BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 11 to 20

Ayya ce ta bude inda abincin yake, tuwon tsaki ne da miyar kubewa wace aka yita da naman shanu ta sha dadawa da kayan miya ????..ga kuma man shanu na kirki a gefe, 

Sai su fruits da aka hi masu yanka mai kyau aka sasaka cikin plat plat, sai jus da ruwa,

A hankali Ayya ta dauko abincin, Agaishat ta dauko abin zubawa, 

Cikin wannan banban plateau din Ayya ta zuba abincin ta daidaita miyar, ka.ida ne in dai ka zo gidan Ayya daidai cin abinci bata raba assiete, sai dai a hadu a ci a abu guda …….

Bayan ta zuba ta kare Agaishat ta kawo abin wanoe hannu da kuma cokula a wata yar roba,

Gaba dayansu cokulan suka dauka banda Agaishat da Ayya , hannayensu suka wanke ….

Ayya ce ta fara saka hannunta, sai Wardugu, sai Mu.azam, sai Alhinayettt, sannan Agaishat dake karamar cikinsu, hakane gidan Ayya baba ke fara saka hannu cikin kwanon cin abinci sannan yaro ke rike kwanon dan kar ya ringa yawo, ba.a magana idan ana cin abinci, ba.a dane danen waya, ba.a wani kale kale sai an gama, sannan bata yarda ana tsaka da cin abinci ana shan ruwa ko jus, sai an gama ake sha, sannan ana cin abinci daidai ne ba.a matsawa ciki a yi mugun koshi, lamarin gidan Ayya sai yayanta (????),

Abincin nan ake ci cikin nutsuwa, Alhinayettt ta kure Agaishat da kallo, sam batai mata kama da tubawa ba, sannan ba bahausa bace ko daya duda hijabin dake kanta gaban goshinta lufluf yake kwonce da gashi, girartama wani irin gazar gazar da ita, du bakinta lebenta haske ne da shi tas tas, ga girar ido ga manyan idannu, wannan cikin biyu daya ce ko bakar balaraba ko bakar buzuwa! 

Alhinayettt dai ba wani yawan zuwa gidan Ayya ba take ba, sukan hadunsu ne da wardugu a wani wajen, yanzuma zuwa ta yi da rigimarsu ta kansu wace ta zo su yi kan irin yanda ake cece ku ce a gari na matarsama idan ta cika dare kwanan cel take bare wani banza!

Alhinayettt kwata kwata ta manta zancen ba.a magana idan ana cin abinci gidan Ayya dan haka ta kali Agaishat da kyau, haka kawai ta yi niyar yi mata magana da buzanci dan ta gaskata zatonta, 

*ABZIN?* , ta fada tana kallon agaishat,

Agaishat da ta hadiye abinci ta kaleta itama, itama ta so ta ayanna hakan cewa wannan buzuwa ce, gannin yannayinta sai dai bata fadi ba dan ba wajen fadin bane, 

Ai kuwa Agaishat ta washe baki itama da yaren buzancin ta maida mata cewa” eh , ke fa??

Alhinayettt zata maida mata maganar Wardugu ya tsimki hannunta na dama dake kusa da shi, sannan ya zabgawa Agaishat wata muguwar harara wace ta sakata sada kanta hannunta na rawa rawa, 

Ayya yatsina fuska ta yi bata yi magana ba, 

Sai da aka gama mai aiki ta shiga kwashewa, Agaishat na tayata kaiwa komai wajensa ta dawo ta zauna kasa kusa da kafar Ayya,

Wardugu ne ke kallon wayar Alhinayet tana nuna masa hotunnan birthday dinta da ta yi baya nan yana dan murmushi kasa kasa ya ce” Alhinayettt , ina tunanin kin girma ashe dai na daina tunanin nan?

Alhinayettt ta yi dariya ta dora hannunta saman nasa ta ce” na baka ka sha? (Irin su taba zata bashi wani labarin) 

Ai kuwa Wardugu ya dan cafke hannunta yana sauraronta, inda ya bata hankalinsa suna ta hirar su,

Ayya ce ta dan ja tsaki, ta girgiza kai tana kallon Mu.azam ta ce” kana ji? Zamani ya zo mana da abubuwan mamaki, sai ka ga mace na tafawa da namiji, tana raba jikinta da nasa wai a zuwan mutunci kawarsa, !  

Mu.azam ya zaro ido yana kallon Ayya, a fili kuwa ya furta” Lah, yana dafe bakinsa,

Wardugu da ya gama jin komai ya saki murmushi yana kallon Ayya, ya ce” Ayya, qna abota mace da namiji, abota sak ba wani soyaya ba kuwa,

Ayya ta juyo bangaren su a takaice , daman jira take wani abin ya hada su ta ce” wardugu ba abota ba dai yayan awaki! Nace yayan awaki, Ke yanzu Alhinayettt kike ko wa? Aman ke marainiya ce ko? Ina nufin mahaifiyarki ta rasu?

Alhinayettt dake kallon Ayya a dan tsorace ta ce” Aa Ayya,

Ayya ta dafe habarta ta ce” Toh abin mamaki, aman ita baku rainata kamar yanda kuka rainani ba ko? Ina nufin Wardugu baya zuwa gidan ku a matsayin aboki sai saurayi?

A tare suka kalli juna Alhinayettt da Wardugu, suka maida dubansu wajen Ayya, 

Ayya ta ce” to in ba haka ba, ya za.a yi ni ina mahaifiyarki , kato ya ringa zuwa wajenki a matsayin aboki kuma na zuba ido yarinya kin kai kin kawo min a gida? 

Wardugu ya shiga gyada kai yana kallon mahaifiyarsa, ta jima tana son aikata wannan aika aikar wa zumuncinsa da Alhinayettt, yau dai ta yi hankalinta sai ya kwonta kuma ko? 

Ayya kamar zugata ake sai magangannunta take son ranta karshe ta ce” to ni ba tsohuwar banza bace, in sonta kake ka fito a mutun ka fada ku daina boyewa Allah kadai ya san tsakanin ku! Dan haka tun wuri a fasa daukana a wata marar ilimi ana ce min wai kawa! Aa abokiyar tagwaitakarka ce Wardugu!  

Wardugu kallon Ayya kawai yake, inda Alhinayettt ta dan sada kanta kasa, a ranta ayannawa take ita bata ga laifin zumunci da suke da Wardugu ba, walahi da soyaya suke da ba haka ba, kwata kwata ba wani zance wai shi soyaya tsakaninsu, haka kawai Allah ya hada jininsu suke mutunci, Wardugu bashi da shamaki a gidan su, hakama saurayinta wanda zasu yi aure suna mutunci da Wardugu, aman haka ne itama kakarta ta sakawa zumuncinsu ido har sun mayar da ita tamkar mahaukaciya domin idan sun ga zata fice sai su shiga magana kasa kasa da yaren french ai kuwa ta kama zage zage tana fadin ita za.a munafinta? Toh gashi itama maman Wardugu kallon masu soyaya take masu bayan ita koda bindiga ba zata iya soyaya da wardugu ba domin ta san waye shi, Wardugu dan yana son ki ba zai hana ya yi maki dukan mutuwa ba, dan yana son ki baki fi hukunci a wajensa a gaban koma waye ba, hum soyayama da wardugu ai tashin hankali ce, ita mai ya kaita? Ta fi son namiji marar rigima mai bata damar ta yi rayuwarta cikin aminci……..

Wardugu dake kallon Ayya tar, ya maida dubansa wajen Mu.azam ya ga sai gumtse dariya yake, 

Kansa ya girgiza ya maido dubansa wajen Ayya, da hannunsa na dama ya daga ya sara mata, sannan ya yi mata nuni da ta ci wasanfa , ta more abinta, 

Hannunsa na hagu ya mikawa Alhinayettt ta mike itama ya ja hannunta tana waiwaye tana so ta yi hira da agaishat aman ya jata kiiii sukai waje

Kusan motarta suka tsaya, 

Alhinayettt bata bi ta kan fadan Ayya ba, bata nuna damuwarta ko a fuska ba, ta ce” Wardugu, rigingimunka sun isheni haka, ya isheka malan! 

Wardugu ya shiga gyada kai yana kallonta bai bata amsa ba, 

Ta ci gaba da maga domin ta san ba amsar zai bata ba, ta ce” ta ya zaka saka Walyn kwana a cel? Wardugu ina jin zafi idan na ji ana fadin baka da sasauci, baka wasa, baka sulhu, Wardugu matarka ce fa? Ya kake so mutane su fasaraka??

Wardugu ya tsura mata ido kawai, 

Ta ci gaba murya a sanyaye” ka daina Wardugu, ina so idan na zo waje na tarda ana fadin alkhairi a kanka, ina so idan ana maganarka ta kasance ana yabonka Wardugu, ka ringa sasauci freind, 

Wardugu ya yi mata dan murmushi ya miko hannunsa ya dungure mata kanta bai ce mata komai ba, 

Alhinayettt ta ce” Wardugu ina kula samu buzuwa??

Wardugu ya yatsina fuska ya ce” hum, Ayya ce ta daukota wai ta yi y’a,

Alhinayettt ta ce” yarinyar ce ta birge ni, irin yanda tana buzuwa , bakar buzuwa aman bata bata bakinta ta hanyar shafe shafe ba, ina son mutun haka walahi…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button