magana sai ga Ayya ta dawo da Agaishat,
Doguwar riga simple irin ta zaman gida ce Ayya ta bata, bayan ta saka ayya ta bata Dan kwalin rigar nufin ta yane kanta sai dai suka hau rigima kan aa dan Allah ta bata hijab,
Gannin sai su bata lokaci ne ya saka Ayyar bata hijab ta zumbula suka sauko,
Sai a lokacin Agaishat ta duka ta ce” ina yinin ku,
Alhinayettt da Mu.azam ne suka amsa inda Wardugu ya kebe bakinsa bai wani amsa ba aman yana yi mata kallon tsaf, a ransa yake ayyana black, but ko a baki *BUZU MAI KYAU NE* ???????????????????????????????????????????????????????????????????? na fada a zo a dake ni????????????????????????????????????????????????????
May be 23……zuwa dare in sha allah, idan comment ya birge ni????????????????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣3️⃣
Waje Ayya ta samu ta zauna , nan Agaishat ta je kusa da ita sosai itama ta zauna ya kasance an saka baban plateau din a tsakiya,