BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 10

Page -1️⃣0️⃣

Talba ya mikawa Daddy wayar bayan ya gama dubawa.

“Daddy ku da kuke kusa da gobnati ya kamata ace kuna fada musu halin da ake ciki mana, mutanen nan suna cikin bala’i, kamar ni ne, kana zaune kana rayuwarka sai a iskoka a koreka daga gidanka a akashe yayanka kuma a keta haddin matanka, Wallahi tausayi suke ba ni matuka”

Cewar Talba cikin wani irin bacin rai da jin zafin abun da yake faruwa. Daddy yayi murmushi yana gyara zamansa.

“Mu’az kenan, waya fada maka gobnati bata san halin da ake ciki ba? Sun san komai, wannan matsalar tsoro tana kawo kudi sosai, fiye da yadda kake tunani, duk jihar dake fama da matsalar tsaro kudin da ake ware mata dabam, idan har aka magance matsalar to abinci wasu zai tsaya, kuma duk jihar da kaga suna fama da matsalar tsaro to suna da cigaba da ake bukata”

“Amman Daddy basa tsoron hakkin rai?”

“Wannan kuma ai sai lahira, Allah dai ya kyauta kawai amman matsalar tsoro a yanzu abu ne mai wahalar magancewa, domin an fi samun kudi ta gurin tun daga manya har kanana, na mu dai addu’a ne, da kuma taimaka musu da abun da Allah ya ba mu”

A hankali Talba ya busar da iskar bakinsa ya kalli Amal data doso inda suke sanye da uniform dinta na makaranta.

“Na yi magana da PA zai yi list din abubuwan da zamu siya mu kai musu soon”

“Maa Shaa Allah, hakan na da kyau”

“Wa za a kaiwa? Baaba?”

Amal ta tambaya tana aje fular abinci. Daga Daddy har Talba kallonta su kai, ta san ba maganar Baaba ake ba, kawai ta dauko maganar ne saboda tana son fadawa Daddy abun da ya faru ne, daman ita ce yar gulmar gidan komai akai a bakinta za aji.

“Wace Baaba kuma? Yan gudun hijira ake magana”

“Au na dauka Baaba za a kaiwa, Allah yasa dai ta ji sauki”

“Miya same ta?”

Daddy ya tambaya, a nan Amal ta zauna gefensa ta labarta masa irin abun da ta fadawa Talba.

“Taya Doctor zata yanke wannan hukunci bs tare da sani na ba? Tafi ki kirata”

Daddy ya fada rai a bace. Sai ta mike tsaye gabanta na faduwa.

“Ya sai ka ce ni kai ka fada”

Talba yayi murmushi, ita ma murmushin tai ta fice, bayan ta wuce Daddy ya kalli Talba.

“Ka san da maganar ne?”

Talba yayi shiru ba tare da ya amsawa Daddy da eh ko aa ba. Wanda hakan ya tabbatarwa da Daddy cewar ya sani kenan, domin idan be sani ba kai tsaye zai fadi cewar be sani ba.
Daddy be sake cewa komai ba har sai da Momy ta shigo dauke da wasu manyan kulolin abinci ta aje a gabansa, sai da Momy ta kalli Talba sannan ta kalli Daddy tana karantar yanayinsu.

“Lafiya dai engineer?”

Daddy ya kalleta irin duban da ke fassara mata bacin ransa.

“Baaba ta fado, har kun kaita asibiti amman baki sanar da ni ba”

Dagowa Momy tai ta kalli Talba da kansa ke kasa.

“Ina ganin kamar karamin abu…. ”

“Karamin abu? Da gaske? Amina kin san abun da kike fada kuwa? Mutum ya fado daga sama zuwa kasa ki kira shi karamin abu? Idan har karamin abu ne yayanta zasu dauke ta su tafi da ita ne? Ko da ma karamin ciwo ne tun da har a nan ta samu matsalar ai ya kamata ki sanar da ni, kuma be kamata a bar yayanta su tafi da ita ba, a nan ya kamata a dauki nauyin komai na ta, shekara biyu tana aiki tare da mu”

“Ranka ya dade, ba wani ciwo ne sosai ba, kuma na kaita asibiti sun bata magani sai ta kira yayanta tace zasu tafi da ita, babu yadda ban yi ba amman suka ki yarda, kuma ina da niyar fada maka anjima da dare idan ka natsu”

“Yanzu idan wata ce a cikin yayanki ta fado zaki mata haka ne? Balle tsohuwa? Sometime kina abu kamar damuwar wani ba damuwarki ba ce”

“Allah ya huci zuciyarka Engineer, amman be kamata damuwar wani ta dame mu ba, mu ma yanzu idan muka shiga cikin wata matsalar babu wanda zai damu da halin da muke ciki”

“Okay, yayi kyau daga yau ba zan sake biyan mai aiki ba, indai zan dauki mai aiki ta taya yaranki aiki ne ba za a sake ba, idan har damuwar wani be kamata ya dame mu ba, karki sake gabatar min da wata matsalar yan’uwanki balle kawaye”

Yana kaiwa nan ya mike tsaye a fusace ya nufi hanyar dakinsa. Momy ta rutse ido ta bude ta kalli Talba da shi ma kallonta yake domin ya san shi zata dorawa laifi.

“Karamin abu ma, sai ka tasa mahaifinka a gaba kana tsegunta masa? Talba wacce irin rayuwa ce wannan? Mun yi fada hankalinka ya kwanta? Kuma zai fita be karya ba, ina tunanin haka kake so ai? Kai na ya fara kwnacewa da lamarinka”

Uffan Talba be ce ba, har tai ta gama ta mike tsaye ta fice, mikewa yai tsaye ya ciro wayarsa dake ringing.

“Ali”

Ya fada bayan ya danna picking.

“Talba ka fita office ne?”

“No ya akai?”

“No ina son magana da kai ne, na dauka kana office na biyo”

“No yanzu zanje, yau da wuri zaka je aiki kenan?”

“Eh muna da patients da aka kawo mana, kasan sojoji sun samu kwato wasu daga cikin wadanda yan bindiga suka tafi da su, akwai wadanda suka samu rauni sosai an kawo mana su”

“Eh na ji an kai hari abun ba dadi Wallahi”

“Sosai an kawo wasu shekaran jiya wadanda suka harba abun ya kazanta”

“Allah ya kyauta, We can talk later”

Ya sauke wayar, sannan ya nufi kofar fita yana kiran Jahid.

AMINATU POV.

Labarin harin da aka kai ya karade ko’ina a Nigeria, gidanjen jaridu da kuma kafofin sada zumunta. Hakan yasa aka turo jirgin sojijin tun daga jihar Lagos har zamfara.
Kwashe gari aka bi su da danyen dankalin hausa a hannu duk wanda aka gutsawa sai yai sauri ya cinyewa, bayan sun gama ci kuma sai a bisu duka musamman wadanda aka akai maganar kudi da yan’uwansu ba su kawo ba. Sun fi dukansu fiye da kowa, duk abun da ake Aminatu na kwance bata iya komai ba, har yanzu bakinta a nauyaye yake, idanuwanta ne kadai abun da suke aiki a jikinta sai numfashi. Tana kwance galala ta daga kanta sama tana kallon jiragen sojoji guda biyu da suke shawagi a sama, kararsu kadai ta isa ta kurmantar da mutu, sun yi kasa kamar zasu saki wuta sai dai ba su saki wutar ba suka gangara can nesa da damarsu suka saki wutar a inda babu mutane.
Bayan ya wuce barayin suka fito daga gidanjensu na bukka dake can nesa da inda aka daure su Aminatu, suna da yaya da mataye a cikin bukokin sai dai akwai tazara mai yawa a tsakaninsu.
Suna isowa inda suke mutunen jiya ya sake rokon su bar shi yai sallah, sai suka hau shi da zagi.

“Kawo shi nan”

Dayan ya fada, sai sauran suka kwantoshi daga inda yake suka nufi wata bushiya inda mutunen yake, suka daureshi jikin icen suka sako kansa kasa kafafuwansa a sama yana ta lilo.
Tun yana kuka yana rokon su kwance shi har ya gaji ya fara kalmar shahada, majina ta fara fitowa ta hancinsa tana zazzagowa kasa tare da hawayensa.
Ba su kwance shi ba sai da su suka tabbatar rai ya bar jikinsa, sannan suka sauke shi kasa, lumshe ido Aminatu tai wasu hawayen suka cika mata ido.
Bata sake bude idon ba sai da ta sake jin karar jirgin, wannan karon da fatan mutuwa take kallon jirgin burinta ya sako wuta kowa ya kone har ita, domin tana da tabbacin babu wata rayuwar jindadi a tare ita ko da rayu! Ta ina ma zata rayu? Taya zata fita a nan? Idan ma ta fita gurin wa zata je? Da wa zata zauna? Wa zai rike ta? A kashe mata kowa, yayyu da iyaye, idan zata nemi yan’uwan uwa ko na uba ta ina zata fara nemansu? Ina zata gansu? Zata fita a nan ma?

‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’

Ta maimaita a cikin ranta, domin bakinta ya mata nauyin da bata iya saka komai ta tauna balle har ta furta wani abu, wata kila kalamanta sun kare wata kila kuma har da rayuwarta, farinciki kam ta tabbatar da ya barta. Bayan sallah isha’i ta dan unkura ta tashi zaune tana jin kamar ba zata iya zaman ba kuma gashi ta gaji da kwanciyar. Hannunta ta kai ta damki kasar gurin ta junke a hannunta da wani irin karfin zuciya, sai dai na jiki kam babu shi ko kadan a kusa da ita, a galabaice ta dago kai tana kallon mutanen da suka doso inda suke da manyan fitulu suna haske su, matasan yan bindigar ne suka kwance matan kusan shiri maza takwas, a cikin mutanen da aka kwance har da Aminatu.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button