BAKAR WASIKA 10

Murmushi yai ya bude mata baya ta shiga, shi kuma ta bude front seat ya shiga ya zauna.
“Ku gaisa da abokina”
Ya fada yana juyowa ya kalleta.
“Sannu ya aiki”
“Alhamdulillah ya hanya”
“Da godiya”
Ta amsa sai ta maida dubanta gefen titi tana kallon motocin dake kai kawo.
“Wace unguwa ma?”
“Gada biyu”
Ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, ko kadan tsoro be kamata ba balle ta ji faduwar gaba, ta saba shiga motar maza duk kuwa da kasancewar tana da aure, sai dai bata barin wanda ya santa ya ganta, wannan karon ma bata haufin ganinta ne saboda ta san yayanta ya san labarin bata tan idan ya ganta da wani ba zai mata fada ba.
Har kofar gidan yayanta suka sauketa, kato gidan mai kyaun gaske, sai da tai musu godiya sannan ta bude motar zata fita.
“Ga katina maybe zamu iya gaisawa”
“Okay thank”
Ta fada tana karbar katin sannan ta fice ta maida motar ta rufe sannan ta tura gidan ta shiga.
“Ina ka hadu da wannan?”
“Ta sha kuma ta min”
Ya fada yana murmushi.
“Tana da kyau gaskiya”
Dukansu dariya sukai sannan abokin nasa yaja mota suka juya.
LEILA POV.
Tsaye take jikin windo tana kallon garden din dake cike da itatuwa, fuskarta dauke da hawaye, haka ma zuciyarta babu dadi ga rashin natsuwa da samun sukuni da take.
Hannu ta saka ta share hawayenta tana jin wani irin nadama da bakincikin abun da ta aikata.
“Why? Sometimes I’m very selfish”
Ya fada tana kai hannunta ta shafa wuyanta, bakinta ta cika ma iska ta busar sannan ta juyo ta baro jikin window ya nufi kofar fita har yanzu jin take babu dadi, tsaye tai tana kallon bakin kofar dakin a daidai inda Baaba ta tsaya sannan ta dauke kai ta fara tafiya, sai da ta leka dakin Momy ganin bata ciki yasa ta sauko kasa gaba daya sai ta same ta zaune akan sofa tana amsa waya. Wucewa tai dinning taja kujerarta ta zauna tana ta kallon abincin dake gabanta kamar mai wani nazarin.
“Leila…”
Momy ta kira sunanta bayan ta gama wayar, sai Leila ta juyo ta kalleta da idanuwanta dake nuna alamar bata samu bachi da yawa ba. Tasowa Momy tai tana karantar damuwar yarta, a take ta nemi bacin ran dake tare da ita ta rasa, hannu ta kai ta rika fuskar Leila.
“Dear ba ki bachi ba?”
“Wallahi Momy na kasa bachi kamar yadda na saba, Wallahi dana rufe ido matar nan nake gani”
Momy taja kujera ta matsa kusa da yarta sosai ta zauna.
“Leila ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, babu wanda zai san wannan abun even if ma sun sani ba su isa su yi komai ba, they’re poor ba su isa su ja da mu ba, kuma wannan abun ai kaddara ce, ki dauka haka Allah ya rubuta”
Ta gyada kai cike da gamsuwa. Sai Momy tai mata murmushi ta share mata hawayenta.
“Ko kadan bana son na ganku a damuwa, ku kenan uku Allah ya bani bana son kuna samun kanku a damuwa, wannan matsalar ma ta Talba zata wuce inshallah sai ya sauke duk girman kan nan”
“Anya Momy Talba zai ce?”
“Dole ya canja, sometime lamarinsa har daure min kai yake, yanzu maganar nan ta Baaba har ya kai ta gurin mahaifinki, simple abu Talba ya rika yinsa kamar wani mace ko karamin yaro, gashi na je Mahaifinku yace ba zai sake biyan mai aiki ba”
“Ba zai rika dafa abinci kenan?”
“Dole a aljihu zan rika biyansu, ai na yi magana da Hajiya Samira ta nemo min wasu yan aikin, a dole mu dauki wasu amman da ni zan biya su”
“Ban san miyasa Talba ya fita dabam a gidan nan ba, ni na rasa gane wane irin mutum ne”
“Shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki, domin bana son ya fara zarginki, ni kam ba dan kin matsa kina son Talba ba….”
Kamin Momy ta karasa Leila tai saurin tare numfashinta tana rike hannunta.
“Wallahi Momy ina son Talba, ina mugun sonsa, Wallahi idan ba shi ba ba zan iya auren kowa ba”
“Shikenan ai ba zamu bari ya dauko mana bare ba, amman halin nan nasa ina ganin kamar zaki wahala idan akai auren nan”
“Momy ba zan aure shi ba sai ya canja, zan canja shi inshallah na san yana son mu yi aure ai zan yi amfani da wannan damar na canjan shi”
“Allah yasa yanzu dai sai ki karya”
Ta daga mata kai ta kai hannu zata fara bude kular akai knocking, kusan a tare ita da Momy suka kalli kofar falon sai dai ta riga Momy mikewa tsaye ta karasa gurin kofar ta bude.
“Madina…”
Suka sakarwa juna murmushi, sai kuma Madina ta juya tana kallon Talba dake kokarin shiga mota, kamin ta juyo ta kalli Leila.
“Fita zai yi?”
“I think”
“Kamar ya you think zai fita baki sani ba”
“Kina abu ke ma kamar baki san Talba ba”
“Ke ce ya kamata ki canja ba shi ba”
Madina ta fada tana sake juyawa ta kalli motarsa, ajiyar zuciya ta sauke a sirance sannan ta shiga cikin falon gabanta na mugun faduwa, irin faduwar gaban da take yawan samun kanta a ciki a duk lokacin da tai arba da Talba.
Alhamdulillah a nan na kawo karshen free page duk page din da zai biyo bayan wannan na kudi ne.