BidiyoBoko HaramChibokLabarai

Bidiyo:; Bayan Shekara Takwas Daya Daga Cikin Yan Matan Makarantar Chibok Ta Tsere Daga Hanun Yan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus da aka yi garkuwa da ita tare da wasu da dama daga makarantar Sakandaren mata ta gwamnati ta Chibok da ke Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014.

Dakarun Sojoji na 21 masu sulke a garin Bama na jihar Borno sun ceto Ruth da danta a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, bayan ta tsere daga hannun ‘yan Boko Haram da ke yankin karamar hukumar Bama ta jihar.

A cikin wani faifan bidiyo da Zagazola Makama, masani a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi ya fitar, Ruth ta ce ta tsere daga dajin Sambisa shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace ta daga makarantarta da ke garin Chibok.

Ta ce, dan ta’addan da ya mata ciki, yaje hada bom ne bom ya tashi dashi anan ya rasa ransa.

Ta kara da cewa har yanzu sauran ‘yan matan makarantar na tare da wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa.

“Na dauki kwanaki uku ina tserewa daga yankin  Na dauki abinci amma ba yawa dan  yaro na na dauka.

Wasu daga cikin ‘yan Boko Haram sun ganni a lokacin da nake fitowa amma sai na gudu daji don gudun kada a kama ni,” inji ta.

Ga dai bidiyon ku kallah kuji daga bakin ta:;

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button