BAKAR WASIKA 3

Ya daga kafadunsa alamar be damu ba.
“Then ai zan samu wata da gudu ma”
“Hakan na nufin ba wani son Leila kake ba, because idan kana son ta you won’t said that”
Ya dan yi shiru kamar mai nazari.
“No i love her Daddy kawai dai ina sonta, but i won’t tolerate nonsense”
Daddy yayi Murmushi yana dafa kafardarsa.
“Idan so ya zurfafa a zuciyarka, baka san lokacin da za ayi maka nonsense ba kuma ka dauka, a lokacin zaka zama wani stupid, fool, za a fada maka baka ga tana maka kaza ba, kace ka ji amman kana sonta ba zaka taba ganin laifin abun da take maka ba, mark my words”
Talba yayi murmushi irin murmushin nan dake nuna ban yarda ba, ranar ma ba zata zo ba.
“Yanzu ka gama cin abinci kaje ka samu Leila duk inda take ka dauko ta ka dawo da ita gida, kuma ka bata hakuri”
“No no no Daddy kasan ni bana ba wanda yake kasa da ni hakuri”
“Ba sai kace mata sorry abun da nai ban kyauta ba, no ka mata abun da zata ji farinciki sai ta manta da komai simple”
Ya dan yi jimm yana jin kamar an dora masa katon aiki.
‘Maybe i can try’
Ya fada a ransa a fili kuma sai ya amsawa Daddy da.
“Okay Daddy, for the sake of you”
Daddy yayi murmushi yana jinjina lamarin dansa.
FARUQ POV.
A gidan Mahaifiyarsa yai wanka sannan ya fito ya nufi gurin abokinsa, dake unguwar. He got lucky yana gida, yana sallama masa ya fito, bayan sun gaisa Faruq ya gabatar masa da abunda ke tafe da shi.
“Shamsu, na zo neman wata alfarma ne a gurinka”
“Allah yasa zan iya Faruq”
Faruq ya busar da iskar bakinsa.
“Wallahi ina cikin matsaloli ba ma daya ba, kasan matsalar kasar nan, mutum zai yi karatu amman aiki shiru, ga dan shagon da na kama sabuwar unguwa ce ba mutane sosai”
“Wallahi kasar ce har ka rasa yadda zaka misalta ta, abubuwan sai a hankali, idan baka yi karatu ba abun ya dame ka idan kuma ka yi aikin ya gagara”
“Shine nake son na fara koyon irin sana’arku, duk da ba iyawa nai ba amman dai idan nayi tare zan iya da yarda Allah”
Shamsu ya masa wani kallo na mamaki, a tunaninsa zai ranci kudi ne a hannunsa, sai ya ji yana masa maganar sana’arsu, ba Shamsu kadai ba kusan duk wanda ya ji mutum mai degree zai yi sana’ar gini zai yi mamaki, domin muna a zamanin da masu degree da kuma mutane suke ganin ba ko wane irin aiki ne ya dace da su ba, wani abun ana ganinsa kamar kaskanci ne, ace kana da degree kuma kai yi shi.
“Faruq zaka iya sana’ar gini kuwa? Kai da kai karatu? Kuma jikinka be saba da aikin wahala ba”
“Shamsu kenan, wanda ya tashi a area kamar wannan kuma dan talaka zai ce be saba da aikin wahala ba? Ya kake magana kamar ba san gidan da na fito ba?”
“To abun ne da mamaki Faruq naga kai ka yi karatu ka ni ban yi karatun ba”
“Ka aje komai a gefe ka duba bukatata idan zai yiyu”
“Inshallahu, sai dai ka san aikin mu tasowa yake ba wai kullum ba ne sai idan ta samu, inshallahu da mun samu zan kiraka a waya tun da ina da number ka”
“To na gode sosai sai na jika”
Ya mika masa hannu sukai musabaha, Shamsu ya koma cikin gidansa cike da mamaki, Faruq kuma ya nufi titi cike da damuwa.
FEE’AH POV.
“Gaskiya kina da kyau sosai”
“Thanks”
Shine reply din da tai ma mutumen da facebook bayan ta tura masa hotunanta masu kyau, kamar yadda ya bukata.
“A ina kike da zama a Gusau?”
Wannan karon tashi tai zaune tana tunanin irin karyar da zata masa, domin bata fada masa cewar tana da aure ba, duk kuwa da kasancewar bata dora hotonta a profile picture ba, sai hoton sunan Allah data saka as her profile picture dinta.
“Gida dari”
Ta bashi amsa.
“Na san gurin idan na shigo zamfara inshallahu zan neme ki mu gaisa”
“To Allah ya nuna mana”
Ta bashi amsa tana murmushi, kamin ta sake shiga profile dinsa ta duba komai nasa, ciki har da gurin da yake aiki da kuma hotunansa, kana ganinsa ka ga wani hamshakin mai kudi mai connection da yan siyasa, domin yadda ake masa fadanci a profile ma ya isa ya sanar da hakan. Murmushi ta sake yi sannan ta dawo inbox din ta duba tambayar da yai mata ta biyu.
“Are you on whatsapp?”
“Yeah”
Ta bashi amsa da sauri tare da rubuta masa number wayarta ta tura masa.
“Okay Thank You so much Baturiya”
Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana jin sunan har cikin ranta. Sannan ta fita facebook din ta shiga whatsapp, few massage ta samu ciki har da reply din da MD Saleh yai mata, shi ta fara budewa da sauri jikinta har rawa yake kamin ta gama karantawa.
“Subhanallahi, Allah ya wadata, turo account number dinki”
Mikewa tai tsaye ta daka wani uban tsalle ta dire tsabar murna da jindadi sannan ta tura masa account din tana masa godiya.
“Alhamdulillah”
Ta furta sannan ta shiga group chat dinsu na makaranta, ta fita ta leka na matan aure ta fita ta shiga na novels nan ma bata dade ba ta fita ta bude chat din Ramlee.
“Kawata kin yi ciniki, wani ya ga Hotonki a wayata ya matsa na nemo masa ke”
Tana gama karanta sakon kawarta Ramlee ta zaro ido tare da sakin baki a lokaci daya, domin ta san sana’ar kawarta, tana da connection da manyan masu kudi tana hada su da mata kyakkyawa kuma masu siga kamar yadda ita ma take hulda da su, sai dai duk iskanci Baturiya bata taba aikata alfasha ba, za dai hadu da mutum har su gaisa ko kuma ta yi masa nata wayon ta waya ta samu yan canji, amman bata san tai mu’alama da maza ba, bayan Faruq babu wanda ya taba saninta a ya mace.
“Gaskiya aa Ramlee ni dai ina jin tsoro ba zan iya ba, amman idan kin san irin wanda zan yi ma wayo ne na ci kudinsa ba sai mun hadu ba, ba matsala”
Ta mayar mata da amsa duk da kasancewar Ramlee tana Offline a lokacin, sannan ta kashe datan ta aje wayar ta mike tsaye ta fito waje.
“Sultan zo nan yau zamu ci kaza”
Ta fada tana zaunawa jikin kofar falon tana mikawa danta hannu fuskarta cike da murmushi kamar yadda zuciyarta take fal da farinciki saboda kudin da za a turo mata, Sultan din ya rugo da gudunsa yana murna.
“Abba zai siyo mana ne”
Ta shiga kabe masa riga tana fadin.
“Ba nace ka daina cewa Abba ba? Ka rika cewa Daddy, yayan talakawa ne suke cewa Baba ko Abba, yaran masu kudi kuma su ce Daddy ka ji?”
“To Daddy ne zai siyo mana?”
“Aa adashen zan kwasa yau sai na siyo mana, amman karka fadawa Daddy ka kaji? Har da lemun kwalba zan siyo mana”
Sultan din ya shiga murna yana jindadi yau za su ci kaji, rabon da su ci nama har ya manta.
AMINATU POV.
A bakin kofar shiga gidansu ta hadu da Sanusi tsaye yana latsar karamar wayarsa.
“Ya Sanusi”
Ya kalleta sai kuma yai dariya.
“Igee ai sai ki fada mana cewar kin fara fita zance, mu shirya yi miki aure”
Ta cinno baki gaba.
“Ni dai dan Allah ka daina, Allah yasa ba ka fadawa Inna ba ko Baba”
“Ban fada ba, amman dai zan fada masa, Baba ma baya nan”
“Ina yaje?”
“Gwaggo ta Makka aka aiko bata da lafiya sosai, shi ne suka je tare da Junaidu a babur”
“Yanzu?”
“No tun dazun”
“Allah ya bata lafiya shi kuma ya dawo da ita lafiya”
“Inna tace naje na dubo ki, idan kin shiga ki ce ni na zo da ke”
“Wallahi ba zan fada ba”
Ta fada tana nufar cikin gidan.
“Ni kuma zan fada mata cewar kin yi saurayi”
“To na bari”
Ta yi saurin fada har tana dawowa baya, sai ya saka dariya ya biyo bayan kanwarsa suka shiga cikin gidan tare. Kamar Kullum inna na zaune tsakar gidan tana jiran dawowarta, domin bata bachi sai ta saka yarta a ido.
“Oyoyo Auta yar albarka, an siyar ko?”