BAKAR WASIKA 2

“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah, sai yunwa da nake ta ji tun jiya”
“Toh Allah ya buda mana kofafin samu”
“Amin…”
Ta amsa tana kallon Sultan dake motsawa alamar zai farka daga bachin da yake.
“Na ce wai ba zaka kira abokin nan naka ba, ka roki shi dan wani abu?”
Ya girgiza mata alamar aa.
“Ba zan dauna kullum ina bin abokai ina rokonsu ba, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abun da zai ci ba, kuma ni ma na yi karatun idan mu kai hakuri komai zai wuce”
“Matsalar kenan Faruk girman kai, kana da girman kai, yanzu haka zamu zauna mu wuni da yunwa gashi idan ka fita baka dawowa sai dare? Ga ni da ciki ga Sultan?”
Yayi shiru yana jin yadda kansa yake sara masa saboda maganganun da Baturiya ta fara masa.
“Shiyasa na ce zubar da cikin nan zan yi na huta, kai ma ka huta domin na san ko ragon suna da wahala a samu a yanka masa wannan bakin talaucin da muke fama da shi”
Ta fada cikin kukanta na munafurci. Sai ya kalleta a raunane.
“Zubar da ciki ba zai kawo mana Mafita ba Rafi’a miyasa ba ki da tunani ne wai?”
“To ni dai gaskiya yunwa nake ji, tun jiya fa ban ci komai ba, kuma anjima na nan ga Sultan ma”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya mike tsaye ya fice daga dakin cike da damuwa. Binsa tai da harara.
“Ni dai Wallahi na gaji da wannan bakar rayuwa, Allah kadai ya san yadda masu kudi suke ji, su kwanta a mai kyau a ci abun da ake so, ni ko na kare a nan duk kyau na”
Ta fada tana mikewa tsaye tare da bin bayansa, sai da ta tabbatar ya fita sannan ta dawo ta dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta kamo number da tai saving jiya. Maryam Dahiru Sokoto ta aika mata kira, ringing tai har ta tsinke ba a daga ba ta sake kira nan ma ba a daga ba.
“Ka ji yan gayu sai ayi ta kira basa dagawa…”
Whatsapp dinta ta bude ta shiga gurin numbers ta kamo number wanda ke dauki da hoton wani matashin da ba zai wuce sa’an mijinta hakimce cikin mota. Sai da ta gama kallon hoton sannan ta shiga aika masa sako.
‘Assalamu Alaikum, ranka ya dade fatar an tashi lafiya, ya aiki ya Madam da yara. Ranka ya dade sunana Fee’ah matar Faruq abokinka, na kira baka daga ba shiyasa na yanke shawarar turo maka sako. Wallahi muna ciki matsala, yau kusan kwana nan mu hudu ba mu girka komai ba, shi ma idan ya fita haka yake dawowa saboda shagon da aka bude sabon gurin ne cikin wata sabuwar unguwa ba kowa yake ta aski ba, yanzu haka Sultan kuka yake, ni kaina dauriya kawai nai saboda da na, Dan Allah ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka, na duba na ga a cikin abokan Faruk babu mai tausayinsa da son taimaka masa irinka, na so Faruq yai maka magana da kansa amman yace nauyi yake ji, yanzu haka be san na dauki number ka ba, domin idan ya sani ina ciki matsala. Ka huta lafiya Allah kara rufa asiri’
A rarrabe ta tura sakon har tana gadawa da emoji din rokon da kuka. Sannan ta duba last seen dinsa tun jiya da dare, tana jin motsin turo kofar gidan tai saurin aje wayar ta kwanta kasa. Faruq ne ya shigo dakin rike da bakar leda har biyu a hannunsa. Ya aje mata dayar a gabanta ganin hakan yasa ta tashi zaune tana kallon 200 dari biyun da ya mika mata.
“Ina ka samo?”
“Ke dai ka bar”
“Dan girman Allah Faruq ka daina mana cin bashi kana kara mana kanskanci a unguwa kamar kan mu farau talauci”
“Ba bashi na ci ba wayata na bashi jingina”
Bata ce komai ba ta karbi dari biyu kana ta bude ledar tana duba taliya da makaroni dake ciki sai maggi da mangyada.
“To wannan ledar fa?”
“Mama zan kaiwa”
Yana fadar hakan ya juya ya kalli dansa dake sharar bachi sannan ya fice ba dan ranta ya so ba.
“Mu ba mu wadatu ba amman sai dauka ka kaiwa wasu, mtchhhh”
Ta karasa tana jan tsaki.
“Kuma Wallahi sai na zubar da cikin nan haka kawai zan zauna ga talauci ga wahala da kurciyata da kyauna”
Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki ledar taliyar ta fito waje domin sarrafawa. Kallo daya zaka masa ka karanci damuwarsa abubuwan duniya sun taru sun masa turr kamar ya zagi arziki kamar komai yake juye masa, gashi yayi degree amman aiki ya gagara duk inda yai applying shiru ba wani motsi. Da tunani kala kala mai achaba ya sauke shi unguwar Dallatu wato gidan mahaifiyarsa, sai ta ciro naira dari a mika masa sannan ya ratsa cikin gidanje har ya isa kofar gidan ya tura ya shiga da sallamarsa. Kanensu biyu mata da suke tsakar gidan suka amsa masa suna masa sannu da zuwa, bayan ya amsa musu ya nufi dakin Mahaifiyarsa ba karamin faduwa gabansa yai ba ganinta a kwance domin ba al’adarta bace yawan kwanciya musamman a irin wannan lokacin.
“Mama lafiya dai? Ko jikin ne?”
“Da sauki ai Alhamdulillah”
Ta amsa masa tana murmushin karfin hali.
“Wani irin da sauki ga ki kwance? Kai Innalillahi Wa’inna illahirraji’un”
Jin furuncinsa yasa ta yunkura ta tashi zaune tana kallonsa.
“Ina Sultan?”
Kasa amsawa yai sai kallon mahaifiyarsa yake, yana jin kamar ace yana arzikin da zai iya kaita Asibiti, domin ba yau ciwon ya fara ba.
“Mama ko dai maganar auren Aisha da akai ne jiya ya tada miki hankali? Idan ma fasa aurenta zai yi ai ba wani abu ba ne zata samu wani”
“Har aure nawa za’ayi ta fashi ne Faruq? Haka zamu ta zama ana fashin aure saboda talauci? Kuma yaran nan sai girma suke, sai gulma ake mana a unguwa”
Ta tambaya idonta tab da hawaye, Faruq yayi saurin kawarda nasa idon yana sauke ajiyar zuciya, domin kukan mahaifiyarsa na daga cikin abun da ya fi tsana a rayuwarsa.
Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.
Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.