BAKAR WASIKA 5

“Kasan mi ye Talba?”
Talba ya kalleshi yana kokarin yanke kiran Ali da yake.
“Kai dan’uwana ne, ba zan so ka cutu ba, kamar yadda ba zan so Leila ta samu matsala, ni shawarar da zan baka karka auri macen da baka so, domin zaku yi ta samun matsala ne kawai, ji abun da kake yi a yanzu saboda Momy da Daddy kake yi ba wai dan ka faranta ranta ba, kuma ba dan kana so ba, hakan kuma zai haifar da kiyayya da tsana a tsakaninku”
Talba ta saka wayar aljihu yana kallon Kabir.
“Ina sonta Kabir…”
“No, maybe dai kana sonta saboda baka san miye so ba, ko kuma kana sonta saboda baka son ka bawa Daddy kunya, ko kuma kana sonta saboda kana son ka yi aure, amman na san wata rana zuciyarka zata so wata wata kila Leila ce ko wata dabam, a lokacin da zata maka laifi kuma na bata hakuri Wallahi baka ko sani ba, wanda zaka so faranta mata a karan kanka, idan tana cikin damuwa kai ta kokarin ganin ka cireta, idan tana kuka karika jin hawayenta kamar mutuwarka ne, duk wannan shan kunun da kake yi ita zaka sake mata ka rika neman tai maka murmushi kana mata dariya, idan zuciyarka ta fara wannan son, duk son da biyayyar da kake yi ma Daddy ko Momy idan suka muzantata sai ka ji ba dadi kamar kai aka yi ma, daga lokacin ne rayuwarka zata fara canjawa…”
“Noo Kabir, you know i don’t believe in love, so wannan daren ba zai taba zuwa ba balle har na kwanta na yi wannan kalar mafarkin, ku ne da kuke karance karance da kallo fina finai kuke dauka irin wannan soyayya gaskiya ce, even if gaskiya ce ma ni bana cikin irin wadannanhawayen mazan…”
Yana fadar hakan ya fara sauka entrance din. Kabir ya bishi da kallo yana murmushi.
AMINATU POV.
Sai da haske ya fara bayyana sannan mutane suka leko gidan, duk da kasancewar kowa yana fama da nasa jimamin. Duk wanda ya shigo ya tararda gawar su Amadu sai ya zubar da hawaye, daman can kowa ya saka ran sai ayi musu ta’asar da tafi ta kowa saboda suna da yan sa-kai har biyu da da barayin yankin suke matukar tsoronsu, domin basa yi ma barayi da sauki musamman idan sun hadu da su a wani gurin. Da taimakon yan tsirarun garin da suka rage aka dauko zage aka rufe gawarsu, Sanusi kuma aka dauke shi kan babur zuwa babbar asibitin shimkafi, a lokacin ne Inna ta fahimci har da Musa aka kashe, kuma aka tafi da matansa biyu bayan matar matar Amadu, cikin yaranta da suka tsira Aminatu ce kawai ita ma dan ba su ganta ba ne, sai kuma Isa da ya tafi kai Baba gurin ganin Gwaggonsu, sai kuma Bashiru dake kasuwancinsa a birni tare da iyalansa.
Karfe bakwai da yan mintuna Baba ya iso cikin gidan, domin labarin abun da ya faru ya same shi a can garin da yake gurin kanwarsa, yana shigowa cikin gidan ya kasa rike kansa, tsayi ma ya kasa duk da kasancewarsa namiji sai gashi ya zube kasa yana kuka da idonsa, Inna kam zaune kawai take tana kallon komai, hawayen sun dauke mata. Da dai daya Baba ya fara bin gawar yayansa har hudu yana dubawa, Isah ma kuka yake sosai, ya ga Amadu da ka fashewa kai, sai kuma Rilwanu, da aka takewa wuya da babur, haka Musa na da dutse aka fashe masa kai. Iro kam gawarsa bata wuce ta karamin jariri ba domin gawarsa ta kone kurmus daker aka samu aka hada dan abun da yai saura gudu daya aka lullube da zanen Inna.
Baba ta fadi zaune ya fashe da wani irin kuka yana dora hannu saman kai.
“Allah ka hana zalinci, Allah ka sani mutanen nan ba mu musu komai ba, Allah ka isar mana”
Baba ya fada cikin wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya, sai kuma ya juyo ya kalli dansa Isah da shi ma kukan yake ya ce.
“Isah ka gani an kashe an yan’uwanka…”
Daga inda Inna take zaune ta amsa.
“An kashe su Malam, d’a hudu, ni na haifi yarana kuma a gaban idona aka kashesu, yaran da ba su wuce sa’an yayana ba suka keta min haddi har su goma sha daya, a gaban yata, suka kone muna abinci, suka kora mana dabbobi, saboda kawai zalinci, titin kwarai ba mu da shi a garin nan, ba mu damu da cigaban zamani ba, taki ma sai an ga dama a bamu, duk wani cigaba ko aikin taimako ba mu san shi ba, da hakkinmu muke tara komai, yanzu kuma zaman lafiya da farinciki ya gagaremu…”
Inna na gama fadar hakan ta mike tsaye da sauri jin kamar numfashinta zai fita, ta dora hannunta a kirji tana kuka tana neman agajin Allah.
“Innalillahi, shikenan sun raba ni da murmushi sun raba ni da dariya, kuma sun keta rigar mutunci na”
Safa da marwa ta fara yi cikin gidan hannunta akai tana kuka tana jijjiga. Duk abun da ake a kunnen Aminatu, domin bachin da take son ya dauke ta ta sake farkawa a rayuwar zahiri be dauke ta ba, har lokacin kuma jikinta be daina rawa ba, kamar yadda kunnuwanta ba su daina jin karar binga, haka idanuwanta ba su kawar mata da ganin da tai ana yi ma mahaifiyarta fyade ba.
“Ina Auta? Ko sun tafi da ita?”
Baba ya tambaya yana kuka sosai, sai wata matar dake tsaye kusa da Inna tana kokarin bata hakuri ta ce.
“Aa tana daki”
Duk wanda ya ji ko ya ga ba aje da Aminatu ba ya san da cewar ba su ganta ba ne, yadda suka kwashi matan garin suka tafi da su babu abun da zai hana su zuwa da Aminatu. Baba ya tashi da sauri ya shiga dakin, sai ya same ta a inda ta saba kwanciya tana lullube, ba jikinta kadai ba, har hakoranta kana jin kara yadda suke haduwa da juna tsabar yadda jikinta yake rawa. Baba ya kai hannu ya janye mayafin sai ta tashi da sauri idonta a kumbure ta kalleshi.
“Baba…Baba… Baba… Baba”
Baba ya sake fashewa da kuka.
“Baba wasu mutane ne suka zo.. Ba mu musu komai ba Wallahi, ba mu musu komai ba… Sun… Sun… Sun… ”
Ta kasa fada sai ta fashe da wani irin kuka ganin cewar da gaske ne komai ya faru ba mafarki ba.
Ba ko wace gawa ta samu sallah da sutura yadda ya kamata, saboda yawan gawarwakin, ashe ma samun sutura da masu yi ma gawa sallah da kuma binne ta kamar yadda addini musulunci ya tabadar wani abu ne da ba kowa yake samu ba, domin wasu da tufafin jikinsu ake saka su a cikin ramen, wani ramen kuma sai a hada mutum hudu guri daya.
Bayan an binne gawarwarkinsu ne, Bashiru ya iso, hankali tashe, yana shigowa shi ma ya fara nasa kukan, na rashin yan’uwa. Aminatu kam tana can gefe daya zaune ta ki yarda ta zauna cikin mutane ko kallon mutane bata so, kuma ta ki cin komai. Sai da ta ji Baba yana maganar zai tafi asibitin gurin Sanusi sannan ta mike tsaye da sauri.
“Baba dan Allah ka tafi da ni”
Ta fada cikin kuka, wani irin tsoro take ji ganin take kamar sake dawowa zasu yi, gaba daya a firgice take, a dayan bangaren kuma tana son ganin halin da dan’uwanta yake ciki.
“Aa Auta ki zauna a nan, asibi ce fa”
Ta yi saurin rike rigarsa ta fashe da wani irin kuka.
“Dan Allah Baba ka tafi da ni, ka taimaka min dan Allah Baba ka tafi da ni”
Idon Baba ya sake cika da kwalla.
“To saka talkaminki mu tafi”
Ta saka talkamin dake kusa da ita, bata tsaya neman nata ba, haka suka fito cikin gidan tana rike da rigar Baba, Baba ya nuna mata wani babur.
“Ki hau Babur din Buba, ni zan hau na Isah”
Sai ta girgiza masa kai tana kuka ta rumgume shi.
“Aa Baba Baba dan Allah karka sake yin nisa da ni”
Gani take kamar idan yana nan babu abun da zai faru, gaba daya ta rasa gane kan komai, kwakwalwarta ba zata iya dauka ba.
A dole babur daya suka hau ita da Baba, dan motsi kadan sai ta ji kamar zuciyarta zata fado tsabar tsoro, har suka isa idon a rufe yake domin ganin take idan ta bude ido mutanen zata gani.
Ko da suka isa sun tararda asibitin a cike, domin a kauyensu ko a gidansu kadai akai ta’asar ba, an kawo mutane da yawa, wasu sai ihu suke wasu kuma suna zaune suna jiran a gama da wasu a duba su. Baba da Aminatu waje suka tsaya Isah ya shiga ciki, ganin ya dade yasa Baba ya shigo cikin emergency tare da Aminatu, gaba daya ta kara firgicewa ganin yadda wasu ke zubar da jini. Kamin su karasa inda suke zaton dakin da Sanusi yake ne, Isah ya fito yana kuka.