Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 18

BAYAN KWANAKI UKU

          Dukan shawarar da First lady ta bada su Alhaji yaro glass sun aiwatar da ita ta hanyar nuna cewa sunyine dan Alhaji Hameed Taura da kuma Ramadhan dake matsayin surukinsu a da, dama zamansa haka babu aure na damunsu. Hundred percent Alhaji Hameed Taura ya yarda.
      M. Dauda kam da su Hajiyar birni haukacewa sukai dan farin ciki, dan manyan kuÉ—aÉ—e da aka mallaka musu. M. Dauda, hajiyar birni. Asabe, Hajiya mama. M. Gambo. KuÉ—aÉ—ene da zasuja jari. Koda Asabe ta nuna hakan bai mataba hajiyar birni masifa ta dinga mata, harda rantsuwar inhar bata yarda Raudha ta auri Ramadhan ba wlhy sai ta tsine mata, kuma sai dai ta É—au Raudha subar garin dan bazata zauna inuwa guda da mai mata baÆ™in ciki ba.
     Kalaman hajiyar birni yay matuÆ™ar tada hankalin Raudha da aka sallamo daga asibiti yau, dan Alhmdllhi Æ™afarta tayi sauÆ™i sosai saboda kula da take samu da ingantattun magunguna gashi bata da Æ™an jiki. Bazataso a sanadinta a tsinema mahaifiyartaba. Sannan idan sun bar nan ina zasuje, tunda babu wanda ke garesu sama da su a yanzun. Dan haka tace ita ta amince zata auresa duk da batajin son Ramadhan a ranta ko kaÉ—an, sai dai a gani guda datai masa har zuwa yanzu tanajin kwarjininsa cike da idanunta, yayinda kalamansa ke zaune daram cikin ranta shiyyasa takejin matuÆ™ar tsoro. Amincewa aurensa na nufin tabbatuwar kalamansa gareta, sai dai kuÉ—i ya rufe idanun iyayenta sun kasa fahimtar ni’imar da suke ganin suna ciki BAƘAR INUWA… ce, gara ranar da suke ciki da ita. Zata amince domin gujema hawan tsinuwa akan mahaifiyarta, zata kuma amince dansu samu farin ciki koda ita zata rasa nata farin cikin. Dan duk wanda ya dubeta ya dubi Ramadhan ya tabbatar shi ba tsaran aurenta bane ba, kawai dai kakansa ya kalli abinda tai masane da tunanin zai mata tukuyci da auren alhalin bazai zame mata irin inuwar da shi yake hango mata ta jin daÉ—i ba.  

       A lokacin da waccan cakwakiya ke gudana a gidan su Raudha anan fadar shugaban Æ™asa shugaban jam’iyya ne ya fitar da sunan É—an takara a yau a zaman taron da akayi yau É—in na manyan jam’iyyar. Inda kamar dai yanda aka saba wasu suka nuna jayayya akan Ramadhan É—in kodan Æ™arancin shekarunsa, tare da kawo hujjar bai san siyasa ba, bakuma zai iya ba tunda bama zaman Æ™asar yake ba, bai san komai na wahalar talaka ba.
        Idanu Ramadhan ya rumtse da Æ™arfi saboda wani irin sarawa da kansa yake masa a dalilin hayaniyar da É—akin taron ya kaure da shi. Dama da Æ™yar Bappi ya sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna É“acin ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa’an Pa sai sa’annin Bappi baiji ko É—ar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki Æ™irjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa matasa ace anayi dasu a Æ™asar NAYA dan sune Æ™asar.
     A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuÆ™a zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin Æ™asar NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin Æ™addarar rayuwarsa. Da Æ™yar shugaban jam’iyya ya tsawatar akai shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za’ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu É“ace wasu ransu fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar.

    Wani meeting É—in su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaÉ—ai akan batun, kafin kuma da yamma shugaban Æ™asa da shugaban jam’iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A

         Koya ya shiga matuÆ™ar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiÆ™e da kuÉ—aÉ—e shi da abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama’a fankama da kuÉ—i da nuna sumafa sun kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiÆ™en ya dawo. Nan take aka fara Æ™ananun magana da dangantasu da É“arayi saboda hankalin jama’a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M. Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za’ai daga barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haÉ—a kai suka kai Æ™ararsu gidan hakimi, hakimi baiyi Æ™asa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da iyalansa haÉ—a Æ´an kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄).
          Hakimi da Æ´an fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa basu kuÉ—in nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan mutane da sukayi yasa hakimi saka Æ´an sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a É“ata lokaciba wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki.
        Nan É—in ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuÉ—i, sai dai shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda É—in suka ambata na manyan mutane. Sai ma hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne dan É“ata musu suna. Baiyi Æ™asa a gwiwa ba wajen fara neman waÉ—anda yakeda kusanci da su ciki harda Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taÉ“a haÉ—asu a jami’a.
         Da Æ™yar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A É—insa, bayan sun gaisa cikin mutunta juna matsayinsu na manya da Æ´ar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban Æ™asa ne sukai musu Æ™yauta. Sai da aka haÉ—ashi da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta email.
      Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaÆ™ar dake shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed É—in ba ran salla sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa.
     Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauÆ™in kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana Æ™yautata musu zato dan bai taÉ“a damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne bisa Æ™yaÆ™yÆ™yawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace Æ™arama kuma nutsatstsiya.
     Cikin Æ™anÆ™anin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alÆ™awarin za’a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a Æ™arÆ™ashin mulkin jiharsa take. Alhaji Hameed yayi matuÆ™ar farin ciki yayi kuma godiya.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button