BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 12

“Haka ma Arziki ba hauka ba ne malama, karki nemi fada min maganar banza saboda na zo nema a gidanku, ni ba wulakantaccen ba ne”

“Really”

Ta bude motar ta fito tana masa wani banzan kallo.

“Dubi ka! Ka zo nema a gidanmu kuma kana cewa kai na wulakantacce ba ne? To waye kai? Kai kama isa ka zo nema a gidanmu kuma fada min maganar banza?”

“Maganar banza ana furtata ne a lokacin banza kuma ga mutanen banza irinki”

“Ni…”

Ta nuna kanta Faruq ya daga mata kai cikin bacin rai daman be gama wankewa daga na matarsa ba ita kuma tana neman kara masa wani, hannu ta daga zata mare shi sai ya rike hannun da mugun karfi ya jefar da shi.

“Kika kuskura kai hannunki a fuskata sai na illataki, dan ina neman taimakonku ba shi zai baku damar wulakanta ni ba”

Bata sake ce masa komai ba ta juya da sauri ta isa gurin gate din ta buga da karfi, daman Police din ya rufe gate din a lokacin daya bude mata ta fita, da sauri ya bude sai ta nuna masa Faruq.

“Ku rike mutumen can”

Da sauri ya fito shi da wasu Police din biyu suka nufi inda Faruq yake tsaye suka rike shi, ita kuma ta nufi cikin gidan da saurinta kamar zata tashi sama, Talba dake kokarin tashin motarsa yana kallonta ta danna door bell din kofar be kula ta ba ya ja motarsa zuwa gate ya hanna horn, dai dayan Police din ya dawo ya bude masa gate din ganin suna rike da Faruq ga kuma motar Leila dake bude a kunne yasa shi tsaya ya sauke gilashin motarsa.

“Lafiya?”

“Wallahi ba mu san abun da ya faru ba, Hajiya Leila ce tace a rike shi”

Talba ya kalli Faruq daga sama har kasa, be masa kama da yan ta’addaba, kuma ya san halin yar’uwarsa mafi akasari fadan da take da mutane ita ce bata da gaskiya. Hakan yasa shi tambayar Faruq dake kokarin fisge kansa daga rikon da Police din suke masa.

“Malam Lafiya?”

“Lafiya ce zata saka Police rike ni? Daman idan za ku taimaki mutum sai kun wulakanta shi”

Faruq ya fada cikin fusata, hakan yasa Talba ya bude motar ya fito ya nufo inda suke tsaye.

“Ku sake shi”

Ya fadawa Police din sai suka saki Faruq, Talba ya saka hannayensa aljihu yana kallon Faruq.

“Bari na fada maka wani abu, ba a min tsawa kuma ba a fada min bakar magana, amman na maka uzuri saboda na fahimci kana cikin bukatar taimako ne, and bana son na yi ma mutun wani abun ta dalilin taimako, da ace a hanya na hadu da kai da zan iya maka cin mutunci fiye da kima, now tell me miya faru”

Kalaman da Talba yai yasa Faruq sasautawa zuciyarsa domin ya fahimci ba fada Talba yake son yi da shi ba, idan ma sun yi fadan ba riba zai ci ba.
Cikin bacin rai Faruq ya fadawa Talba abun da ya faru, sai Talba ya girgiza kai ya lumshe ido ya bude, ba dan baya iya bawa kowa hakuri ba, da sai ya bawa Faruq, domin ya fahimci halin da
yake ciki.

“Ka manta da abun da tai maka yanzu fada min wani iri taimako kake so?”

“Mahaifiyata ce ba lafiya”

Faruq ya fada domin yana jin cewar shi ne kawai abun da zai iya fada a halin yanzu, kasancewar shi ya fi damunsa. Talba ya juya ya koma cikin motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna, wani karamin diary ya dauko yai rubutu akai, sannan ya bude wani guri a cikin motar ya dauko 100k ya fito ya nufo Faruq.

“Ga wannan Allah ya bata lafiya, and idan kana neman taimako a foundation din Mahaifina ka tuntubi wannan number, su za su tantance komai su sanar mana”

Ya mika masa number bayan ya bashi kudin. Faruq ya saka hannu biyu ya karba cikin jindadi.

“Na gode sosai Allah ya saka da alheri, ya kara sutura”

Uffan Talba be ce masa ba balle har ya amsa da Ameen, sai juyawa yai ya nufi motarsa, yana kokarin shiga yaji dayan police din na fadin.

“Hajiya tace a rike shi, ku rike shi”

Juyowa Talba yai ya kalli Police din, sai suka fasa rikon Faruq.

“Hajiya Babba ba Leila ba ita ta kira ni yanzu”

Da kai Talba yai ma Faruq alama daya wuce sannan ya shiga motarsa ya danna horn suka sake bude masa gate din yai ribas ya shiga cikin gidan. A harabar Entrance din ya faka motarsa sannan ya fito ya nufi kofar falon kamin ya karasa sabuwar mai aikin Momy ta bude kofar da sauri da alama fitowa za ta yi.

“Yauwa ranka ya dade Hajiya tace na kira ka”

Shiga yai cikin falon hannayensa zube a aljihu sai kamshi turare yake zubawa, tsaye ya samu Momy Leila na gefenta dayan mai aikin Momy Zulai tana tsaye nesa da su, domin wannan karon har masu aiki biyu Momy ta dauka. Yana kallonta ya san ranta a bace yake, can kuma ya kalli Leila da ke hawaye, kamin ya kalli Kabir dake zaune rike da waya yana kallonsa.

“Talba haka zamu zauna mutane suna ci mata mutunci kana daukar side dinsu”

“Ta fada miki Abun da tai masa?”

“I don’t care, amman komai tai masa ai be kamata ya rike hannunta ba, har ya fada mata bakar magana alhalin shi yanzo nema a gidansu, har kuma ka bar shi ya tafi”

Talba be ce komai ba, har Mairo ta shigo tare da police din da Momy tasa ta kira daman shi da Talba ta ce ta kira. Yana shigowa Momy ta nuna shi da yatsa.

“Wannan ya zama na karshe da wani zai zo ya takura mana kofar gida, karka sake barin kowa ya shigo mana ba tare da saninmu ba, idan makamancin haka ya sake faruwa a bakin aikinka, ba wai a gidan nan kadai ba, no ka daina saka Police Uniform kenan har a bada mark my words”

“Ayi hakuri ranki ya dade Inshallah zan kiyaye”

Cewar police din sannan ya juya ya fita. Da ido Talba yai ma Mairo da Zulai alamar su fice daga falon sai suka fice da saurinsu.

“Wannan abun yayi yawa Momy, ya kike Leila ta zama? Ba fa Amal bace, taya Leila zata raini yara masu tarbiya idan tana wannan halayyar? Saboda wani ya zo nema daga abun da Allah ya wadata mu da shi sai ya zama abun wulakantawa? And ji yadda kike fadawa Police din nan magana kamar wanda yai wani babban laifi”

“To ya kake son na yi? Haka zamu yi ta zama Leila bata da yanci a gidan nan? Haka zaka rika mata idan kun yi aure ka bar ko wane kare da biri suna cin zarafinta? Shi ne jindadinka?”

Talba ya kalli Leila cikin yanayi na rashin jindadi.

“I wonder what kind of woman zan aura! Akwai karamci tarbiya a tare da ke, ba zan iya daukar wannan halin na ki ba kina bukatar ki canja rayuwa Leila…”

“Kai kake bukatar canja rayuwa ba ni ba…”

Ta fada mishi kai tsaye sannan ta nufi upstairs. Momy ta kara da nata.

“Kana fada min Leila bata da tarbiya ko? An maka dole ka aureta ne? Ko kuma kana son ci min fuska ne Saboda ba ni na haife ka ba?”

Talba ya kalleta da sauri, Kabir ma mikewa yai tsaye sai a lokacin ya saka bakinsa a maganar.

“No haba Momy… ”

Momy ta daga masa hannu.

“Na san abun da yake nufi, duk abun da kake kana yi ne saboda ba ni na haife ka, kuma na sani, daman tsintacciyar mage bata taba zama mage ba, amman karka manta ni na raine ka, ko da ka bude ido baka san mahaifiyarka ba ni ka sani, na raine kamar uwa, so weather you like it or not I’m still your mother, karka manta da wannan…!”

Tana kaiwa nan ta nufi upstairs ya bita da kallo kalamanta na ratsa kowane lungu da sako na zuciyarsa. Leila ma da bata karasa hayewa ba juyowa tai ta kalleshi cikin yanayin da ke nuna bata jidadin kalaman Momy ba, balle kuma Kabir da ya tsaya kamar hoto yana kallon dan’uwansa cikin yanayi na rashin jindadi.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button