Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 17

     A tare suk rankaya gidansu Asabe, sai dai Bappi motar Dr Shamsu yabi yace Ramadhan ya koma gida, dan sanda suka fito barci ya samesa yanayi a cikin mota, ya sanshi da barcin wuri, dan shi ƙa’idarsa da tara na dare tayi to ya kwanta kuma. Sai dai kwana biyun nan daya tsinta kansa a NAYA hakan bai kasanceba, shiyyasa daya ɗan kaɗaice sai ya kama barci saboda tsabar buƙatarsa da yake yi.
      Rikicewa sosai Hajiyar Birni tayi da ganin Alhaji Hameed Harith Taura har cikin gidanta. Mutumin da bata taɓa tunanin koda ganin motar hawansa ba a hanya balle shi kansa. Babban abinda zai birgeka da shi babu wani damuwa ko tsantsamin gidan tare da shi, hasalima da aka kawo ruwa shine ya fara sha tare da godiya.
     Su M. Dauda dai an nutsu saboda hararar da Hajiyar Birni ke antaya musu tamkar ƙwayar idonta zai fito.

       “Kuyi haƙuri da lattin zuwan gareku matsayin wanda ƴarku tai kasadar bama kariya. Da farko dai naso ace sai ta samu lafiya zanzo da kaina na kawota gareku nai muku godiya na kuma baku haƙuri. Sai dai an samu akasin hakan a dalilin zuwan waɗan nan bayin ALLAH da ayanzu na fahimci shine mhaifin Raudhat. Duk da dai na haɗu da ita mahaifiyarta a aaibiti tun randa abun ya faru, hakama ku da bansan matsayinku garetaba har yanzun. Zanyi amfani da wannan damar domin neman afuwarku, ku gafarceni, da nasan Raudhat zatayi wannan kasadar domin ni tabbas zan dakatar da ita, sai dai masu iya mafana kance ƙaddara ta riga fata, sai muce ALLAH ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta. Ku kuma kuyi haƙuri ku koma tare dan na fahimci baƙwa tare da juna, kuma Raudhat batajin daɗin hakan”.
          Kafin kowa yace wani abu hajiyar birni ta amshe zancen cikin washe baki. “Ai muke da godiya ranka ya daɗe, ALLAH ya saka da alkairi bisa kulawar daka nuna akan Raudha, dan bamu taɓa zaton hakan ba. ALLAH ya kara lafiya da nisan kwana. Suko babu sauran aure a tsakaninsu dan saki uku ne yallaɓai……”
        M. Dauda yay wata zabura tare da fashewa da kuka. “Ni wlhy ina son matata kuma a bincika ba’a cikin hayyacina na saketaba ranka ya daɗe…”
       “Eh wlhy wani malami yace asiri Larai ta maka ai”. M. Gambo ya amshe zancen yana matsar kwalar ƙarya shima. Dan dukansu kowa da abinda ke ransa tsakanin shi da M. Dauda ɗin.
         Hajiyar birni ta amshe zancen da faɗin, “ALLAH yayama wannan malami albarka tare da Larai, dan sun taimakeni da suka aikata wannan asiri matsiyaci”.
     Kuka M. Dauda ya sake fashewa da shi yana fyatar majina da tsohuwar babbar rigarsa tare da matsawa zai duƙa gaban hajiyar birni ta daka masa tsawa. Itama Asabe miƙewa tai cikin masifa sai dai duk Bappi yay azamar dakatar dasu dan shikam baisan hayaniya a rayuwarsa.
        “Inaga dan ALLAH ayi haƙuri tunda dukanmu nan ba yara baneba. Kamar wannan magana tana buƙatar nutsuwa kuma tsakaninku ne. Dama nima akwai abinda ke tafe dani game da Raudhat. Dan tayimin abinda wani mahaluki bai taɓa minba a rayuwa, bani da abinda zan sakanka mata da shi amma ina buƙatar irinta a kusa dani. Ma’ana inason ku bani aurenta dan ALLAH ko ta hanyar hakan zan samu damar kwatanta mata kwatankwacin alkairin data min nima…”
       Gaba ɗayansu suka waro idanu a kansa, tare da auna shekarunsa dana Raudha. Cikin rawar baki Asabe tace, “Alhaji kai da kanka?”.
        Karon farko ya saki ɗan murmushi domin ganin yanda duk sukai diri-diri, gasu dai a mu’amulat tamkar mutanen banza, ƴarsu kuma nutsatstsiya kamila, amma ashe sun san abinda ya cancanta, amma bara ya sake gwadasu. Numfashi yaja ya fesar da gyara zamansa.
      “Eh ni da kaina”.
“Wlhy na baka ranka ya daɗe”
M. Dauda ya faɗa cikin zallo da rawar jiki yana sake gurfana gaban Bappi tamkar mai neman gafara.
Da sauri Asabe ta amshe da, “Nidai dan ALLAH ka gafarceni Alhaji ban amince ba, Raudha bazata auri tsoho sa’an kakanta ba. Son zuciyar da naso tafkawa a baya na biye maka Dauda kan alhaji Maude Dallatu ya kaimu ga zuwa wannan matsayin, yanzu ko na gane gsky mutuncin ƴaƴana da ƙyautata rayuwarsu yafiyemin komai a duniya dan sune gatan wata rana. K….”
        “K! Yima mutane shiru!!”.
Hajiyar birni ta faɗa cikin daka tsawar data saka Bappi toshe kunne tilas. Aunty Hannah ma da illahirin jikinta ke rawa tun fara mganar Asabe saurin fincikon Asaben tai baya da faɗin, “Asabe kina da hankali kuwa? Kinsan wanene shi a ƙasar nan?”.
       Kuka Asabe ta fashe musu da shi. Cikin matsar kwalla tace, “Adda ni babu ruwan da koshi ɗin wanene. Ina duba rayuwar ƴaƴana ce, bana fatan su tashi a irin tamu rayuwar, fatana suyi ƙyaƙyƙyawar rayuwa bawai ta kuɗi ko son duniya ba. Dan haka ku gafarceni, ko ni akace na auresa yamin tsufa balle Raudha”.
        A tare suka hayayyaƙo mata har M. Dauda dake jin a yanzu baya buƙatar lallaɓa Asabe, dan zata masa ƙafar angulu ta kaisa ta barosa. Ganin suna neman harmutsa falon Bappi ya dakatar dasu cikin roƙo. Sai da suka nutsu ya fara magana cike da dattakonsa da kamun kai.
        “Lallai wannan baiwar ALLAH ta fiku gaskiya, dan kuwa tayi ƙyaƙyƙyawan hange da iyaye da yawa kan kasayi harma da ƴammatan wannan zamani akan auren wanda yake da manyan shekaru. Lallai ke ɗin uwace ta gari, kuma na gode da yanda kika nuna mutuncin ƴarki da farin cikinta shine gaba a ranki fiye da kuɗi ko wani matsayin da rayuwa ke bama bawa mai ƙarewa. Banzo nan dan na koma da buƙatata ba. Dan haka zan sake roƙonki a karo na biyu. Ina son ki yarje mijinki mahaifin ƴarki ya bama jikana auren ƴarku dan ALLAH badan wani matsayi namu ba ko abinda muke da shi. Domin Raudhat a yanzu tana buƙatar ta samu tsaro kodan rayuwarta dake a cikin haɗari, to zamanta anan tare daku kuma komai zai iya faruwa harya shafeku. Badan mu zamu iya kareta ko hana wani ƙaddara sauka gareta ba, domin muma bayin ALLAH ne kamar ita, kamar kuma ku. Alkairin da taiminne yasa nakejin kwaɗayin ɗaukarta ta zama ɗaya daga cikin family ɗina. Ta kuma haifamin jikoki daga tsatsonta da nake fatan suyi koyi da ƙyawawan halayenta wanda tarihi bazai taɓa gogewaba daga abinda ta aikata na alkairi a gareni”.
      A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, tare da zubama Asabe ido. Zukatansu har zallo suke nason jin amsar da zata bama Bappin.
     Taja kimanin wasu dogayen mintuna tamkar mai nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
      “Amma dan ALLAH Baba miyasa bazaka duba akwai tazarar rata tsakanin jikanka da ɗiyata ba…..”
       “Babu wani banbanci ɗiyata, domin kuwa dukanmu ALLAH ne ya haliccemu, ya kumace mu bauta masa shi mai rahamane ga duk wanda yayi biyayya ga hakan, sannan mai azaba ne ga duk wanda ya bijire masa. Dan haka ki sani babu wanda yafi wani a gun ALLAH sai wanda yafi jin tsoronsa. Ni da ku da Raudhat duk abu gudane. Mutanene masu barci, masu kashi, masu mantuwa, masu shagala, masu… Masu…. Masu….. Da yawa.”
       “Hakane ranka ya daɗe. Na gamsu da bayaninka, zan kuma iya amincewa da buƙatarkane idan har Raudha ta amince da auren jikan naka”.
          Babu wanda baija ajiyar zuciya ba a falon, kafin suɗan ƙara tattaunawa da Bappi, daga ƙarshe yay musu sallama suka rakasa har wajen Dr Shamsu dake jiransa a mota dan shi bai shigo ba. Tare da su M. Dauda suka tafi, dan yace zai kama musu masauki tunda nan babu wajen kwana.
     Aiko sai murna suke tamkar su ciza uwawunsu dan daɗi😂😝………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button