BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 11

“Yanzu kika iso ne? Na dauka gida zaki wuce ai”

“Ko naje gida me zan yi tun da ba abinci ke akwai ba, yunwa kawai zan sha”

Juyowa yai da kyau ya fuskance ta.

“Rafi’a wannan wane irin magana ce? Idan ma kasa kike ci naga ai gidan aurenki ne”

“To karya na fada? Ni yanzu ga shi na rasa waya da sauran canjina”

“Rashin jinki ne yaja miki ai”

“Kaji ba bakar fata kawai yake min, shiyasa ai baka ma damu ka san inda nake ba sai yanzu”

Uffan be sake cewa ba ya kama hannun dansa yana wasa da shi.

“Ya kira ni ai ya tambaye ni”

cewar Raliya kanwar Baturiya. Sai mahaifiyarsu ta tashi ta nufi dakinta tana fadin.

“Allah ya kyauta”

Bayan ta wuce, Faruq ya kalli Baturiya.

“Tashi muje gida”

“Yanzu yanzu fa na shigo, sai na huta zan tafi gida”

Ta fada tana turo baki gaba tana hararsa kasa kasa.

“Rafi’a me ke damunki, sai ki rika min abu kamar ba mijiki ba, danki ne ni?”

“To idan naje gidan me zan maka? Yanzu fa na dawo ai sai ka bar ni sai na huta sannan anjima zan koma ai ban ce nan zan zauna ba”

Sanin cewar idan ya biye mata za su siyar da hali ne a gidan da ba a ganin mutunsa da kimarsa ne yasa be sake ce mata komai ba ya saki hannun Sultan ya mike tsaye.

“Raliya ki fadawa Umma na wuce”

“Okay”

Raliya ta amsa tana kallon Baturiya cike da jin haushin abun da yar’uwarta take yi a gabanta. Sai da ya fice sannan ta kalli Baturiya ta ce.

“Wallahi Rafi’a baki kyautawa, talauci ba fa ba hauka ba ne, baki san budin da Allah zai masa nan gaba ba”

Baturiya taja wani shegen tsaki.

“Ki dauki arziki ki ba shi, idan mun zauna mu kadai kin san iya abun da yake min ne? Kin san yadda yunwa take halaka mutum kuwa? Dan Allah karki kara min da wata damuwar ki bar ni na ji da wanda nake ciki”

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta nufi dakin mahaifiyarta, Sultan ya bi bayanta.

Family house dinsu ya nufa cikin rashin jindadi, daman ta saba masa a gaban yan uwanta, yan’uwansa kam daman sun san irin zaman da suke, hakan yasa kanensa basa sha’awar zuwa gidan sai da wani babban dalili, domin bata musu tarbar arziki.
Mai achaba na sauke shi kofar gidan ya ciro kudinsa ya mika masa sannan yai sallama ya shiga cikin gidan, tun daga yanayin yadda ya ga gidan ya san ba su girka komai ba, domin murhunsu a bushe yake, a take ya ji ransa ya kara baci domin baya son ganin mahaifiyarsa a hali na yunwa, ga kuma damuwar halin da suke ciki na neman kudin aure. Da sallama ya shiga cikin dakin kanwarsa Aisha ta amsa ciki yanayi na damuwa. A bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon mahaifiyarsa dake lullube da wani tsohon zanen gado tana ta rawar sanyi.

“Jikin ne?”

Ya tambaya da muryar dake bayyana tsananin damuwarsa.

“Haka ta kwana”

Aisha ta amsa.

“Miyasa ba a kira ni ba?”

“Ita ce kar a kiraka kar a tayar maka da hankali”

Runtse ido yai ya sauke ajiyar zuciya, ya dade a haka kamin ya bude idon ya nufi inda mahaifiyarsa take kwance ya zauna daf da ita, sai ta yaye mayafinta ta kalleshi da idanuwanta dake fassara irin tsananin zazzabin da take.

“Faruq”

“Mama damuwar nan ce kika dauka kika saka a ranki ko? Allah shi yake yin komai, kuma daman na yi tunani zamu hutar ta da kanmu da wani lefe ya bada kudin kawai a siya mata kayan daki da su”

“Ko ya bada kudin ai ba zai wuce 100k ba kuma ba zai isa a siye kayan daki ba, ko kujeru kanana yanzu sai an siye su 60k ko fiye ma”

“To ai sai a kara da wani abun idan Allah ya mana fatahi, dan Allah ki cire damuwa a ranki, Mama so kike ke ma mu rasa ki? Haba Mama”

“Damuwa dole ce Faruk bayan ta auren yaran nan akwai ta yau da kullum, yanzu ga shi abun da zamu karya ma ya gagaremu sai da na ba Asiya ta siyar da tufafina sannan zamu samu su karya, tun safe har la’asar ace bawa bai saka komai a bakinsa ba”

“Allah be manta da mu ba Mama, bayan wuya sai dadi, kuma idan ka ga tsanani yayi yawa sauki na tafe, Inshallah komai zai warware kamar ba a taba yi ba”

“Allah yasa muna da rabon jindadi ko kadan ne Faruq, lokaci tafiya yake baya jiran kowa”

Ta karasa tana runtse ido da karfi sakamakon bugawar da zuciyarta tai da karfi. Daga Aisha har Faruq hankalinsu tashi yai.

“Sannu Mama”

Kai ta daga musu cike da karfin hali har lokacin idonta na rufe saboda azabar ciwon da take ji. Ajiyar zuciya Faruq ya sauke ya mike tsaye ya bar dakin cikin damuwa, ji yake kamar ace yana da halin da zai magance damuwar mahaifiyarsa, kuma ya kaita asibiti a duba lafiyarta, amman ina? Talauci ya saka shi a gaba kamar wanda ya zagi arziki.

LEILA POV.

Rike da takardun Madina ta shiga dakin Momy ta zauna gefen gadonta.

“Momy Could you do me a favour?”

Momy ta aje plate din abincin dake hannunta ta kalli Leila dake sanye da doguwar rigar shadda ta sha aiki kamar sabuwar amarya.

“Minene?”

“Kin san kawata Madina ai…”

“Har sai kin sake gabatar min da ita? Madina ai ta zama yar gida”

“No Momy ina son ki gane cewar maganar da zan miki tana da muhimmanci ne, Wallahi ta min magana tana son aiki a kamfanin Daddy and i promise her zan saka a dauke ta”

“And….?”

Momy ta bukata tana tsattsage hakoranta na makka.

“So daman dazun na mata magana ta kawo takardunta shi ne ta kawo, da na zo naje na samu Daddy kai tsaye da maganar amman na san zai ce na bawa Talba ne, Talba kuma zai iya cewa ba zai dauke ta ba, kuma kin san be kamata na kasa yi mata haka ba, ko da ba ita ba ma a kamfanin mahaifina ya kamata ace zan iya yin komai ina da ikon yin komai”

Momy ta yi dariya.

“Leila kenan, kina abu kamar ke ce Amal, idan za a dauki wani aiki ta dalilinki har sai kin tsaya wani kame kame? Ki same yayanki Talba da maganar mana”

“No Momy ni fa bana son magana da shi sai idan wani babban abu ne, yadda yake jin kansa haka nakr jin kaina, kuma kin san zai iya amfani da wannan damar ya wulakanta ni ko ya fada min wata maganar marar dadi, idan kuma na rama ke da Daddy ni zamu dorawa laifi”

“Wannan ai da ne Leila, amman yanzu na fahimci halin da kike ciki, halin Talba sai mai hakuri da kai zuciya nesa ni kaina yanzu ya fara min ai”

“Shiyasa nake son ki saka shi ya dauke ta… ”

Tana rufe baki Talba ya kwankwasa kofar dakin sannan ya murda kofar ya turo ya shigo, juyowa tai ta kalleshi, a take annurin dake fuskarsa ya auri idanuwanta, duk yadda ta so ta dauke kai daga barin kallonsa sai ta kasa har ya karaso inda Momy take ya zauna a saman kujera, lumshe ido tai tana ta yaki da numfashinta dake ta kokarin sauya mata kamshin dakin Momy zuwa na turaren Talba da ya cika daki.

“Momy barka da dare”

“Yauwa”

Yanayin yadda Momy ta amsa masa ne yasa shi murmushi domin ya san har yanzu bata gama hucewa daga laifin da be aikata mata ba.

“Allah yasa dai ba fushi kike da ni ba har yanzu Momy?”

Uffan Momy bata ce masa ba, hakan ya saka shi kara yin Murmushi sai dai wannan karon be ce komai ba.

“Abun da kake dai ba abu ne mai kyau ba, mata aka sani da tsegumi ba maza ba”

“To ayi min afuwa ba zan sake ba, Leila…”

Ya karasa yana kiran sunanta, sai ta bude idonta a hankali ta kalleshi ba tare da ta amsa ba, daman shi ma he called her name ne kar Momy tace ta ganta be mata magana ba, duk kuwa da kasancewar ita ya kamata ta fara masa magana a lokacin daya shigo a matsayinta na kanwarsa kuma wacce zai aura, ko ba komai ai ita ce karama.
Mikewa yai tsaye sai Momy ta dauki takardun da Leila ta aje mata gefenta ta mikawa Talba. Sai da ya kalli takardun sannan ya mika hannu ya karba ya bude yana dubawa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button