BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 10

“To ku fadawa sauran dabobi an yi diyya kar sai mun kama hanya su bude mana wuta”

Wanda yai maganar fuskarsa a nade take da rawani babu ta inda zaka iya ganinsa balle ka shaida shi, sauran yan bidigar kuma wasu na sanye da rigar soja wasu kuka wandon suka saka wasu kuma duka biyu sai dai dukansu suna dauke da manyan bindigogi.

“Ai dai hanyar da suka biyo zaku bi karku kuskura sauya hanya, idan ba haka ba zaku hadu da wata dabar, kuma za mu aika musu”

Dayansu ya fada, sannan aka fara dukansu da bulala aka korasu kamar dabbobi.

“Ku wuce yan iska, ni na tsani kado Wallahi”

Cewar dayan yana dukansu, masu kuzarin cikinsu suka tashi suka fara tafiya ban da Aminatu da sauran da akai ma fyade kamar ta, ganin hakan yasa mutumen ya roki a dorasu akan babur, a fitar da su sauran da suke iya tafiya a kafa kuma a korasu a kasa. Wadanda aka kora a kasa suna tafe suna jin tsoro saboda daukin ba dadin da ake da babbar daba, daman can sun fi kowa dauka da zafi, karama daba kudin fansarsu ba su da tsada kuma ba da taurin kai kamar babbar daba, kasancewar karamar daba matasa ne masu tasowa wasu ma duk yara ne, babbar daba kuma manya ne wadanda suka dade a cikin harkar.
Su Aminatu sun riga isa kusan da bakin dajin saboda an dauke su a babur, sai dai zubesu akai a kasa suka zauna a gurin har sai da na kasan suka karaso sannan aka hadasu aka nuna musu hanya. Sauran wadanda sukai musu rakiya kuma suka juya suka koma ana kusan kiran sallah asuba suka fiton daga dajin, Aminatu na tafiya daker tana hawaye, idan ta gaji da tafiyar sai ta zauna a kasa ta yi rarrafe idan ta gaji sai ta unkura ta mike tsaye ta fara tafiya.. Da haka har suka iso bakin gari a inda motocin sojojin suke. Da farko sun tsorata duk kuwa da kasancewar an fada musu akwai sojoji a gaba, sai dai ganin a cikin barayin ma akwai masu uniform din sai ya saka wasu suka tsorata, sai dai kana ganin wadandan sojojin kasan zaratan sojoji ne ba kamar yan bindigar ba. Karasowa sukai suka dauki mutanen a mota, Aminatu kuma da ire irenta suka daukesu suka saka a motarsu, suka kama hanyar gari da su.
Ko da tara na safe ta yi, labarin nasarar da sojojin suka samu a kokarinsu na kwato mutanen da akai garkuwa da su ta kwarade ko’ina, labarin barin wutar da akai ya shiga lungu da sako na nigeria, ya leka gidan jaridu ya cika social media.
Masu lafiya aka tafi da su inda za a buka fuskarsu ayi ado da su a jaridu, marasa lafiyar kuma aka wuce da su asibiti a sirrance.
A tsakanin iskar dake dajin dana cikin gari zuwa na asibitin da aka wace da su Aminatu ko wane dabam, na dajin na tawaya ne da damuwa da bakinciki, shigowa garin kuma samun iskar yanci ne, sai dai shiga asibiti kuma na fata ne, wata kila ta rayu wata kila kuma rayuwar ta zaba mata mutuwa.
Mutanen da suka zo da gudu suka karbeta a hannun sojan daya dauko ta, sai su ka yi mata kama da wata halittar da taban kasancewar suna cikin farin uniform ne na aikinsu. Lumshe ido tai tana sauraren yadda aka dagata sama aka dorata saman gadon asibiti ana turata.

FARUQ POV.

A gurin mai shagon ya karbi wayarsa, ya saka line sa ya kira number Baturiya ya jita kashe. Hakan ya saka ya kira ta kanwarta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta yi picking.

“Hello Raliya ya kike?”

“Lafiya Kalau Ya Faruq”

“Yayarki ta zo?”

“Aa, tana Kano fa”

“Kano?”

Ya maimaita cikin tsananin mamaki.

“Eh Napep ta hau shi ne…”

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraren abun da Raliya ta fada masa, sannan ya sauke wayar yana jin babu dadi. Ya sani ba dan komai Baturiya take masa haka ba sai dan talauci, da yana da arziki da bata isa ya mata umarni ta saba ba, daman ai ta fada idan yana da kudi ba zata taba gujewa umarninsa ba, tabbas da yana da arziki da iyayenta sun nemi inda yake sun fada masa halin da matarsa take ciki, sai dai ba su yi hakan ba saboda ba kowa ba ne a idonsu, wannan dalilin ya saka a duk lokacin da ya kai kararta akan abun da take masa sai du bata gaskiya su goyi bayanta. Cire line yayi ya ya mika masa wayar ya juyo ya dawo cikin gida cikin yanayi na rashin dadi ya maida gidan ya rufe.

BATURIYA POV.

Washe gari mutanen gidan suka bata wani tsohon Hijab ta saka ta talkami, Bayan ta karya suka rakota har bakin titi suka tara mata Napep zuwa tashar mota. Su suka biya mata na napep din, tana ta musu godiya, idonta har yanzu be warware daga kukan da tasha ba, babu abun da take ji kamar wayarta, domin samun wata wayar a gareta yanzu abu ne mai matukar wahala a halin da suke ciki, har kara ma a gidansu wata kila mahaifiyarta zata iya taimaka mata da wani abu, yayanta ya cika mata sauran ta siye wata wayar, amman ba daga bangaren Faruq ba kam.
Tun daga yanayin hausarta suka gane yar zamfara, abun ka da kanawa sai dariya suke mata ita kam bata ma bi ta kansu ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta data bata yadda zata samu wata wayar kawai take tunani, gashi hanyar samun kudinta ta facebook ne inda take yaudarar maza, yanzu kuma babu wayar yaudara ma.

“Kai Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Ta furta wasu hawayen na cika mata ido.

‘Dan Allah aljanuna idan kuna jina ku taimaka min da wayata ku dauki kudin na bar muku’

Wannan karon a cikin zuciyarta tai maganar hawaye na sauko mata.

“Malama Lafiya dai?”

Wani matashin saurayi dake kusa da ita ya tambaya yana kallonta. Banza tai masa ta ta juya masa fuska, sai yai murmushi ya cigaba da danna wayarsa. Sai da motar ta cika sannan suka kama hanyar Zamfara suna tafe suna addu’a saboda yanayin hanyoyin nigeria kowa ya san yadda tafiya take a yanzu. Sai da tafiya tai nisa sannan aka kira saurayin a waya, Baturiya ta kashe kunne tana sauraren yadda yake amsa wayar a cikin har da amsar da yake fadawa cewar motar haya ya shigo saboda motarsa ta tsaya ya barta a nan Kano.
Baturiya na jin haka sai ta juya ta kalleshi sai a lokacin ma ta lura da shaddar jikinsa babbar shadda ce, haka zalika wayarsa ma.
Tun da suka kama hanyar direban be tsaya ba har suka iso Zamfara.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Baturiya ta fada da muryar kasa kasa tana fashewa da sabon kuka. A nan ma kallonta yai ya tambayeta.

“Lafiya…?”

Kai ta girgiza ta share hawayenta ta fada masa abun da ya faru da ita, sai dai ta canja cewar tana da aure, sai ta fada masa cewar mahaifitarta ta aiketa.

“Subhanallahi, ki gode Allah ma be kai ki wata kasar ba”

“Haka yan gidanmu suka ce, ni daman Allah ya sani gidanmu bama hawan Napep duk inda zamu je a mota ake kai mu yanzu ma tsautsayi ne”

Ta fada kamar gaske, kallon lace din dake jikinta yai kamin ya kalli kyakkyawar fuskarta.

“Allah ya tsare gaba”

“Amin”

“Amman miyasa kike kuka?”

“Haba Malam dubi tufafin dake jikina fa? Ban taba kwana a irin gidan dana kwana ba sai jiya, yanzu kuma motar haya na biyo tun daga Kano har Zamfara abun da ban saba ba”

“Ba dadi gaskiya, ni ma ban saba hawan motar haya ba sai dolen dole”

“Ba dadi ai”

“Gaskiya”

Daga haka be sake cewa komai ba sai da suka isa cikin tasha. Bayan sun fito ta jero ita da shi suka fito titi, fitowarsa tai daidai da fakawar wata bakar mota mai kyau har wani sheki take tsabar sabuntaka.

“If ba wani matsala zan iya sauke ki a gida ai”

“Aiko da naji dadi Wallahi domin tsoron Napep nake yanzu.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button