BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 13

“Ya kamata ka sauke wannan nauyin daka dorawa kanka Talba life is very simple”

Talba ya juyo ya kalleshi.

“Ko?”

Sai Ali yai dariya domin ya san halin abokin nasa yanzu zata iya bare musu su fara siyar da hali.

“Yanzu dai forget about it, akwai maganar da nake son mu yi da kai”

Talba ya juya ya cigaba da kallon harabar asibiti da yadda mutane suka zirga zirga sai dai hankalinsa da ears dinsa suna gurin Ali.

“Akwai wata yarinya da aka kawo last week, tana cikin mutanen da yan bidiga suka raunata”

Yana tsaka da maganar sai kuma yai shiru yana duba wata takarda dake gabansa.

“To ta ina alakarta ta shafe ni?”

Talba ya tambaya ba tare da juyo ba, jin Ali ya dauko masa wata maganar da be san ta inda zata masa amfani ba. Murmushi Ali yai yana jinjina halin abokin nasa.

“Tana bukatar taimako ne sosai gaskiya”

Juyowa Talba yai ya rumgume hannayensa yana kallon Ali.

“Kai ina zuciyar taimakonka ta tafi ne? Ko baka taimako?”

Ali yayi dariya.

“Talba kasan irin taimakon da na yi mata? Tun da aka kawo su ba Gobnati bata sake waiwayarsu ba, babu wani tallafi da ake kawo musu, mostly yan uwa da iyaye ne suke daukar nauyinsu, sisin kwabo babu daga gobnati komai daga alijunsu dana yan’uwansu yake zuwa, wasu an sallame su sai dai wadanda albarushi ya shiga jikinsu ne kawai suke nan suna jinya har yanzu”

Ya hade yawun bakinsa sannan ya cigaba.

“But yarinyar har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, babu wani da yazo yace shi babanta ne ko yayanta, komai da ake biya daga aljihuna ya fita na taimaka mata saboda ta bani tausayi sosai”

Ganin Ali yana maganar babu alamar wasa a tare da shi yasa shi tambayar abun da yake son ji daga gareta.

“Miya same ta?”

“Na farko dai she can’t walk, she can’t talk tun da aka kawo ta bata taba magana ba, idan dare yayi sai na yi mata allurar bachi sannan take iya bachi, kuma na yi na yi da ita ta ki tai magana, babu wata alama data nuna yarinyar tana magana, idan ma kaga ta motsa to na matso kusa da ita ne da allura, sai ta fara kallon allurar tana hawaye, and the most sadness part is an yi mata fyade sun lalatata ko mai haihuwa iyaka kenan”

Kusan a lokaci daya komai dake aiki a zuciya da jinin Talba ya tsaya cak na dakiku. Kalmar fyade wata irin babbar kalma ce mai razanarwa da muni a kunnuwan tsabtattacin mutane irin Talba, shi din namiji ne ba mace ba, amman ya tsani jin duk wani abu daya shafi fyade balle kuma fyaden kansa, be taba ganin Aminatu ba, labarin wanzuwarta be taba ziyartar kunnensa ba, kamar yadda zuciyarsa da tunaninsa ba su hasaso masa mai irin rayuwarta ba, wani abu daga cikin cikin tausayinta ya kusa zuciyarsa ya samu guri a kusa da kirjinsa ya zauna, hankalinsa ya kara tashi sosai a lokacin da Ali yake kara fada masa halin da yarinyar take ciki.

“I don’t think kurma ce, domin idan na ce kee zata kalleni amman bayan haka bata yin komai, na sha jera sunaye ina kiranta da su amman bata taba min wata alama da zan gane sunanta ba, kuma kafanta ya kumbura wanda hakan ke nuna ta yi tafiyar da ta wuce kima kuma ta taka abubuwa da yawa gaskiya yarinyar tana bukatar taimako”

“Ta ina ya kamata na taimaka? Irin mutanen kamata yai ace gobnati tana daukar nauyin maganinsu fa”

“Wallahi kuwa ni ma abun da nake fada kenan amman sai kaga an barsu kara zube ba a kula su. Yanzu dai tana bukatar a duba lafiyar duka jikinta, a kula da kafafuwanta, private part dinta dai yana samun sauki sai dai da zata samu wanda zai kula da ita da zata fi samun sauki”

Ali na kaiwa nan ya mike tsaye.

“Zo muje ka ganta”

“No ba sai na ganta ba, kasan akwai mutane sosai a gurin nan”

“Haba dai irin abubuwan nan suna karawa mutum tsoron Allah, Allah kadai ya san halin rayuwar data shiga, ni ba abun da ya fi bani tsoro kamar rashin maganar ta, kuma gashi har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, and bata kallon mutane idan zan shiga inda take har na yi abun da zan yi na gama ba zata kalleni ba sai idan na dauko allura, and wani lokacin sai kaga hawaye na sauko a idonta, idan aka aje mata abinci bata ci yadda ka bar shi haka zaka zo ka tararda shi, idan ka danka mata abu a hannu bata rikewa”

“Ya ake take rayuwa bata cin komai?”

“Ta hanyar allurar da maganin da muke saka mata a drip”

Talba ya lumshe ido ya bude.

“Mutanen nan suna ganin rayuwa, farincikin da suke so, kadan ne amman ya gagaresu, a kashe su, a kwashe dukiya a kune kuma wandanda aka raunata a bar su da daukar nauyin kansu, Allah kadai ya san abun da akai mata ko ta gani”

“Wallahi ai mu muna ganin abubuwa sosai”

Ali ya nufi kofa Talba ya bi bayansa sai suka fito tare suka jera zuwa gurin da ake aje marasa lafiya, suna tafe Ali na masa hirar wasu da aka kawo da yadda sukai ta fama da su, Talba dai be ce Uffan ba har suka shiga female ward din suka doshi gado na 36 da inda Aminatu take kwance. Ko da suka isa sun tarar an ja mata lalube gurin da take, an rufe ta ta ko’ina ta yadda bata ganin kowa kuma kowa baya ganinta. Ali ne ya fara daga labulen ya shiga sannan Talba ya shiga. Kwance suka same ta idonta a rufe hawaye na saukowa ta gefen idonta. A zatonsa babbar mace ce sai da ganinta yarinya mai kananan shekaru yasa jin tausayinta ya karu da kashi talatin cikin dari, domin ya san fyade na daga cikin abun da yake lalata rayuwar ya mace, kuma yana daga cikin abun da mace tafi tsana balle kuma wannan da take karamar yarinya. Ali ya saka hannu ya dauki safar dake gurin ya saka a hannu sannan ya taba kafarta sai ta bude idonta da suka yi ja da alama ta dade tana hawayen ta sauke su akan Talba dake kallonta fuskarsa cike da haiba da annuri. Shi ma kallonta yake ba yabo ba fallasa, daga can cikin zuciyarsa cike take da tausayinta sai dai jinkai da rayuwarsa daya daukarwa kansa ya saka ya kasa barin hakan ya bayyana a kyakkyawar fuskarsa.

“Da son samu ne, a ware mata daki daya ita kadai saboda halin da take ciki, so that ta samu kulawa ta musamman kuma tana bukatar ayi mata gwaje gwaje, tana ma bukatar jini”

Ali ya fada yana kama hannunta ya tabawa. Har lokacin Aminatu Talba take kallo ji take kamar ta taba ganinsa a wani gurin sai dai bata san ko’ina ba ne, ji take kamar ta bude baki tai magana sai dai bara da kuzarin yin haka, kamar yadda take jin jikinta be da kuzarin riketa balle har hannunta ya jimke wani abu, tabbas yanzu kam ta tabbatar da kalamanta sun kare, kamar yadda take jin komai na rayuwarta a yanzu ya zama tarihi, bata yarda ita ce dai wacan Aminatun dake rayuwa a karkara tare da iyayen da yan’uwa ita ce a nan ba.
Da ace zata iya bude zuciyarta ta sun yi arba da tarin bakinciki da duhu zuci, wanda idan suka karanta wata kila likitan zai tausaya mata ya daina bata taimakon da yake bata na drip da allurar so that ta samu ta huta ita ma tafi sahun yan’uwanta da iyeyenta. Har gobe tana jin karar bindigar da aka kashe mahaifinta da mahaifiyarta a cikin kanta, ta kasa manta yadda yan ta’addan suka rika yawo a jikinta a lokacin da suke kokarin keta rigar mutuncinta, idanuwanta sun ki su goge hoton fyaden da akai ma mahaifiyarta a gaban ido wai shin miya rage mata? Miyasa take a raye har yanzu?

Ali ya kalli Talba dake tsaye ya kalli Aminatu data kafe Talba da ido, a zahiri shi take kallo, a badini kuma rayuwarta bayan take hange a cikin idanuwan mutumen da take jin kamar ba a yau ta taba arba da shi ba. Har lokacin hawaye ba su daina zubar a idonta ba.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button