BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Bayan tafiyarsu da kamar minti ashirin, Wardugu dai na nan zaune yana bin kowa da kallo ta kafurin bakin glass dinsa,Mintuna tsakani sai kukan jiniyar sojoji ta fara yin salama wajen,

Da farko tunaninsu ficewa zasu yi, sai dai abin kara yi masu salama yake,

Hajia Aisata dake zaune saman cinyar karuwinta suna shagali aka dokowa waya,

Dagawa ta yi da yannayin duniyanci ta ce” Ya?

Masu tsaron kofar Wardugu Place ne daya ya yi kiranta a tsorace ya ce” Hajia me motocin sojoji ke yi a kofar nan? Na ga sai jeruwa suke suna didirowa da alama wani suke jira,

Ai bata san lokacin da ta diro daga saman kafar mutumen ta ce” me me me ka ce? Sojoji? A nan? 

Bata tsayin jin amsarsa ba ta fito da wani irin gudu ta ce” du wanda ya san da hoda gabansa ya yi gagawar rabuwa da ita ga arnawa a kofarmu!

Nan fa wajen ya rikice, mutane du suka tsorata, 

Aka fara kokarin guduwa wasu na nufar motocin su da gudun tsiya wasu na auna tsayin katangar sai dai ba halin dirawa domin ga tsayi ga abin kama barawa an zagaye wajen da ita,

Du masu jan mayan nan suka aniya gudu suna boyewa wasu na watsawa cikin ruwa wanda kadan ta rage masa ya janye abinsa, manya manyan masu fada a jin wajrn suka fara nufarta suna tambayarta me hakan ke nufi? Dama ba da lamuncewar gwamnati ta bude wajen raba masu eh yane ba? Ba wanda ya daure mata a gwamnati?! 

Ita dai ta cire dogon takalmi sai bi take table table tana kara goge dan sauran hodar da wani farin tishu ita da yarenta masu aikin wajen, 

Du sun haukace sai ihu take yiwa mutane kan wa.inda tsiraicinsu ya bayanna sosai sai fadi take su yi maza su saka kayan da ya fi wannan, 

Sannan da gudu wata bagwariyar yarinya ta fito da abaya ta kawo mata ta luluba mata daidai nan tuni sojojin sun cafke masu tsaron kofar sun fara tura su cikin motar wasu kuwa na tsare masu bi ta hanyar da wa.inda ke zuwa a lokacin,

Wani sergent ne ya kali abokinsa ya ce” yau fa akoy buro.uba a wajen nan, domin lamarin na gida ne, fadan gida ne,

Kai ya girgiza ya ce” ai ba na gida ba, ko na waye ta tarowa kanta dan oga ya yi mata tashi daya! 

A guje ta karaso table din wardugu tana babala botiran rigar tana zuwa da mamaki mamaki haushi haushi ta ce” kai waye mai hular nan ne wai? Kai ana a yi maza a kawar da komai kai kana zaune kikam , to walahi bara ku ji kaf wajen nan dan na lura hoda ta coshe tunanin ku! Du dan iskan da aka kama da ita ba ruwana, tawa kaf ta wajen nan ta bi Wc! Ta hannayen ku kuwa ban sanku bama bale na san me kuka shigo da shi, kun kuwa san wajen da girma ba lale ne sojojin su yarda da ina iya control din kowa! 

A hankali ya dago yana hangen yanda ake shan tsere da mutanen tsakar wajen fa sojoji suna yi masu cafkar fara suna yin waje da su,

Ransa ne ya kara baci , me ya kai su kokowa da su? Su saka lasifika su yi magana kan du dan akuyar da ya nemi gudu za.a watsa masa tire a gaz! Aman sai wani guje guje suke da juna harma su yi tunanin mu tsarensu ne! 

Gilashin idonsa ya cire a hankali ya dago da jajayen idannuwansa ya sauke saman fuskarta , murya a dake a dage ya ce ” aman kuwa da kin ci amanar clients din ki *AISATA*, na ji kuna fadin client sarki ne ke kuwa kina ikirarin ba ruwanki dan an kama shi da hoda yana zuka, 

Mutuwar tsaye ne Aisata ta yi, mutanen wajen kuwa gannin mai maganar sannan ya karasa mikewa tsaye du ya saka suka rude abinka da mai laifi suka fara neman hanyar fita, 

A rikice ta nuno shi da yatsarta ta kusan baba ta ce” Wardugu? Wardugu! Wardugu, 

Ya ce” ki ajiye yatsarki da nuna da ita, ko ki hade yatsutsanki ki nuno ni da hannun baki daya, rashin tarbiya ne nuna baban mutun da yatsa Aisata! 

Wani irin juya ta fara ji, hankalinta tashe ta ce” aman kai da kanka zaka tonawa wajen nan asiri? Ka fa san mamalakin wajen, 

Sergent Kabir da ya shigo da sauri ya zo dan jin me Wardugu zai fada kiran da ya tura nasa ya ja ya tsaya ya sara masa,

Wardugu ya juyo wajensa ya ce” ankwa! 

Da sauri ya mika masa, sannan ya kara ja ya kame,

A bainar jama.a Wardugu ya ja hular kansa ya cire ya nufota ya ce” Madame *MARAHUT AISATA* iko ya kama ki bisa laifin buda gidan badala, yada mugayen ayuka a boye, da siyar da hoda a fili kuma a bayane, ki yi shiru ko dukan abinda kika fada zai yi aiki kan ki, kina da damar tsayar da lauya dan kare kan ki ko kwato incinki………

Yana fada ne yana sarkafa mata ankwa irin na an kamo barawo, kafi yake turata gaba da kansa ransa bace ,

Suna fitowa ya daga murya ya ce” lasifikha sergent! 

Ai kuwa da gudu aka fita aka kawo masa,

Ana kawowa tuni yan jarida sun halarta sun fara dauka abinsu, 

Wardugu na amsa daidai kunenta yana rike da ita hannunsana dama ya daga, a dake kalamai a rarabe ya ce” Duk wanda ya yi gigin guduwa daga wannan waje zai jawa kansa rigima, zamu saki batkonon tsohuwa (????????), koda kana da rashin lafia kan ka! Ku hade gaba dayanku tsakiyar wajen nan minti biyar na baku, du wanda bai zo ba tawa ce ni da shi!

Ji kake wajen ya dan lafa da iface iface, nan fa dan koke koken yan matan ya fara tashi,, wasu na dora hannayensu a kai suna ihun sun mutu sun lalace yau asirinsu ya tonu, wasu na kaico da tunanin mai tsaya masu domin dama ba wani abin iyayensu gare su ba , irin sun samu dan masu kudi ne suka zubar da tarbiya aji daraja irin ta ya mace suke bin su ana shan kida, wasu samarin sun sato motar gida ne an zo a more da yan mata haka ta ritsa su, wasu manyan mutane ne masu iyalai a gida suka baro suka dauko wata yar shilar suka zo a cashe, waje dai ya fara daukan kimtsi, waje ya yi tsit sai iza keyarsu ake ana waje da su, 

Murya kasa kasa Aisata ta ce” Wardugu, ka bar ni na kirayi abanka,

Bindigarsa karama ya daure a kugunsa kafin yake turata itama ya yi mota da ita,

A wannan rana Wardugu bai nufi gidan su Alhinayettt ba sai wajen karfe bakwai na dare,

Yana zuwa bai fita a motar su ta sojoji ba kira kawai ya yi suka fito ba tare da ya yiwa kowa magana ba suka duru a motar ya ja, inda Alhinayettt ta bi su da kallo ta koma tana shan dariyar mahaifiyarta na fadin” yau fa akoyta, Alhinayettt yau ana rigima a garinnan, kina ji shiru ? Ba galama basu fara kade kadensu ba

Alhinayettt ta yi dariya ta ce” Anna (Matar babansu ce), ai sai adu.a kawai, Wardugu Wardugu Kowa Wardugu, ni dai zan yi ta yi masa adu.ar Allah ya tsare shi……..

Gidan Ayya ya kai su, wace ke zaune tsakar gida da waya a hannunta sai dokawa wardugu kira take aman ba.a dagawa,

Ai tana gannin sun sauko ta nufo wajen su sai dai bai tsaya ba ya yi gagawar juyawa ya fece abinsa, domin ya sani ne yanzu har an fara zuwa wajenta, bayan ta sani shima bai isa ba , shima yana bin dokar ne ! 

Gidansa ya yiwa tsinke,

Nan ya tarar da Mota uku a ciki bayan na kofa da aka hana shiga,

Mita daya dai ta mahaifiyar Walyn ce, biyun ne bai gane ba, dan haka ya shige bangarensa yana haharde kafafuwa yana so ya je ya zauna ya kashe du wata waya dake yi masa kuka a kunne ta hana shi sakat sai doko masa kira ake shi kuwa ba wanda zai daga kiransa domin ba wanda zai saurara, ba tonon asiri ne ya yi niyar yi masu ba, ba huce haushi ne ya yi niyar yi wa mahaifinsa ko matarsa ba, abin ne ya daje shi, ya diro masa a lokacin da bai yi tunani ba, tashin hankalinsa shi ne…ta ina ake shigo da hoda har ta gama gari haka? Ya sani ne sai sun sha masifa fa lauyoyi, inda ya san ya shige gabansu harda dan gidan banban lauya baki daya, in ya yarda ya ce a saki mutane, iyayen yara da manya masu daraja zasu sako shi a gaba ace dan da yaronsa ne ! 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button