BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 3

Aminatu ta aje kwallon tuwon da bokitin miyar da plates din roba a gaban ina tana sauke gajiya.

“Eh Inna wai Baba ya tafi gurin Gwaggo?”

“Eh an aiko bata da lafiya, aka ce mai rabon ganawa da ita ya zo”

“Allah ya bata lafiya”

Ta fada cike da damuwa, sannan ta ciro kudin cinikin ta mikawa Inna, sai da Inna ta kirga kudi ta ga sun cika sannan ta cire wadanda ta saba bata tana sakawa a asusu ta mika mata.

“Ga na ki”

“Na gode”

Ta fada bayan ta karba tana kallon Sanusi zuciyarta sai raya mata take zai fadawa Inna maganar, sai har sukai yar hira da zasu yi suka gama bata ci ya dauko zance ba, hakan yasa ta ji dadi sosai. Bata bude wasikar da Maniru ya bata, da fitilar da take zuwa talla ta haska wasikar da ya rubuto mata da hausar ajami, tana karantawa sai murmushi take tana jindadin yadda ya jera mata kalaman soyayya da kwantar da hankali.

Bayan ta gama karantawa ta rumgume wasikar a kirjinta, can kuma ta tashi ta saka a cikin littafanta na Islamiya kamar yadda ta saba, sannan ta gyara gurin kwanciyarta ta kwanta. Inna kam bata kwanta ba sai da ta gama komai ta kintsa komai kamar yadda ta saba sannan ta kwanta tare da rage fitilar kwai dake dakin, hasken ya rago sai dai bata kashe gaba daya ba saboda Aminatu na tsoron duhu sosai, bata bachi babu fitila a kusa da ita.
Misalin 12am gidan yayi tsit domin kowa ya nemi gurin kwanciya ciki har da yan awaki da tumakin da ake kiwo, can cikin bachi Inna ta soma jiyo hayaniya, tare da karar babura hakan yasa ta ta tashi zaune tana sauraren jikinta na bata ba lafiya ba, domin kowa ya san matsalar kasar a yanzu, balle kuma su da suke kauye. Aminatu kam sharar bachinta kawai take bata ma san ana yi ba, jin ihu da kuma fadar Innalillahi a makota yasa Inna ta nufi inda Aminatu take ta shiga tashinta.

“Auta Auta”

Ta fada murya can kasa kasa, a hankali Aminatu ta bude ido ganin Inna yasa ta tashi zaune.

“Inna…”

“Shiiiii”

Inna ta mata alama da tai shiru. Wanda hakan yai daidai da banko kofar gidan ta kwano a shigo, ga wata uwar fitila mai shegen haske da suke ta hasken gidan da ita.

“Innalillahi Wa’inna illahirraji’un”

Inna ta furta gabanta na bugawa da mugun karfi, Aminatu ta mike tsaye da sauri kamar wanda ta rude, Inna ta shiga duba dakin tana jin kamar ace akwai wata hanya da zata bi ta fita, a rikice ta nufi gadonta.

“Shiga nan Auta shiga shiga”

Da sauri Aminatu ta nufi karkashin gadon na karfe ta shige, zuciyarta na wani irin zillo kamar zata fito, Inna ta nufi kofa domin duba sauran yayanta sai dai kamin ta isa kofar suka shuri kofar da mugun karfi ta cire suka shigo cikin dakin kamar an aikosu. Baya baya Inna tai tana fadin.

“Innalillahi Wa’inna illahirraji’u”

“Rufe mana baki dan ubanki”

Yanayin yadda yai maganar da karayar halshe kadai ya isa ya sanar da cewar gayu ne suka hauro garin a yau, wato bandits abun da ba a taba ba, domin duk wani hargitsi da ake fama da shi sai dai su ji a makotan kauyukan ko kuma a hanya abun ya rutsa da yan garin, amman ba a taba shigowa cikin garin ba. Ba Inna kadai ba har Aminatu dake karkashin gado sai da ta saka hannayenta ta rufe bakinta. Ta ko’ina jikin Inna rawa yake, ganin manyan makaman da ke hannunsu.

“Ina mijikin yake?”

Kasa magana tai bakinta sai rawa yake kamar jikinta ga wani gumi dake karyo mata.

“Wato ke ce uwar yaran ga yan iska ko?”

Nan ma Inna kasa cewa komai tai sai ambaton Allah take a zuciyarta, hannayenta duka biyu rike da bakinta.

“Innalillahi”

Inna ta jiyo muryar yayanta a tsakar gidan, wani irin abu ne ya ziyarci zuciyarta sai ta ji kamar ace akwai abun da zata iya yi ta ceci yaranta.
Dun dun dun ta ji tashin bindiga kamin ta tantance komai ta ji muryar Sanusi yana kuka.

“Wayyo Allah na, la’ilaha illahu, Innalillahi”

A lokacin ne hawaye ya cika idonta, irin hawayen da kowace uwa take yi idan ta kasa taimakon yayanta.

“Wayyo”

Ta jiyo ihun matar Amadu, bata san da inda kuzari ya zo mata ba har ta iya tambayarsu kamar ta rikice.

“Me muka muku?”

“Tambaya ma kike? Ba kun aje yan sakai a gidanku ba, wai masu yaya ko? To yau sai mun kashe su sai mun muku wulakanci”

Inna ta hade hannayenta biyu tana kuka tana rokonsu.

“Ku dubu girman Allah ku yi hakuri, ku kashe ni kar ku kashe yarana dan Allah…”

Bata gama rokon ba, wani ya karaso kusa da ita ta fisgi rigar jikinta.

“Cire wannan rigar ai har ke da kike uwarsu ba zamu bari ba”

Sai a lokacin Inna ta kara firgicewa, ta fara bin fuskokinsu da kallo tana ganin komai kamar a mafarki.

“Cire cire”

Sai ta rika jin kamar ba hausa suke mata ba, gaba daya ta rasa gane abun da suke nufi, bata fahimci manufarsu ba har sai da suka barge rigar dake jikinta suka kama zanen shi na suka fisge suka jefar da shi can gefe, suka mata tsirara a gabansu. Aminatu dake karkashin gado ta yi saurin kara rufe bakinta wasu irin zafafa hawaye na sauko mata, saurin rumtse ido rai hango mahaifiyarta tsirara a kwance yaron da be wuce sa’ar danta na biyar ba ya fara keta mata haddi!!
Ba mutum daya yai ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, haka suka jera su goma sha daya suka yi mata yadda suke so, sannan suka fita suka barta kwance kamar tsumma. Abun ka da uwa suna fita ta yi karfin halin rarafawa ta isa inda zanenta yake da idanuwan da take jin kamar kukanta ya kare a yau. Ta dauki zanen da hannunta amman yadda zata sarrafashi ta daura ta suturta jikinta ne ta manta sakamon jin ihun Sanusi, cikin rashin kuzari zuci da na jiki ta isa jikin kofar tana kallon yadda yan bidigar majiya karfi, suka danne Rilwanu a kasa, dayansu ya kunna babur dinsa ya hau ta kan wuyansa ya tsaya.

“La’ilaha Illahu”

Inna ta fada da wata irin muryar da bata taba sanin tana da ita ba, tana mika musu hannu. Ba su kulata balle su fasa abun da suke, ba su saukar da babur din a wuyansa ba sai da suka tabbatar ransa ya rabu da gangar jikinsa, daman haka suke ma irin su Rilwanu masu aikin sa-kai domin kare rayuwarsu da kuma ta al’ummarsu, idan suka halbeka da bingida suka ga bata tashi ba, sai su gwada adda, idan ita ma ba tai ba sai su saka dutse ko babur. Bayan sun kashe Rilwanu suka fashe rumbun hantsen dake gidan suka saka Iro a ciki suka kunna masa wuta, tare da hatsin. Wani irin ihu yake yana neman ceto amman babu wanda zai iya kawo masa dauki.

“Kaico Kaico kaico”

Inna ta fada tana kallon yadda danta ke ci da wuta, ga kuma wani a kwance, wani irin shiga da fita numfashinta ya rika yi da karfi, tana jin wani abu na mata yawo a ciki, gaba daya sai ta nemi dan sauran kuzarin nata ta rasa, a bakin kofar ta fadi kwance yawu da majina suna zubo mata a lokaci daya, cikin karfin hali ta dan dago kanta ta juyo ta kalli Inna Aminatu take boye, sannan ta juya tana kallon yadda suka dauko katon dutse suka daga sama suka saki a akan Amadu da yake da wasu barayin suka danne a kasa ko motsi baya iya yi, kamar yadda sukai ma Amadu haka wadancan barayin da suka zagaya gidan Musa suka masa, domin duk wanda ya san yayan Mai Damma ya san wuka ko bindiga bata hudasu, ya sha kuma ba bawa yaransa, ba dan komai ba sai dan kariyar irin wannan ranar, sai dai ayau shan be amfana musu komai ba, ba su kadai ba har da sauran mazan gari da bindiga bata fasawa, sukan kashe su da babur ko dutse, balle kuma Rilwanu da Iro da sukai kwarin suna a garin saboda aikin sa-kai da suke.
Sanusi kam sai yai kamar ya mutum ganin nasa mai sauki ne, domin da babur sauka hau kafarsa dan kawai su gana masa azaba, baya ambatar komai sai Allah, ba a gidan Mai Damma kadai ba, a garin gaba daya haka suka ci suka shude babu wanda ya kawo agaji, suka ci karensu babu babbaka yadda ransu ya so sannan suka bar garin bayan su kwashi abinci da mata cikin har da matan Musa da matar Amadu.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button