Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 18

Typing📲

Episode 18

…………Tun bayan wucewar su Alhaji Hameed Taura Aunty Hannah keta faman kai kawo a ɗakinta da kiran number First lady. Sai dai kuma tayi kira yakai biyar amma ba’a ɗagaba. Ta sake duban agogo ƙarfe goma da mintuna ashirin da huɗu. Tasan yanzu first lady batai barci ba, da wahala kuma ace tana tare da president, sai dai idan wayar ta bari a wani waje. Wannan tunanin ya sata canza akalar kiran ta tura mata guntun saƙo, da ga haka ta ajiye wayar ta faɗa wanka zuciyarta fal wasiwasin ta yanda zata ɓulloma Raudha da Asabe su amince da auren nan cikin sauƙi.

WASHE GARI first lady ce ta tada Aunty Hannah a barci, dan ko sallar asuba bata tashi tayi ba har kusan 7am. Da ƙyar ta lalubo wayar takai kunnenta tana faɗin, “Hello waye?”.
      Amsar da first lady ta bata ya sata wartsakewa babu shiri ta tashi zaune. “Ranki ya daɗe sorry barka da safiya! Wlhy barcine a idona”.
          Kanta ta jinjina saboda amsar da first ladyn ta bata tana faɗin, “Okay to babu damuwa gani nan zuwa yanzun nan insha ALLAH”.

       ★

   Su Asabe na a falo suna karyawa aunty Hannah ta fito cikin gayu na ɗaukar hankali. Fatisa da Fatima dake sanye da Uniform ɗin wajen abincin Hajiyar Birni suka fara gaisheta da yaba ƙyan nata. Tai murmushi tare da musu alamar love da yatsunta. Kafin ta ɗauka doya guda a cikin plate ɗin Asabe. “Ƴar uwa barka da safiya”.
       Duk da Asabe tayi mamakin gaisuwar saita share ta amsa mata. “Barka dai Adda fita zakiyi ne?”.
         “Eh wlhy zan ɗanje wajen aiki ana nemana ne”.
     “Aiko da zakibi ta wajen asibiti ne dana biki sai na sauka dan inason yin magana da Raudha game da zancen nan na jiya karma suje su yaudareta abun yay nisa gara na sani”.
        Hajiya mama dake fitowa daga kicin a masife tace, “O ke Asabe wai mike damun kanki ne dan ALLAH? Ƙiri-ƙiri kina neman mana baƙin ciki da arziƙin dake tinkaromu!. Alhaji Hameed Harith Taura fa akace. kinsan wanene Taura kuwa a ƙasar nan dama Africa gaba ɗaya?”.
       Kafin Asabe tace wani abu aunty Hannah tai murmushi da amshe zancen tana ƙyaftama Hajiya mama babbar yayar tasu ido. “A’a Hajiya Mama karkiga laifin Asabe. Tana da gaskiya wlhy, ya kamata muji ta bakin Raudha mu kuma binciki halin yaron, dan aure ba abin wasa bane. Tunda ba kuɗin zata aura ba mai kuɗin zata aura”.
              “Yauwa Adda dan ALLAH ki fahimtar dasu. Dan naga su dukiyar waɗan nan mutanen kawai suke kallo har shi uban nata da dama kwaɗayayye ne. Yanzu idan ta auresa bata son sa, ko taje tana shan wahala fa? Ai kunga mun tauye mata rayuwa”.
         Hajiya Mama ta danne ɓacin ran maganar Asabe da ƙyar tana ƙaƙaro murmushi. “Hakane kuma Asabe yanzu na fahimceku. Ki bar Hannah kawai ta wuce maje wajen Raudha ɗin tare tunda dama jiya banje ba”.
    Badan Asabe taso hakan ba ta amince. Aunty Hannah tai musu sallama ta fice kusan tare da su Fatisa da zasu hau keke napep dan hajiyar Birni tuni ta jima da wucewa ita.

GOVERNMENT HOUSE

            Tun tattaunawar da sukai da aunty Hannah ɗazun da safe ta kasa zaune ta kasa tsaye, dakon shigowar shugaban ƙasa kawai take gidan, amma har zuwa yanzu ƙarfe goma sha biyu na dare babu shi babu labarinsa. Duk da dai tun kusan tara na daren ya shigo gida, sai dai sun shiga meeting ne shi da su Alhaji Yaro glass, kuma har yanzu basu fitoba. Tai ɗan gajeren tsaki tana tura hular kanta baya ta faɗa saman kujerar, duk da sanyin ac dake gauraye da falon wata irin zufa takeji mai mannewa iya fata da jini. Ta zame rigar sama ta kayan barcinta dan itama nauyi take mata saboda tsabar ƙaguwa. Rashin mafita ya sata zamewa ta kwanta a kujerar, dan ta ɗau alwashin ko zai kai asuba tana nan tana jiransa.
       “Gimbiyata kina lafiya kuwa?”.
Shugaban ƙasa da ya shigo a matuƙar gajiye ya faɗa lokacin da yake zubewa saman kujerar gefenta. Zumbur ta miƙe zane tana ware idanunta a kansa, sam bataji motsinsaba, duk da dama tasan shi bai damu da sallama ba dan zai shiga waje.
       “Lafiyar nan da sauƙi wlhy tun ɗazun zaman jiranka nakeyi anan excellency ”.
      Fuska ya sake ƙwaɓewa yana ture hularsa. Cikin tabbatar da matuƙar gajiyar dake tare da shi da barci yace, “Bushira kiyi haƙuri babu abinda nake buƙata a yanzu irin barci da wanka”.
         “Shiruna bazai yuwu ba, inko nayi to zai iya cutar damu baki ɗaya. Dan maganar ta shafi shugaban ƙasar da kuke son ɗorawa na wucin gadi” Bata bashi damar yin magana ba ta cigaba da tata maganar saboda ganin ya bada hankalinsa gareta. “Tunda ka sanarmin ƙudirinku akan Alhaji Hameed da jikansa daya kawo a maimakonsa naketa nawa ƙoƙarin nima. Dukanmu munsan Ramadhan a yanzu baida mata, tunda kune kukai sanadin rasa matar tasa, shiyyasa nake ganin a yanzu ma inhar kuna buƙatar mutuwarsa kamar yanda kuka tsara (wa’iyazubillah 🤦🏻) to dolene sai mun haɗa da matarsa, dan itace mafi kusanci da shi da zatai mana aiki batare da wani zargi ya shiga ba. Kaga kenan mune ya dace mu bashi mata a karo na biyu”.
        “To amma…..”
“Karka katseni excellency ”. Ta faɗa tana murmushi.
      “Nasan tambayarka itace bai wuce ina zamu samu ba? To na gama da wannan matsalar, yarinyar data bama Alhaji Hameed kariya a filin idi ɗiya ce ga ƙanwar Hannah tsohuwar matar Alhaji Yaro, kuma a yanzu haka Alhaji Hameed ya buƙaci su bama Ramadhan auren yarinyar, sai dai mahaifiyarta na neman bijirewa dan tace sai idan yarinyar naso. Amma babanta ya yarda saboda shegen ƙwaɗayi, hakama hajiyar birni da su su Hannah ɗin, duk da dai ita Hannah muna tare, dan itace ma ta tabbatar min inhar Asabe ta nunama yarinyar bataso itama bazata amince ba saboda tanada kafiya da son uwar sosai……”
       “Bushira sorry na katseki, ni abinda ban fahimtaba anan, ribarmi zamuci na shiga maganar tunda sun gama ƙulla zancen auren? Inhar kuma yarinyar zata iya bijirema auren muma zata iya ƙin amsar buƙatarmu ai. Sannan karki manta Hannah zata iya yin komai danta rama korar kare da Alhaji Yaro yay mata. Imagine ma ace kina tare da Hannah har yanzu batare dana sani ba”. 
       “Duk yanda kuke tunanin Hannah ba haka take ba, tana son Alhaji yaro har yanzu, kuma ta san ba laifinsa bane laifin Fanta ne. Amfanin auren yarinyar nan a garemu Hannah zata iya sakata tai mana aikinmu cikin siyasa batare da ita kanta tasan ita ta kashesa ba, kai koda ta sani ko muna tunanin zata sani itama zamu iya kashetan dan mulkin dai ya koma hannun Alhaji Yaro. Kasan kuma inhar zaka taimaka Hannah ta koma gidan Alhaji yaro zata aikata komai har mutuwar yarinyar, dan da arziƙi a garin wasu gara a naku, a garin wasunma gara a gidanku, a gidankun ma gara a ɗakinku, a ɗakinkun ma gara a kanka. So zataima kanta yaƙine itama”.
         Karon farko ya kwashe da dariya yana kamo hannunta. “Oh woow gimbiyata! yanzu dai na fahimci komai wlhy. Gaskiya kinada kai tawan. To amma mu yanzu wace rawa zamu taka?”.
       “Yauwa yanzu kai magana shugaban ƙasar NAYA. Abinda zakuyi shine ku samu mahaifin yarinyar ku jikesa da mahaukatan kuɗaɗe. A bashi gidan zama, itama uwar a jiƙeta tare da mahaifiyar su Hannah ɗin, dama duk wanda keda faɗa aji akan auren. Sannan ku samu Alhaji Hameed ku nuna masa goyon bayanku akan auren da nuna cewar yayi hallaci ya cancanci yabo, kar kuma ya yarda yarinyar ta suɓuce ga Ramadhan dan irinsu akeso ga mulki zasu taimaki talaka. So ko yarinyar ta bijire bataso bazata taɓa samun haɗin kan kowaba ita da uwar dole su amince”.
      Tashi yay kawai ya rungumeta, ji yake tamkar ya haɗiyeta dan daɗin wannan shawara tata. Tun a daren ya turama su Alhaji Yaro glass saƙo da ɓoyayyar number ɗinsa da su kaɗai keda a laƙa da ita akan gobe akwai mitin ƙarfe 6 na safe kafin ya fita office.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button