BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 12

Kamin ya sake cewa wani abu ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta dauko wayarta ta mika masa.

“Saka masa number a nan”

Be karbi wayar ba, ya ciro tasa wayar ya karanta mata number ta saka a wayarta.

“Idan ya zo zan fada masa sai na ba shi number”

“To yayi na gode”

Ta rufe gidan tana murmushi ta dawo falonta tana kokarin saving din number.

“Ba Alhaji Sule kake ba ko Alhaji lule kake sai na ci ubanka, talauci ya matsa shi ne kai kuma zaka kunno mana wata wutar dan kana da shegen tsohon gida”

Ta fada tana ƙwafa.

FARUQ POV.

Ya lalaba aljihunsa ya ciro naira 100 da ta rage masa ya mikawa Aisha.

“Je ki siyo koko ku sha”

Aisha ta saka hannu biyu ta karba.

“Yaya Wallahi ko jiya Mama ba tai bachi ba, yanzu ma jikinta zafi yake”

Ajiyar zuciya ya sauke.

“Jarabawa ce, ga rashin kudi, ga rashin mata ta gari, ga rashin lafiya Alhamdulillah”

Ya fada yana kallon mahaifiyarsa dake lullube bata ma san ya zo ba, karasa yai kusa da ita ya yaye mayafin data lulluba da shi ya taba jikinta sai ya ji shi da zafi sosai.
Mikewa yai tsaye ya fito daga dakin cikin wani irin yanayi na rashin jindadi. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya rike a hannu yana kallo, ya san ko siyar da ita yai kudin ba zai isa ya kai Mama asibiti ba, jinginar daya bada ma daker ya samu ya biya mutumen ya karbo wayar. Bakin kofar dakin ya zauna ya dafe kansa, yana mamakin lamarinsa wani lokacin shi kansa abubuwa suna daure masa kai, ga karatu yayi kuma ya fito da kwali mai kyau amman aiki ya gagareshi, wadanda sukai karatu tare wasu duk sun samu aiki har sun bar kasa, wasu kuma suna Abuja wasu a manyan mukana gobnati wasu a manyan bankuna da kamfani amman shi ya kare a shagon Barber, shi ma daker ya samu wani kawunsa ya bude masa shagon.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Allah ka kawo mana sauki”

Ya furta yana dago kansa ya shiga contact dinsa ya nemo number abokinsa kuma amininsa Nura.
Wayar bata dade tana ringing Nura ya dauka.

“Hello Faruq”

“Na’am Nura ya gida?”

“Lafiya kalau kwana da yawa”

“Sai godiya, ina su Sakina”

“Lafiya kalau”

“Wallahi Nura ina cikin matsala”

“Subhanallahi miya faru?”

“Abubuwa da yawa, yanzu dai wanda ya fi damuna rashin lafiyar mahaifiyata, kudi nake so rance idan zan samu na kaita asibiti”

“Kash…. Wallahi Faruq yau da 500 na tashi na basu su karya, ka san abu ga ma’aikaci idan ba albashi akai ba, ba mu da kudi, kuma gashi albashin na jihar zamfara sai a hankali anki a gyara mana, ga kayan masarufi sai tashi suke, abun da zaka siya da 20k yanzu sai 40k shiyasa albashin baya mana auki”

“Haka ne, Allah ya sauwake”

“Ameen, amman da zaka iya da kaje gidan Alhaji Mu’azu Shimkafa ance suna da Foundation na taimakon marayu da mabukata, amman idan baka jin kunya kasan wasu basa son zuwa irin abu na neman taimako”

“Haba Nura ina zancen kunya ga mai nema, suna nuna mutun a tv ne?”

“No babu ma wanda zai san an maka, amman ance Dattijon yana taimako sosai gaskiya, ban san yadda ake bi ba, amman dai idan kaje can gidansa ba rasa taimakon da zai maka ba, har aurarwa suna yi ga marayu su masu komai”

“Ai ban sani ba, ina dai jin ana fadarsa Tsohon Minister kudi ko? Ban san yana taimakom nan ba Wallahi, amman zan je yanzu Inshallah na gode sosai”

“Allah yasa a dace, ya bata lafiya anjima zan shigo na dubata Inshallah”

“Okay”

Ya dauke wayar daga kunnesa ya mike tsaye da sauri sai a lokacin ya tuna da be tambayi unguwar da yake ba. Hakan yasa ya sake kiran number Nura.

“Baka fada min sunan unguwar ba?”

“Shimkafi Road, kana shiga unguwar kace gidan Alhaji Mu’azu Shimkafi kake nema, za a nuna maka”

“Okay”

Ya saka wayar aljihu be ma koma cikin gidan ba ya nufi titi, da kafa ya taka tun daga gadar gaba har unguwar Shimkafi road, akwai tazara amman a haka yai ta cin kasa saboda babu ko naira aljihunsa.
Kamin ya karasa shiga cikin Quarters din wayarsa tai ringing, yana ciro wayar ya duba, a take gabansa ya fadi ganin number Malam Musa Dillali, hakan nan dai ya daure ya dauka.

“Hello”

“Hello Faruku haka ake daga karbar number sai ka ba matarka ta ciwa mutun mutunci?”

Tsaya yai daga tafiyar da yake fuskarsa da mamaki.

“Wane mutum kuma?”

A nan Malam Musa ya fada masa yadda sukai da Baturiya dazun sannan ya dora da abun da mai gidan ya fada masa.

“Wata kila kiransa tai ta ci masa mutunci, yanzu ya kira ni yana ta masifa wai wata ta kira shi Baturiya ta zage shi, ya baku daga yau zuwa gobe ku tashi ku bar masa gidansa”

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Wallahi Malam ban san Matata zata yi haka ba, kuma Wallahi ban ce zan karbi number sa ba”

“To yanzu dai sai ku san abun ba, Baturiya ko balaraba ta ja maka”

Malam Musa na fadin haka ya kashe wayar, Faruq ya dafe kansa.

“Na shiga uku wai me ke damun Rafi’a ne? Ta sake janyo mana wata fitinar kuma? Ina ruwanta da mai gida?”

Wani irin kololon bakinciki ne ya taso masa, sai ya ji kamar na runtse ido ya bude a gansa a kabari ya huta, yana fama da wasu matsalolin yanzu kuma ta ballo masa wani.

“Wallahi yau sai na miki mugun duka, Rafi’a sai kin dawo hayyacinki in ma baki da hankali sai kin yi shi”

Ya fada rai a bace, duk abun da take masa na bacin rai bata taba mata masa rai irin wannan ba, domin be san inda zai je ba idan ya bar gidan haka nan ya cigaba da tafiya ransa a bace. Da tambaya ya aka nuna masa kofar gidan Alhaji Mu’azu Shimkafi, Gate din gidan kadai a abun kallo ne, balle kuma farar ginar da aka kawata da farin fenti ga shuke shuke itatuwa da fulayoyi, idan ka daga kanka kuma sai ka hango gidan sama daga can cikin gidan an kawata ko’ina da gilasai komai a tsare kamar ba za a mutu ba. Faruq ya girgiza kai.

“Allah man yasha’u, ka baiwa bawa ba dan kana son shi ba, kuma ka hana Bawa ba dan baka son shi ba, Allah ka bamu na mu arzikin na halal, yanzu nan gidan mutum daya ne”

Ya fa da yana mamakin tarin dukiyar dake gidan. Karasa yai bakin gate din yana kallon security cameras daka laka hagu da dama na gidan sannan ya kwankwansa kofar gate din. Ba dade wani police ya bude masa yana sanye da uniform dinsa.

“Malam Lafiya?”

Faruq ya mika masa hannu suka gaisa cikin mutumci.

“Dan Allaj ina son ganin mai gidan ne matsala ce da ni”

“To ganin mai gidan a yanzu ai, sai an jira domin be fito ba, idan zaka iya jira a nan wajen idan ya fito sai ka tare shi da matsalarka, duk dai baya son a ana mishi haka amman karka nuna masa na san da zuwan ka”

“Ba Matsala na gode sosai”

Faruq ya nemi wani gurin ya zauna a nan kusa da gate din, shi kuma police din ya koma cikin gidan ya maida gate din ya rufe. Be yi minti talatin da zama ba, aka sake bude gate din sai dai wannan karon gate din gaba daya aka bude ganin mota zata fito yasa yai saurin mikewa tsaye a zatonsa mai gidan ne sai ya nufi motar da sauri, ganin ya nufota yasa ta tsaya ta sauke gilashin motar tana kallonsa.

“Ya akai?”

“Daman na dauka mai gidan ne shi nake son gani”

“Saboda me kake son ganinsa?”

Ya tambaya tana kare masa kallon from head to toe.

“Taimako nake nema”

Hannu ta saka ta cire katon gilashin idonta.

“Okay idan ana neman taimako sai azo har kofar gidan mutum a takura masa? Baka san yadda zaka bi ta Foundation ba? Ba ma taimako a gida sai ta karkashin kungiya, kaje can ka samu kungiya karka sake zuwa nan, Talauci ba hauka ba ne”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button