BAKAR WASIKANOVELS
BAKAR WASIKA 13

“Kallon mutane ba dabi’ar bace ko dai ta san ka ne?”
Ali ya tambaya, kallonsa kawai Talba yai ya dauke kai.
“Kin san shi ne?”
Bata dauke ido daga kallon Talba da take ba balle har ta kali Ali ta amsa masa. Ali ya kalli Talba dake kallonta shi ma har lokacin.
“Ka yi mata magana wata kila zata amsa”
“A canja mata daki idan kana ganin hakan ya dace, idan ka yi list din ko nawa za a ashe sai ka fada min”
Shine abun da Talba ya fada sannan ya sakar ma Aminatu murmushinsa mai tsada kadan wanda yafi kama da na yake ya juya ya fice. Yana fita sai ta lumshe idonta kamar mai bachi sak rayuwar da take a gidansu ita da iyayenta da yan’uwanta ya soma kawata idonta dake rufe. Juyawa Ali yai ya fice yana kokarin cire safar hannunsa.