BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 13

Juyawa Talba yai ya fice daga falon, sai Leila ta sauko da sauri zata bi bayansa, kamar wanda ta tuna wani abu sai kuma taja ta tsaya cikin yanayi n rashin jindad

“Yanzu ai kin jidadi ko?”

Kabir ya tambaya yana gyara shirt din jikinsa. Sai ta kalleshi cikin yanayin damuwa domin har ga Allah bata son Talba ya shiga damuwa duk kuwa da irin son da take ya canja bata son ace saboda ita Momy ta yi masa Wani abun bacin rai domin ba su saba haka.

“Wane irin dadi kuma? Kana jin kalaman da Momy ta fada masa fa”

“Eh ai ke kika ja, ke dai burinki wulakanta mutane”

Yana kaiwa nan shi ma ya nufi kofar fita falon cikin bacin rai, duk irin rashin jituwar da suke samu da Talba baya son wani abun bacin rai ko damuwa ta same shi, kamar yadda Talba ma baya son ganin bacin ran Kabir sai dai dukansu sun san cewa ba a komai na rayuwa suke shan inuwa daya ba, musamman ma Talba da yafi kowa girman kai a gidan.
Juyawa tai ta hau stairs din ta nufi dakin Momy, ko knocking bata tsaya yi ba ta tura kofar ta shiga kamar zata fasa kuka.

“Haba Momy wannan abun har ya kai ki fadawa Talba irin wannan maganar ne?”

Momy dake zaune gaban madubi tana kokarin cire awarwaron hannunta ta juyo ta kalleta da mamaki.

“Ba ki kalmar da yake jifata da ita ba?”

“Da ni yake ba da ke ba”

“No cewa yai baki da tarbiya, kai tsaye na fahimci inda kalamansa suka dosa, tun ba yau ba ai na lura da yadda ya canja kamar mai son yai kishi da ni”

“Haba Momy Talba ne zai yi kishi da ke?”

“Eh mana, bakisan wasu yayan suna tsanar iyayen da ba su haife su, Idan ba haka ba ai ba zai min kalaman banza ba, ko ba komai ni surukarsa ce right”

“Momy yanzu zai ji babu dadi Wallahi ransa zai bace”

“Ran nasa ya dade be bace ba, wannan wane irin so ne kike ma Talba wai? Shi fa baya son ki kamar yadda ke kike sonsa, kuma naga ke ma ai kina bata masa ran”

“Eh amman Momy wannan ai matsalar mu ce ta dabam ba wai akan ba”

“I don’t care, idan ke baki san zafin abun da ya fada ba ni na sani”

Mikewa tai tsaye cikin yanayin damuwa ta fice daga dakin tana ta sake sake, ko ta kira ta bashi hakuri akan abun da Momy tai ko kuma ta kyale shi, sai dai idan ta tuna cewar saboda ita komai ya faru sai ta ji wani iri.
Dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira Madina ta labarta mata abun da ya faru, daman komai na duniyar ba zata iya boyewa Madina ba, no matter how Momy ta kwatseta akan abu sai ta fadawa Madina.

“Amman Leila baki taba bata min rai irin yau ba, wai miyasa kike barin zuciyarki tana aikata abun da Talba baya so? Ke baki san yadda zaki faranta masa rai ba? Haba Leila ni kam da baki labarta min wannan abun ba da ban shiga damuwa ba Mtchssssss ”

Ta yanayin yadda Madina take mata responding kadai ya isa ya karantar da ita cewar Madina ta fita shiga bacin rai ma.

“Ni ma fa ban jidadi ba, that’s why na kira ki ko zan samu mafita”

“Mafitar me? Ni Wallahi kin bata min rai, i don’t think i can eat today, kin bata ran bawan Allah, na sha fada miki haka rayuwarsa take ki bishi a haka mana sai ku samu zaman lafiya amman kin gagara daukar shawarata”

“Look Madina na yarda a nan ina da laifi daya janyo aka fada masa magana marar dadi, amman maganar Allah ban ga laifi a abun da na yi ba, Talba yana shigar min hanci da yawa fa”

“Yanzu dai na ji, idan kina son mu shirya da ke kije ki bashi hakuri”

“Na bashi hakuri fa? Gaskiya ba zan iya ba”

“To miye a ciki, ke fa kika ja komai, kuma ba akan abun da yai miki fada zaki bada hakuri ba, akan abun da Momy tai masa”

“Zan ga idan zai yiyu”

“Please do this for me, tsakani da Allah ko kadan bana son na ji ran Talba ya bace, Mutumen yana son ki Leila kin kasa ganewa ne, kina raina yadda rayuwarsa mata da yawa suna can suna sonsa a haka, ki bi a hankali”

“Na ji”

Ta fada tana juya ido, bata tsaya jiran abun da kawarta zata sake fada ba ta yanke wayar ta wurgar saman gadonta, sannan ta fadi kwance.

TALBA POV.

A lokacin daya fita daga falon cikin motarsa ya nufa ya zauna, ba karamin taba shi kalaman Momy sukai ba, duk yadda ya so ya ga laifin kansa kan abun da yai ma Leila sai ya kasa, zuciyarsa nata raya masa a daidai yake, hannu ya kai ya dauki wayarsa ya kira Ali.

“Hello”

“Kana ina?”

“Office ya akai?”

Iskar dake bakinsa ya busar ya kashe wayar ya aje gefensa sannan yai ma motar key yai reverse ya danna horn, tun kamin ya isa gate suka bude masa sai da ya fito ya ga motar Leila dake waje har lokacin sai dai wannan karon an kullenta amman motar tana kunne, horn ya danna har sau biyu wanda hakan ya saka Bello Police lekowa ya nufo motarsa da sauri, sai ya sauke gilashin motar ya nuna masa motar Leila, Bello na ganin ya nuna motar ya san abun da yake nufi na sai ya masa magana ba. Sai ya nufi motar Talba kuma ya hau titi, driving yake kamar wanda be san inda zai je ba, kadan kadan yake lafiya har ya isa asibitin FMC a inda ya saba fakin ya faka motarsa ya fito yana jin kamar ya juya ya tafi gurin aikinsa sai dai ya san he need someone to talk to, a duk lokacin daya shiga wata damuwa komai kankantarta Ali yake fara fuskanta ya fada masa damuwarsa duk kuwa da kasancewar wani lokacin za su rabu a fada ce ne. Kai tsaye office dinsa ya nufa and he got lucky Ali yana ciki sai dai office din ba shi kadai ba ne tebur biyu ne na dayan abokin aikinsa. Ko kallon gefen da abokin aikin na Ali yake be yi ba ya nufi teburin Ali ya zauna a kujerar baki. Ali na kallon abokinsa ya fahimci akwai damuwa.

“Leila ce ko?”

Talba ya dago ya kalleshi, sai kuma ya juya ya kalli teburin abokin aikinsa sai a lokacin ya lura da be shigo ba

“No”

Ya amsa masa cikin yanayin damuwa.

“Na san dai abu ne mai wahala yadda Daddy yake ji da kai abu ne mai wahala ya bata maka rai, sai dai idan wata damuwa ce ta dame shi a san zata iya shafarka”

Ajiyar zuciya Talba ya sauke, sannan ya labatawa Ali abun da ya faru. Ali ya kwanta jikin kujerarsa yana kallon Talba duk kuwa ya san kallo na daga cikin abun da abonkinsa ya tsana.

“Momy dai ta fusata ne, kuma kai ke da laifi”

“Amman Ali ban yi dan taji haushi ba, ba ina nufin bata bawa Leila tarbiya ba, kawai bata fahimci ni ba”

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya nufi windows din office din.

“Kuma na ji babu dadi, na san ba ita ta haife ni ba, amman ban taba mata wani kallo na dabam na bayan uwa, ita ta raine ni a hannunta na tashi na girma”

“Kai ka ji zafin abun da ta fada maka balle ita? Yanzu dai ka manta da komai ka dauka cewar kuskure ne irin wanda kowa yake yi”

“And seriously ba zan iya zama da Leila da wannan halin ba”

“Kai da za a bibiya zata ce ba zata iya zama da kai saboda halinka ba, Talba dan adam duk tara ne be cika goma ba kowa ka ganin yana da inda be cika ba, abun da zai fi kawai ka dauke idonka daga gareta, musamman a yanzu da ka fahimci idan ka taba ta ran Momy yana baci, ka bita a yadda take sai a samu zaman lafiya”

“And… ”

“And ka koyi bada hakuri Talba, ba zaka ragu ba, mata rarrashi suke so, yanzu duk wannan abun daya faru idan ka koma gida ka yi kamar komai be faru ba, ka samu Leila ka lallabata ka bata hakuri”

“Ba a hallici wannan macen da Talba zai bawa hakuri ba, ba ayi mace da zan yi ma yar murya ina lallabata akan tai hakuri ba, matukar tana kasa da ni”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button