BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 11

“Ba mu fara daukar ma’aikata ba, muna da enough”

Ya fada bayan ya dauke idonsa daga fararen takardun zuwa ga Momy.

“Na sani, saka iya replacement dinta da wani ai”

“Na dauka Madina tana aiki da ma’aikatar Alhazai ai”

“Tana yi, yanzu nan take so kuma umarni ne so nake ka dauke ta”

Ya hade yawun bakinsa, sannan ya kalli Leila da ita ma kallonsa take ya rufe takardun ya juya ba tare daya sake cewa komai ba ya fice, binsa Leila tai da kallo har ya fice sannan ta juyo ta kalli Momy.

“Thank Youu Momy”

“Karki damu, je ki samu abun da kika sakawa cikinki”

“Okay”

Ta mike tsaye ta fice daga dakin cikin jindadi. Ko da Talba ya fito Kabir na zaune kan center carpet tare da Amal suna shan kankana. Saman kofa Talba ya zauna rike da takardun yana kallon plasma.

“Malam bismilla karka ce mun maka rowa”

Kabir ya fada yana kallonshi, Talba kallonsa kawai yai ya dauke kai fuska ba yabo babu fallasa. Amal ta kalli Kabir sannan ya kalli Talba ta ce

“Ya Talba Momy ta maka fada dazun?”

Gira ya daga mata, wanda hakan yai daidai da saukowa Leila sai ya mike tsaye ya fice daga falon gaba daya.

“Strangers, ban taba ganin masoya irinku ba, wai a haka zaku yi aure?”

“Miye damuwarka ne Kabir? As long as yana so na miye ruwanka ne?”

Yayi dariya ya mikawa Amal hannu suka taba.

“Hi five Baby”

Dinning ta nufa ta bude manyan kulolin tana duba abun da Momy ta dafa, wayar dake hannunta ta aje a gefe ta dauki karamin plate ta dauka ta fara zubawa, abun ka da wanda baya son cin abinci sai ta zuba kadan ta ja kujera ta zauna. Kamar zaman ake jira tai sai ga sako ya shigo wayarta.

‘Good Night Dear’

Wani irin kasaitaccen murmushi tai bayan ta gama karanta sakon dake dauke da hoton zuciya.

“I love you”

Ta furta a zahiri, sannan ta aje wayar ta juya ta kalli Kabir dake ta rigima da Amal akan waye zai karasa shanye watermelon din da suka raga mai tawa, sai kuma ta juyo ta kalli abinci.

“Talba kana da wuyar sha’ani, wannan girman kan naka yana bani mamaki, ban taba ganin mai tsoro ko jin nakasu akan nuna soyayya ba kamar kai… But i love you..”

Ta furta tana kara jin shaukin kaunarsa na ratsa zuciyarta.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button