BAKAR WASIKA 1

Inna ta daga kai ta kalleshi yana kokarin jingine babur din ta ce.
“Ka dawo?”
“Eh ya gidan?”
“Lafiya Kalau, ya kasuwa”
Ya dan yi jimm cike da damuwa sannan ya sauke ajiyar zuciya.
“Kasuwa da godiya Inna, amman abubuwan kasar nan sai hamdala, komai kara masa kudi ake, idan baka da wani babban jari yanzu sai kasuwancin ma ya gagareka”
“To ya za’ayi kasar ce ta zama abun da ta zama, Allah ya ba mu azzaluman shugaban ni, ba su da tausayi kansu kawai suka sani”
Cewar Sanisu yana nufo inda suke, Sai Amadu ya amsa masa.
“Wallahi ga rayuwar mutane an maida ta kamar ta dabba, kai har kara ma dabba a yanzu, kuma sun kasa daukar mataki basa ma son ana ji, Nigeria kam ban san yaushe zata gyaru ba”
“Allah ya kyauta, ni dai na wuce shago”
Sanusi ya sake fada, sai Inna ta bishi da addu’a.
“To Allah ya tsare ya bada sa’a”
Har ya fice Aminatu bata dago kanta ba, ko da wasa bata son ta hada ido da Amadu, ba ganinsa kadai ba ko muryarsa ta ji sai ta ji gabanta ya fadi.
“Inna Ina Lami kike neshen dawo da kanki? (Saka fura a tukunya)”
Amadu ya tambaya.
“Kai ma ai kasan bata nan, da tana nan ai ba zata bar ni nai wannan aikin ba, ta je ganin dan Kuidu (Kaciya)”
Ya shaf kansa.
“Na manta ta fada min, abubuwan ne sun yi yawa Wallahi”
Ya fada yana nufar bangaren da Iyalinsa suke. Domin irin katon gidan nan ne na kauye mai fili wanda yaya suke dibar bangare suna kafa na su iyalin, bayan shi da yake da mata daya, Musa mai mata biyu ma a gidan yake zaune, sai dai shi ya fitar da kofar gidansa ta can baya sai an zagaya za a iya shiga, Iro da Sanusi ma da ke shirin aure a cikin gidan suka gina gurin da za su aje matansu.
TALBA POV.
Yana zaune a dining din har Momy da Baaba suka gama hada abun karyawa. A hankali ya dago yana kallon yadda Baaba take jera kulolin, hannunsa suke da wayarsa. A hankali ya lumshe idonsa ya bude, cike da kasaita ya motsa bakinsa, yana maida dubansa gurin Momy wanda taja kujera ta zauna.
“Baaba a fadawa yaran nan su fito su karya”
Matar da aka kira da Baaba ta dan risinawa Momy cike da ladabi.
“To ranki ya dade”
Ya nufi upstairs da sauri, da ido Talba ta bita kamin ya maida dubansa gurin KB da ya fito a daya daga cikin kokafin da suke can dayan bangaren falon.
“Momy ina kwana”
KB ya fada yana kokarin jan dayar kujera ya zauna, sai Momy ta amsa masa ba yabo ba fallasa, sannan ya mikawa Talba hannu suka gaisa, ya shiga hadawa kansa tea. A tare Amal da Leila suka sauko downstairs din, kai tsaye suka nufu dinning area, Amal da far’arta kamar kullum, Leila kam sai wani sham kamshi take musamman da ta hango Talba a zaune a dinning din.
Amal ce ta riga isa ta zauna tana fadin.
“Ya Talba Morning”
Ya kai dubansa gareta yana sakar mata murmushi as respond, irin murmushin nan da be saba zama a fuskarsa ba. Bayan ta gaishe shi ta gaishe da KB.
“Ya KB Morning”
“Morning Amal”
Ya amsa yana kai plantain a bakinsa. Leila na zaunawa Talba ya mike tsaye cike da izza, sai duk suka kalleshi.
“Ah ah ba karyawa za kai ba?”
Momy ta tambaya.
“Zan yi breakfast a waje”
Ya amsa kamar an amsa dole, already yayi nisa da dinning din. Sai da ya fice daga falon gaba daya sannan Momy ta kalli Leila.
“Kun sake yin fada ne?”
Leila ta kalleta cike da damuwa.
“Momy miyasa kullum ni ce mai laifi?”
Momy ta zare mata ido.
“Yes tun da ya dawo sallah asuba yake zaune a nan, idan har babu komai to babu abun da zai saka ya zauna tun 6:30 har 9:30 dan kawai kin zauna kuma ya tashi ya ce ya zai karya a waje, zan kaiwa Daddynku abinci yanzu, ki same ni daki anjima”
Momy na fadar hakan ta mike tsaye ta dauki wasu tsadaddun kuloli ta nufi kofar da zata sadata da bangaren Daddy.
“Ni ma ba zan karya ba”
Amal ta fada tana turo baki alamar ranta ya bace sai harara take watsawa Leila kamar ba yayarta ba, sannan ta mike tsaye ta fice daga gurin ta nufi upstairs.
“Munafuka, ai daman tun da Yayanki be ci ba ba zaki ci ba Mtschesss”
Cewar Leila tana binta da harara. KB ya bi Amal da kallo har ta shiga dakinta sannan ya kalli Leila.
“Da gaske fada kuka yi kenan?”
“Ai dole mu sake fada kuma mu yi ta fada, na gaji da halin Talba, na gaji, shi ba dan sarauta ba, ko yan sarauta ba su abun da yake, ba baiwarsa ba ce ni, and i hate nonsense”
Mikewa tai tsaye a fusace har tana jefa da empty cup din dake gabanta, a take ya fadi kasa ya fashe, kamar zata tashi sama haka ta nufi upstairs. KB ya wara ido.
“To ni ina ruwana, can ta matse muku, a takaice dai ni kadai zan karya a yau… Fine”
Ya sake bude wata kular ya shiga zubawa kansa ferfesu.
FARUQ POV.
Ya aje kofin garin dake hannunsa yana kallon dansa.
“Ka koshi ko?”
Sultan ya daga masa kai yana murmushi kamar yadda shi ma yake masa murmushin. Faruq ya dauke shi ya dora saman kafafuwanta sannan ya kalli Mahaifiyarsa cike da damuwa.
“Mama bari mu tafi kar dare yai mana”
“Kara ka tafi da wuri kam tun da a kafa zaka je”
Ya mike tsaye.
“To sai da safe ayi ta mana addu’a dai”
“Addu’a ai dole ce Faruq, Allah ya tsare, Sultan sai da safe ko?”
“Sai da safe Mama”
Sultan din ya fada da muryarsa da be gama kwarewa da iya magana ba. Daukarsa Faruq yai ya fice daga gidan, a kafa ya taka tun daga unguwar dallatu har Gadar Baga, ganin Sultan ya fara bachi sai ya dora shi a kafada Faruq, yana tafe gabansa na faduwa har ya iso gidansa. Sai da ya saka hannunsa aljihu ya lalaba garin kwakin dake cikin aljihun wandonsa da sugar ya tabbatar suna nan sannan ya kwankwasa kofar gidan. Yayi kusan rabin awa a tsaye sannan Rafi’a ta bude masa. Ganin babu komai a hamnunsa yasa ta ja tsaki.
“Mtcheesss”
Be ce mata komai ba ya saka kafarsa ya shigo cikin madaidacin gidan na zaman mutum daya, sannan ya maida kofar gidan ya rufe. Da sallama ya shiga cikin falon amman ta ki amsa masa sai latsar wayarta take kamar bata san da shigowarsa ba. Be damu ba domin in da sabo ya saba da halin matarsa. Dakinsu ya shiga ya kwantar da Sultan sannan ya dawo falo ya zauna kusa da ita, kana ya ciro garin da ba zai wuce gwangwani daya da rabi ba da surga ya mika mata.
“Ga dan abun da muka samu”
Daga shi har garin kallon uku saura kwata ta watsa masa.
“Gari fa nake gani Faruq?”
“Shi ne”
Ya amsa mata kamar wani yaronta.
“So kake jinina ya tsotse ne? Kara min jinin ma ya gagara? Haba Faruq, na wuni ban ci komai ba kuma yanzu ka shigo min da gari?”
Ta masa maganar kamar zata fashe da kuka, ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
“Haba Rafi’a tun da kika ga na shigo miki da gari ai kin san ban samu komai ba ne, shagon na mu sabuwar unguwa ce ba a samun ciniki sosai, tun da na fita har babu wanda ya zo aski, wannan garin ma sai da na biya ta gida Mama ta siyo min aka jikawa Sultan ya sha sauran ne na kawo miki, Wallahi ni tun karin safe da na yi ban sake cin komai ba, kara ke na bar miki gwangwani biyu na wake…”
Be marasa ta mike tsaye tana masa ihu.
“Kai ka so Faruq kai kaso zama da talauci, sa’aninka suna can sun gina manyan gidaje wasu na da manyan motoci, su ci mai kyau su saka mai kyau, amman kai dube ka? Suturar kwarai ma ta gagareka, ni kaina da nake matarka ina kunyar a tararda ni a gidan nan, gida duk ya lalace, da an yi magana kace komai zai wuce sai yaushe zai wuce? Shekara biyar fa da aurenmu Faruq, ka dube ni ka gani tsabar kyau Baturiya ake ce min fa! Amman na kare a aurenka, auren kaddara auren cin garin kwaki, dan sunan mai dadi ma baka iya kirana da shi ba, Rafi’a Rafi’a, Fee’ah Fee’ah haka ake kirana ba Rafi’a ba”