NOVELSUncategorized

DIYAM 35

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman maama

Episode Thirty Five : A Glimpse

Yan uwa da yawa sunzo sun duba ni kuma sunyi min gaisuwar twins dina. Aunty Fatima tazo har sau biyu ita da yaranta, Adda zubaida tazo itama, sai daga baya sai ga kawu Isa nan yazo shida iyalinsa, sai a lokacin yake
tambayar inna nawa ne kudin asibitin? Tace masa kawai an biya shikenan sai ya bar maganar ba tare da yaji yadda aka yi aka biya din ba ko kuma waye ya biya ba. 
Da dare sai ga Hajiya Babba ita da wannan sister din tata, amma babu Saghir babu alamarsa, su inna suka karbe su babu yabo babu fallasa sannan suka tambayesu jikin Alhaji. Sunce yana asibiti har lokacin amma yana samun sauki sosai. Suka kawo min maltina da fruits. Na gaishe su sai Hajiya Babba tace “Diyam, banji dadin abinda kika yi ba ko kadan wallahi, kinga abinda ya jawo ko? Garin kiyayyar Saghir an kusa a rasa rayuka har hudu” Mama da dama kamar jira take yi tace “me Diyam din tayi” Hajiya Babba tace “innarta bata gaya miki ba? Saboda bata son Saghir bata son haihuwa dashi shine ta shiga daki ta rufe kanta wai gwara ta mutu ita da yayan baki daya, gashi nan yanzu yaran da basu ji ba ba su gani ba sun rasa ransu, ga kakansu can kuma rai a hannun Allah. Dan ma Saghir mai taurin zuciya ne da har dashi zamu hada muyi jinya” naji raina yana min zafi, hawaye masu zafi suka kawo a idona, na yunkura zanyi magana Inna ta dakatar dani tace “kar kice komai” ta juya gurin Hajiya Babba tace “wannan magana ce da Saghir ya fada, ita kuma Diyam ba haka ta gaya mana ba tace a gaban Saghir ta haife yara guda biyu yana sheka uban bacci, babu irin tashin da bata yi masa ba amma ko motsawa baiyi ba” sai sukayi dariya duk su biyun, yar uwar Hajiya tace “kuma yanzu ku da hankalin ku sai kuka yadda da wannan maganar? Wanne irin bacci ne mutum zaiyi har a haihu a gabansa bai san anayi ba?” Mama tace “baccin wadanda suka sha suka bugu mana? Wadannan kam aiko yanka su zakayi sai dai su farka su gansu a lahira” sai kuma suka daina dariyar, Hajiya Babba tace “Hafsa? Wacce irin mummunar magana ce kike jifan dan dan’uwanki da ita?” Inna tace “ba mummunar magana bace ba, gaskiyar magana kenan. Saghir shayeshaye yake yi, kuma wannan shayeshayen shi yayi sanadiyar mutuwar wadannan yaran. Wannan shine gaskiyar magana” Hajiya Babba ta juyo kaina, fuskarta babu annuri ta nuna ni tace “Diyam sakayyar soyayyar mu gare ki kenan? Sharrin da zaki yiwa dan uwanki kenan?” Na girgiza kai na nace “ba sharri bane Hajiya, in baku yarda da magana ta ba ku je gidan ku bincika, ku duba dakinsa na tabbatar ba zaku rasa kayan maye ba, ku duba motarsa ba zaku rasa kwalbar giya ba, in still baku yarda ba ku tambayi uwani ta baku labarin yadda ta kwace ni rannan a hannunsa wanda shine dalilin fara nakuda ta ba tare da lokacin haihuwa yayi ba, in still baku yarda ba ku tambayi mai gadin gidan, ai yana ganin dawowarsa gida kullum a buge yake shigowa” sai suka hada baki suna tafa hannaye suna salati “kuji yarinyar nan yar karama da ita amma ta iya shirya magana irin wannan? Ku kuma iyayen ta kuka hau kai kuka zauna dan kun zama butulu ko? Duk kun manta irin alkhairin da Alhaji yayi muku amma shine yanzu saboda abinda ya same shi har zaku juya masa baya ku dorawa tilon dansa sharrin shayeshaye? Dan kunga Alhaji iftila’i ya fada masa shine zaku juya mana baya?” 

Sai ta kama kuka yar uwarta tana rarrashinta. Mama da Inna duk suka tsaya suka saki baki suna kallonta. Sannan Mama tace “Hajiya saratu in kika ce haka baki kyauta mana ba, da Diyam da Saghir duk yayan mu ne amma dole a cikin su in wani ya kauce hanya zamu fada dan gyaransa ba wai dan bata masa suna ba. Bincike ya kamata ayi kamar yadda Diyam tace, wanda duk aka samu da laifi a cikin su sai ayi masa fada dan ya gyara laifukan sa” sai suka tashi cikin fushi suka fice daga dakin. Mama tazo ta zauna kusa dani ta goge min hawayen fuskata tace “kiyi hakuri Diyam, in dai shayeshaye halin Saghir ne wata rana zai yi ne a gaban jama’a yadda babu wanda zai musa”. Ni kam zuciyata zafi take yi min, an jima ba’ayi min abinda ya kona min rai kamar wannan ba, ya Saghir zai kala min wannan sharrin? How can they accused me of killing my own babies?

Washegari da safe Hajiya Yalwati tazo itama, tayi ta bawa inna hakuri wai abubuwa ne suka sha kanta ga Alhaji a kwance ga yara ga gida babu kudi. Sai Inna ta bata labarin yadda mukayi dasu Hajiya Babba jiya, sai tace “dalla rabu dasu, waye baisan Saghir yana shaye shaye ba? Amma su kullum sai su ke nuna kamar ba’a sani ba. Yanzu shima uban da ace lafiyar sa kalau kuna gaya masa zai musa”. Da daddare muna zaune Inna tana ta mitar cewa tunda muka zo asibitin Saghir bai ko kira waya ya tambayi jikina ba, bai bada ko kwandala ta magani ba bai kuma nemi yaji inda muka sami kudin maganin ba. Tace “wannan wanne irin aure ne?” Na dauke kaina dan bani da amsar da zan bata. Bayan mun kwanta na yi mata tambayar da take raina. “Inna Sadauki kuwa ko yasan bani da lafiya? Yanzu shi ko duba ni ba zai zo yayi ba ballantana yayi min gaisuwar wadannan yaran? In babu aure tsakanin mu ai akwai shakuwa ko? Shi din tamkar yaya yake a gare ni” sai tayi shiru kamar bata jini ba, sai can tace “Diyam bansan inda Sadauki yake ba. Yaya ladi ma da naje nemanta gidan Alhaji Bukar ance min ta tashi kuma basu gaya min inda ta koma ba” na mike zaune nace “nemanta kikaje yi inna?” Tace “eh, naje nemanta da niyyar in bata gadon zainabu na gidan ku kamar yadda kika bani shawara amma ban same ta ba. Bansan ya zanyi ba yanzu”. Nayi ajjiyar zuciya kawai ina wondering what happened? Ina Sadauki? Ko yana bornon? Ya samu admission din kuwa ko bai samu ba? Is he doing well? Na lumshe idona ina hangen fuskarsa a cikin kaina.

Washegari bayan an gama duk tests din da za’a yi suka sallamemu, muna shirin tafiya sai ga mutanen gidan Alhaji Babba nan sunzo, har da saghir, a lokacin ne suka fada mana an sallami Alhajin shima jiya, Hajiya Babba tana ta wani yayyatsina tana bata fuska, shi ogan ma a bakin kofa ya tsaya ya gaishe da Inna sannan yace min “sannu” na tattara shi na bawa iska ajjiyarsa. Budar bakin Hajiya sai cewa tayi “amma Diyam gidan ta za’a mayar da ita ba ko?” Inna ta tsaya tana kallon ta tace “ban gane ba” Hajiya tace “ina ganin abinda yafi shine ta zauna a gidanta, sai a tura wata matar haka take kula da ita kafin jikinta yayi kwari saboda kinga shi Saghir kinga babu dadi a barshi shi kadai a gida ba mace” Inna tace “haka ne” sai ta yafa mayafinta ta kama hannuna muka mike, ranta ya baci sosai. Tace “shi Saghir din yasan yana da matar amma tunda ta kwanta kwana bakwai bai waiwayo inda take ba? Shi Saghir din shin anyi masa fada akan abinda tace yanayi ko kuwa haka za’a kuma daukanta a mayar masa in yaso ya karasa kashe ta? Ina son Diyam fa nima ba wai bana sonta bane ba, ina kawaici ne kawai saboda karfin zumuncin da nake hangowa a tsakanin mu amma kuma kunsan wallahi da mahaifinta yana da rai ko soma maganar nan ma ba za’ayi ba ballantana ayi ta” Aunty amarya tace “haba Amina, yanzu kiri kiri a gaban mu kike nuna Diyam taki ce ba tamu gabaki daya ba, yanzu zumuncin har yakai haka tabarbarewa?” Na juya ina kallon Saghir har yanzu yana tsaye da hannayensa a cikin aljihunsa yana bin kowa dai dai da kallo, naji a raina ni kam ko inna ta yarda da komawa ta gidansa ni ba zan koma ba, gwara in shiga duniya yafi min sauki. Na zame hannuna daga na inna na fice daga dakin.

A bakin gate din asibitin na tsaya ina sharar hawaye, sai ga Inna da saurinta ta rike ni, “Diyam ya akayi kika fito ke kadai? Ina zaki je?” Na sunkuyar da kaina bance mata komai ba. Muna tsaye a waje suka fito, Saghir shi kadai ne a motarsa sai Hajiya tace ya dauke mu, nasan a lokacin da inna tana da kudi da ba zamu shiga motar Saghir ba amma dai haka muka shiga muka zauna a baya mu biyu, yana ta wani bata rai irin shi ba haka yaso din nan ba. 

Ina zama na kwantar da kaina na lumshe idanuwana ina tunanin ta inda zan fara neman Sadauki, I just want to see him koda bance masa komai ba. Naji ya tayar da motar, sai naji Inna tace “Yakasai zaka kai mu” nayi saurin bude ido na ina kallonta, a raina nace ‘finally’ Finally Inna ta yi breaking out of her shell zata yi flying, to kawai yace mata ya dauki hanyar gidan mu. Naji mun tsaya na kuma bude idona sai naga traffic light ce ta tsayar damu a gefen asibitin, na dan sauke glass din windown da nake saboda in sha iska tunda babu ac, kamar daga sama naji kamar an ambaci sunana da muryar da ba zan taba mantawa ba, nayi saurin dago kai amma sai naga su inna kamar basu ji kiran ba, and then I smelled him, wani unique smell wanda daga gurinsa kawai nake jin sa, nayi saurin kallon window na and there he was, Sadauki, yana tsaye da hannayensa cikin aljihunsa yana kallona da budaddun idanunsa. Yayi loosing weight sai naga kamar ya kara tsaho, fuskarsa da kansa suna bukatar aski. Na zauna kawai ina kallonsa as the time froze and my heart stopped. He just stood there looking at me, sai kuma na kwalla masa kira “Sadauki!!” Inna ta juyo a tsorace ta riko ni tana tambayata lafiya, na juyo na kalleta sannan na juya da niyyar nuna mata sadaukin dana gani but ge was gone, as if yayi vanishing.

Kuka nake iyakacin karfina ina kiran sunan Sadauki yayinda Inna ta rike ni take tofa min addu’a, Saghir kuma yana bala’i duk da bana jin abinda yake cewa nasan akan kiran sunan Sadauki da nake yi ne ni kuma ban daina ba. 

Manage this please

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button