BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 2

TALBA POV.

Yana shakimce cikin mota har Ali ya iso gurin motar ya bude front seat ya shiga ya zauna yana kallon abokin nasa

“Lafiya dai?”

Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke sai huci yake, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya shiru ya maida dubansa wani gurin. Ali na ganin hakan yai dan murmushi.

“Leila ta tabo ka kenan?”

Talba ya kalleshi da idanuwan dake nuna bacin ransa karara kamar yadda fuskarsa ma ta kasa boye bacin ransa.

“Wai yarinyar nan ni zata wulakanta?”

Magana yake kamar wuta na fita a bakinsa. Ali ya masa kallon natsuwa.

“In I’m not mistaken ka sake mata maganar auren kenan?”

Shirun da Talba yai ne ya tabbatarwa da Ali eh ce amsar tambayar.

“Amman ta wace siga kai mata maganar?”

Talba ya watsa masa wani banzan kallo.

“Kamar wani karamin yaro zaka tambaye ni wace Siga nai mata maganar?”

“No baka gane ba ne Talba, su fa mata yan lalabawa ne, kai kuma sai kace komai da karfi da isa zaka yi ba haka ake ba”

Talba ya watsa masa wani kallo.

“Okay kamar ba baka san ni ba kenan? So kake na je na same ta ina lallashinta ta aure ni?”

“No kai baka gane ba, Talba wannan lokacin ya wuce da zaka dinga tirsasa mace ta yi maka abu any how, na san Leila tana sonka amman kai din ne wani iri”

“Kai Ali duk fa mace da zan aura alfarma zan mata, ba dai ita ta min ba, ina da kudi ina da kyau ina da ilmi ina da addinin da har a kasar waje za a iya bani aure balle a nigeria a nigeria ma a gidanmu”

“Ka ga matsalar ka ba, wani irin alfarma tun da har kuna son junanku? Kar fa ka manta Talba Leila a waje tai karatu kuma wayayyiyar mace ce mai son burgewa, Talba dan kalaman nan na soyayya baka san kai mata ba, dan morning text din baka tura mata, balle har ka kirata ku yi fira, ko ka dauke ta ku fita, mata suna son wannan”

“Ba zan yi ba, ina namiji zan wani zan wani rika lallaba mace, idan ma zan mata sai an yi aure, amman ba a yanzu ba ai sai ta raina ni, besides muna gida daya zan rika mata haka?”

“To miye a ciki, ai an san aurenta zaka yi tun da an muku baiko, kai komai sai kace na zafi zaka yi, idan ka sake mata ba shi yake nufin ka bata umarni ta ki bi ba, dan Allah ka kirata yanzu ka bata hakuri”

Kamar wanda aka cewa cire ranka ka bata haka Talba yai ma Ali wani irin kallo na mamaki da tsoro a lokaci daya.

“Ni Mu’azzam Auwal Shimkafi zan kira mace na ce dan Allah ki yi hakuri? Macen da ba uwata ba? Malam dan Allah fitar min a mota”

“Talba mata fa sai da haka, kuma ka canja hali dan Allah”

“Ita ma ai bata iya kalaman soyayya ba, bata san ta kira ni ta gaishe ni ba ko ta turon sakon soyayya, kai ni bana jin ma akwai ranar da Leila ta taba kallona tace kana da kyau simple word bata taba fada min ba, sai ni zan fada mata? Ba yi wannan macen da zan zauna ina bude mata sirrin zuciyata ba har ina rarrashinta”

“Wannan ji da kan babu inda zai kaika Talba, idan ka sake mata ka nuna mata kauna dole ita ma zata sauko fa”

“Malam na ce ka fitar min a mota…!”

Yanayin yadda yai maganar ya isa ya sanar masa ba da wasa yake ba, kuma ya san halin abokinsa idan ransa ya bace baya jin rarrashin sai dai hakan ba zai hana anjima ya kira shi yace yana son wani abu ba ko kuma su gadu a guri kaza. Salun alum ya bude motar ya fita yana murmushi da mamakin irin halin Talba.

“Ina fada maka matsalata kana wani kokarin ba ni laifi, an fada maka mata haka ake musu ne!”

Magana yake da kansa yana tukin cikin bacin rai, domin be san inda zai je ba a yanzu kasancewar yau weekend kuma gashi safiya ce be ma karya ba.

@12:44pm

Leila na zaune tool din mirror Momy tana zana mata abun da ya faru.

“Kawai sakonsa na gani a wayata wai na fito waje yana son magana da ni, Momy babu ko irin shaukin nan Wai Ke fito waje ina son magana da ke, haka dai na daure na fita, na same shi a balcony ya kusan 30 be ce min komai ba, sannan wai ki yi fixing date na auren mu, Imaging babu ko dan shauki sai wani ji da kai”

“Ke kuma kika ce masa me?”

Momy ta tambaya tana harararta.

“Na ce nasa ba zan yi ba, ni ban tashi aure yanzu ba”

“Ki ba shi hakuri”

Ta kalli Momy kamar tai magana sai dai ganin babu wasa a fuskar Momy yasa ta mike tsaye ba tare da tace komai ba ta fice daga dakin cike da bacin rai. Dakinta ta shiga ta dauki key din motarta da jakarta da wayarta, ta fito babu mayafi ta sauko kasa kamar zata tashi sama, daman ta saba fita babu mayafi abu ne mai wahala ka ganta da mayafi a jiki komai kankantarsa.
Tana fitowa ta nufi gurin da motarta take ta bude ta shiga tai yi warming dinta sannan ta danna horn da karfi mai gadin na ganin hakan yai saurin bude mata gate. Kamar wata mai gasar tsere haka ta fito daga cikin gidan da mugun gudu ta hau titi tana jin kamar ta fasa ihu. Sai da tai nisa sannan ta dauki wayarta ta kira Adam.

“Besty kana ina?”

“Ina gida ya akai? Kamar kina cikin damuwa”

“Ina ciki besty mun yi fada da Talba?”

“Mtssss wai me ke damun Talba ne?”

“Ina na sani, ban san abun da yake takama da shi ba, indai kudi ne ni ma ina da su, ilmin ina da shi kyau ba za a min gori ba, amman sai wani nuna isa da ji da kai”

“Wallahi kam yan kalaman soyayya ma ace ba zaka iya yi ma mace ba, idan an yi auren ya kenan?”

“Shine abun da nake magana a kai, ni kuma sai na nuna masa ina da tsada ni ba kamar sauran mata ba ne, dole na ja masa aji, yadda yake jin ba zai iya min kalaman soyayya ba ko ya dauke ni mu fita ko ba ni hakuri haka ni ma ba zan taba yi masa ba”

“Hakan shi ne daidai, kara ya san darajarki a dole ya sauko idan yana sonki”

“Shine ai, shi kawai abunda ya dauki mace ya mata umarni ta bi ya juyata yadda yake so, ni kuma sai na nuna masa na fi karfin haka Wallahi”

“Yanzu dai kwantar da hankalinki ki samu ruwa ki sha, ki fita waje ki sha iska zan zo na dauke ki mu fita”

“Har na ma fito gida amman bari na koma”

“Okay but ki yi murmushi pls”

Ta yi murmushin mai sauti kamar yadda ya bukata, sannan ta aje wayar, ta juya ta koma inda ta fito. Kamar yadda ta fito haka ta koma gidan da gudunta ba da damuwa da titi ko sauran motoci burinta dai ta aikawatar da abun da take so. Horn biyu tai kamin tai na uku Mai gadin ya bude mata gate ta shiga cikin gidan da mugun gudu ta faka motar a inda ranta ya so ta fito ta nufi kofar falon, door bell ta danna da karfi kamar zata balla shi sannan taja ta tsaya tana tsaki, shiru ba a bude ba har sai da ta sake danna door bell din sau biyu ta hada da knocking. Sannan Baaba ta bude mata.

“Wallahi tallahi kika sake barina a tsaye a waje ina knocking, abincin ki ya kare a gidan nan Baaba”

“Wanke wanke nake yi Leila shiyasa”

“Na dai fada miki”

Ta fada cikin tsawa, ba dan Baaba ta yi saurin kaucewa ba da Leila tureta zata yi ta wuce. Baaba ta maida kofar ta rufe sannan ta juyo cikin falon cikin rashin jindadi zata koma Kitchen din sai ta ji muryar Momy dake tsaye stairs.

“Baaba a rika kula mun dauke ku aiki ne kawai saboda mu huta, a daina batawa yarana rai”

Baaba ta daga kai ta kalli Momy sannan ta daga mata kai cikin da ladabi.

“To Hajiya Inshallahu za a kiyaye”

Sannan ta sadda kanta kasa ta nufi kitchen din cikin rashin kuzari.

FARUQ POV.

Kallonta ya tsaya yi da dayan biyu kamin ya amsa gaisuwar da tai masa, domin ba kasafai take gaishe shi da safe ba sai idan tana son wani abun ko kuma ta lura aljihunsa da dan nauyi.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button